Kamar yadda Ofishin Yada Labaran Hauza ya ruwaito, Ayatullah Alireza A'arafi a taron shekara-shekara na wakilan dalibai da masana makarantun ilimin addini na ƙasa wanda aka gudanar a dakin taron makarantar 'Ma'asumiya' da ke birnin Qom, ya bayyana matsayi na tarihi da wayewar cibiyoyin ilimin addini inda ya ce: Makarantun ilimin addini cibiya ce wacce a cikin jinsinta tana da yanayin wayewa bisa tunanin Musulunci kuma wannan yanayin yana ci gaba sama da shekaru dubu.
Imam Khomeini Ya Samar da Cikakken Nazarin Wayewar Musulunci Cikin Tsari Da Jarumtaka
Shugaban makarantun ilimin addinin bayan ya bayyana hanyoyi uku na fahimtar wayewar Musulunci, ya jaddada cewa: Imam Khomeini (R) tare da gabatar da fassara cikakkiya, tsari da kuma bisa yarda da sauye-sauyen kimiyya da zamantakewa, ya zama mutum mai mahimmanci a tarihin tunanin Musulunci kuma ya buɗe wani sabon mataki a rayuwar tunani da wayewar Musulunci.
Wayewar Musulunci; Cikakkiyar Fassara Da Ta Kalubalanci Fahimtoci Marasa Inganci
Ayatullah A'arafi yayin magana akan fahimtoci marasa inganci game da ma'anar wayewar Musulunci ya ce: Wasu gungu sun fassara Musulunci ta yadda ake tunanin cewa tushen addini ya maye gurbin duk tunanin ɗan adam da ƙoƙarin kimiyya kuma dole ne a rufe hanyoyin jihadin kimiyya. Wannan hangen nesa, wanda aka gani a wasu ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi, ba abin karɓa ba ne kuma bai yi daidai da hakikanin Musulunci ba.
Memba na babbar majalisar makarantun ilimin addini ya kara da cewa: Akasin haka, fassarar da Imam Khomeini (R) ya bayar game da Musulunci, hanya ce mai cikar gaske, wacce ta mayar da hankali ga al'umma da kuma wayewa wacce ta ƙunshi dukkan fannonin rayuwar ɗan adam kuma a lokaci guda, tana karɓar ci gaban kimiyya da sauye-sauye da kuma ba da amsa ga sabbin buƙatu.
Samuwar Nazari na Uku; Sabon Batu a Musulunci a farkon Motsi (Juyi)
Shugaban Hauzar, yayin da yake magana a kan shekarun farko na motsin Musulunci ya nuna cewa: Idan da wani a yau zai sake duba tunanin Imam a shekarun 62 zuwa 64, wadannan jawabai, sakonni da sanarwa bakwai, takwas a tsakankanin wannan lokacin, zai gane cewa Imam a cikin Hauza, ya kasance yana sake karantawa da sake gina Musulunci mai zurfi a fannonin ilimi, al'adu, zamantakewa da siyasa.
Ya lurar da cewa: Yawancin malaman sun fahimci wannan hangen nesa, amma ba su da ƙarfin hali ko yanayin damar bin sa, abin da ya bambanta Imam shi ne hada fahimta mai zurfi da tsari na Musulunci da kuma tsananin rashin tsoro wajen a bayyanawa da tsara magana. Waɗannan halaye biyu Imam Khomeini (Q) ya hada kuma wannan shi ya sa nazariyya ta uku, wato wayewar Musulunci, ta shigo cikin fage.
Tafarkin Hangen Nesan Wayewa a Rubuce-rubucen Manyan Ma'abotan Tunani
Ayatullah A'arafi, lokacin da yake magana a kan tafarkin hangen nesa na wayewa a cikin rubuce-rubucen manyan masu tunani na Shi'a ya kara da cewa: Ana iya ganin tushen wannan hangen nesa a cikin rubuce-rubucen da yawa daga manyan ma'abotan tunanin Musulunci. A cikin rubututtukan masana fikihu, masana tauhidi, masu tafsiri, masana hikima da falsafa muna ganin wannan hanya. A cikin tunanin Allama Tabataba'i, a cikin tattaunawar falsafa ko a cikin tafsirin Al-Mizan, ya nuna hangen nesa na wayewa kuma cikakke na Musulunci a fili.
Memba na babbar majalisar makarantun ilimin addini ya kara da cewa: Duk da haka, mutumin da ya tattara duk waɗannan fannonin a matakin da ya shafi ko'ina da kuma haɗin kai kuma ya kafa tushen wani sabon motsi, shi ne Imam Khomeini (R).
Imam Khomeini; Nuƙuda Mai Muhimmanci a Ci gaban Tunanin Musulunci
Shugaban Hauza, da yana magana a kan bitar da ya yi a kan tarihin sauye-sauyen Hauza a taron kwanan nan na masana a birnin Najaf, ya bayyana cewa: A cikin shekaru 1200 da suka gabata, akwai kusan matakai goma zuwa ashirin na sauye-sauye na asali a cibiyoyin ilimin addini waɗanda manyan malamai kamar Allama Al-Hilli, Khwaja Nasiruddin Tusi da sauransu sun kasance wadanda suka yi aiki a cikin su kuma kowannensu ya haifar da ma'ana mai mahimmanci.
Ya ci gaba da cewa: Duk da haka Imam Khomeini mutum ne a matakin tarihi daban wanda ya kawo babban juyi a tarihi. Ya yi amfani da duk abubuwan da suka gabata, sannan kuma sai ya ƙirƙiri wani motsi na daban; sauyi na ƙarnuka da yawa wanda ya shigar da Musulunci zuwa ga wani sabon mataki.
Tushen sauyi; Kallon Hangen Nesa da Wayewar Imam ga Musulunci
Shugaban makarantun ilimin addinin yana magana akan cewa babban abin da ke haifar da ƙiyayya ga juyin juya halin da tunanin Imam shi ne wannan hangen nesa na wayewa, ya bayyana cewa: Ruhi da jigon sauyin da Imam Khomeini (R) ya haifar, shi ne wannan babban hangen nesa, mai zurfi da kuma wayewa ga Musulunci. Wannan hanya ɗaya ce daga cikin ka'idojin asali na tunanin Musulunci wanda ya farfado da shi kuma ya shigar da shi cikin fagen zamantakewa da siyasa.
Your Comment