Monday 8 December 2025 - 21:57
Yanar Gizo Mafi Kyawun Kayan Aiki ne Domin Bayyanawa da Haskakawa

Hauza/Hujjatul Islam Mehdivi-Pur a bikin kaddamar da shirin horar da kwararru kan watsa labarai da sadarwa ta yanar gizo na musamman ga dalibai da kuma wadanda suka kammala karatu daga nahiyar Afirka, ya yi bayani kan muhimmancin kwarewar daliban ilimin addinin Musulunci wajen amfani da yanar gizo.

A cewar sashen fassarar Ofishin Yada Labaran Hauza, Hujjatul Islam Mehdivi-Pur, wakilin waliyul faqih a nahiyar Afirka, a wannan taron ya jaddada wajibcin shigar malaman addini cikin fannin yanar gizo, ya nuna cewa: Domin samun nasara a fannin wa'azi da koyarwar addini dole ne a gabatar da ita cikin tsari mai kyau, cikin dadi, kuma daidai da abin da masu sauraro suke so, domin mutum a halittar sa yana son kyau, kuma idan koyarwar Iyalan gidan Annabi (AS) ta zo da kayan aiki masu kyau, za ta zama abin tunawa a zukata da tunani.

Ya kara da cewa: "Shi ya sa a cikin Alkur'ani mai girma, yawancin koyarwar siyasa, zamantakewa da ɗabi'a sun zo ne a cikin tsarin labari. Akwai kananan labarai fiye da ɗari biyu a cikin Alkur'ani mai girma, wanda a tsarin su, ban da koyar da darasi, ta fuskar fasaha ma suna jan hankalin mai sauraro."

Hujjatul Islam Mehdivi-Pur yana mai jaddada cewa masu wa'azi suna amfani da damar intanet, yanar gizo, musamman ma 'Artificial intelligence', ya ce: "Dole ne tare da canje-canjen fasaha da na'urori, mu iya gabatar da koyarwar addini da abubuwan da muke so ga masu sauraromu. Dalibanmu a Jami'ar Al-Mustafa kari akan ilimi, dole ne su koyi fasahohi da dabaru, domin koda kun samu ci gaba ta fuskar ilimi amma ba ku da fasahar da ake bukata don gabatar da shi, tasirinku zai yi kasa."

Ya kuma tunatar cewa: "Akwai fiye da fasahohi guda ɗari da dalibai za su iya koya bisa ga sha'awarsu da damarsu, wanda kafin komawa kasashenku zaku iya amfana da ita. Gudanar da masallaci, gudanar da ajujuwa, ba da shawara kan iyali da dai sauransu, kowannensu fasaha ce. A fannin watsa labarai ma akwai fasahohi ashirin da dole ne dalibanmu su koya a wannan fanni."

Wakilin Waliyul faqih a nahiyar Afirka yana mai jaddada wajibcin daliban Afirka su amfana da iya tantance abubuwan siyasa da na zamantakewa a wannan nahiya, ya bayyana cewa: "Mafi kwarewar 'yan jarida, editoci, masu fafutuka a yanar gizo da dai sauransu a nahiyar Afirka, ya kamata ne su kasance daga cikin dalibanmu. A yau fikihunmu da tafsirinmu da tarihinmu da aƙidunmu dole ne a gabatar da su ta yadda zai kasance cikin jan hankali ga mai sauraro, don haka koyarwar addini dole ne a gabatar da ita a matsayin ka'idojin zamantakewa, al'adu da siyasa."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha