Tuesday 9 December 2025 - 06:03
Madubin Annabta | Mace Wadda Ta Rayar Da Tafarkin Annabta Har Zuwa Ƙiyama

Hauza/ Bisa ga fassarar saukar Suratul-Kawthar da kuma abin da mushrikai suka yi wa Annabi (saww) ihu saboda rashin ’ya’ya maza, Allah ya amsa musu ta hanyar bai wa Annabi "Al-Kawthar", domin ya karyata wannan izgilanci.

Acewar Kafar yada labarai ta Hauza, Don tunawa da munasar Kwanakin Haifuwar Sayiida Zahra (as), An fitar da Zababbiyar ma’anar “Al-Kawthar” a matsayin ita ce wanzuwar Sayyida Fātima Zahra (saww), wadda ta kasance tushen ɗorewar zuriyar Annabi da kuma alheri mai yawa ga al’umma, har ta sa maƙiyinsa ya zama ‘abtar’ — marasa albarka da cigaba. kamar yadda Allah mabuwayin sarki yake cewa:

إِنّا أَعطَیْنَكَ الْكَوْثَرَ


Lalle, mun ba ka Al-Kawthar – wani alheri mai yawa.


فَصَلِّ لِرَبِّكَ وَانْحَرْ


Ka yi salla domin Allah, ka kuma yanka hadaya.


إِنَّ شَانِئَكَ هُوَ الْأَبْتَرُ


Lalle wanda yake maka kiyayya shi ne maras ƙarshe (abtar).

A lokacin da 'ya'yan Annabi, Qāsim da ʿAbdullāh, suka rasu cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, mushrikai suka yi farin ciki da dariya suna cewa Annabi ya zama “abtar”. Daga cikin waɗanda suka yi maganar akwaiʿĀṣ ibn Wāʾil, wanda ya ce Annabi ba shi da zuriyya.

Wannan kalma ta ɓata zuciyar Annabi sosai; don haka Allah Maɗaukaki ya saukar da wannan surah domin tausar ransa, a matsayin sa na Habībinsa Muhammadu (saww) da kuma amsa ta tauhidi ga mushrikai.


Al-Kawthar: Shi ne wadata ta alheri, wanda ta haɗa da zuriyar Annabi, ilimi, al’ummar kirki, da ribɓar aiki mai kyau.

Don haka, musulmi na gaskiya suna ɗaukar Sayyida Fāṭima Zahra (As) a matsayin fitaccen misalin Al-Kawthar saboda ita ce asalin zuriyar Annabi mai tsarki, kuma ta haifi Hassan da Husain, wadanda suka ci gaba da rayar da sunan Annabta da addini har zuwa ƙarshe.

Waƙar da aka ambata ta bayyana wannan gaskiyar da kyakkyawar ma’ana:

عطاكَ كوثرٌ من إحسانٍ / فلا يحزن قلبك مرةً أخرى
من نهر الجنة ومن خيرٍ كثيرٍ / ومن تكثير نسلٍ بفاطمة الطاهرة


Allah ya ba ka Kawthar daga rahamarsa — don haka kada ka damu.
Daga kogin Aljanna da alheri mai yawa, ya ƙara maka zuriyya ta hanyar Fāima mai tsarki.

Shi ya sa siffar “Al-Kawthar” ta bayyana ne cikin zuriya da ɗorewar Al’umma ta hanyar Fātima Zahra (As). Mushrikai sun ce Annabi ba shi da zurriyya, amma Allah ya tabbatar da akasin haka: daga ita ne zurriyar Annabi ta wanzu har zuwa ƙarshe, kuma maƙiyinsa (ʿĀṣ ibn Wāʾil) ya zama wanda babu mai bin sa.

Saboda haka, fitacciyar ma’anar Al-Kawthar a cikin tafsirin ilimi da ruhi ita ce wanzuwar Fātima Zahra (As), wadda Allah ya sanya ta zama gadon alherin Annabi da rayuwar addini har zuwa ƙiyama. “Al-Kawthar” alheri ne mai yalwa, wanda ya zama zahiri a cikin Fāima Zahra (As).

Hakika, wanzuwar Fātima (As) – ita ce tushen alheri mai ɗorewa; ta tabbatar da rayuwar Manzanci (Risala) da zuriyar tsarki (‘Ahlul‑Bayt), domin ta haɗa tsakanin alheri na zahiri da na ruhi.

Domin bita:
1. Fassarar Majma’ul Bayan– juzu’i na 27, shafi 309.
2. Waƙar Sayyid Abbas Hosseini (Hiran) daga littafin Manāqib Fāimiyya, shafi 92–22.

3. Tarjamar Hausa: daga Tasirin Shekh Abubakar Mahmud Gumi.

Tushen bayanin: Jāmi’un min Zulālil‑Kawthar, shafi 21–22.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha