Kafar yada labarai ta Hauza ta rawaito cewa, Shekh Sanusi Abdul Qadir, wakilin, 'yan'uwa Musulumi Almajiran sayyid Ibrahim Zakazky na jihar Kano, ayayin da yake gabatar da tunatawar Jumaa a masallaci fage, ya bayyana cewa, Har yanzu wasu mutane a kasar nan, suna ganin cewa waɗanda ke cutar da su, su ne masu cetonsu. Yaya za ka ɗauki dukiyarka ka ba wa barawo amana, sannan ka saka ran dukiyar za ta tsira?
Dakta Sanusi Abdul Qadir ya ce, dole ne sai an bi matakai na kawo gyara; Abu na farko shi ne bara’a, na biyu kuma wilaya. Ka san jagoran zamanka, ka san murshidinka, ka san malaminka, ka san wanda kake bi — ko ba haka ba? Mu dai Alhamdulillah muna da Jagora, mun san wa muke bi; daga Allama Sayyid Zakzaky har zuwa Imamul Hujjah (AF), har zuwa Manzo (SAWA). To wannan ita ce wilaya.
Na uku, dole ne mutum ya yi ƙoƙarin gyara kansa. Ba yadda za a yi kana son a gyara al’umma amma kai kanka kana cikin barna. Kai kanka ka san abin da kake yi ba daidai ba ne. Zalunci ba ƙaramin laifi ba ne, babba ne. Ko azzalumin da zai kwace silifan wani a masallaci, ko azzalumin da zai sace biliyan ɗaya daga asusun gwamnati — sunansu ɗaya: azzalumai. Saboda haka dole mutum ya gyara kansa ta hanyar nisantar abin da Allah Ya haramta da yin riko da abin da Allah yake so.
Na huɗu kuma, addu’a. Wannan bala’in da muke ciki yana bukatar addu’a sosai.Abu na biyar shi ne wayar da kan al’ummar Musulmi. Duk da yanayin da ake ciki, akwai waɗanda ba su san halin da ake ciki ba; a rufce suke. Mafi yawa basu san cewa akwai matsala ba. Dole mu ci gaba da wa’azi da wayar da su. Haka kuma, dole mu nuna rashin amincewa ta duk wata hanya da za mu iya: ta rubuce-rubuce, ta magana, ko ta muzahara. Wajibi ne mu ci gaba.
Ya koma kan tunawa da 12 ga December 2015, wato waki’ar Buhari (LA). Ya ce: “Ina waɗancan jaruman sojojin? Su Burutai da yaransu — Allah Ya tsine musu albarka. Ina jarumtarsu ta lokacin da suka yi ta dannar yara da mata har da jarirai, wai don an tare hanya? To yanzu ga ‘yan ta’adda sun tare dazuzzuka, me ya sa ba su nuna wannan jarumtar ba? An gane ko?”
“Kuna sane mun shiga December, watan da aka yi wannan mummunar waki’a. Wannan abu Isra’ila da Amurka ne suka shirya shi, amma wanda ya ware kuɗin shi ne Saudiyya. Mai magana da yawun yariman Saudiyya ya faɗa haka lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jaridu a Birtaniya. Kafafen yaɗa labarai irin su Muryar Hausa ta Jamus sun rawaito hakan — cewa su ne suka ware kuɗin da aka yi abin nan a Najeriya.”
“Shi kuma Buhari yana faɗa wai ‘an yi gwamnati cikin gwamnati’. A lokacin akwai gwamnatin ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa bai tura jami’ansa an aukar musu ba. Haka nan gwamnatin ‘yan bindiga ta bulla a Sokoto da Zamfara ya yi shiru. To su waɗannan ba gwamnati cikin gwamnati ba ne?”
Daga Media Forum Kano.















Your Comment