Monday 8 December 2025 - 20:57
An Kaddamar da Shirin Horar Da Kwararru Kan Watsa Labarai da Sadarwa Ta Yanar Gizo Na Musamman Ga Daliban Afirka

Hauza/An fara aikin shirin horar da kwararru kan watsa labarai da sadarwa ta yanar gizo na musamman ga dalibai da kuma wadanda suka kammala karatu daga nahiyar Afirka a zauren Arif Husain na Makarantar Imam Khomeini, tare da gudanar da bikin kaddamarwa.

A cewar sashen fassarar Ofishin Yada Labaran Hauza, bikin kaddamar da shirin ya fara ne da jawabin wakilin waliyul faqih a Afirka, sannan kuma Mista Allah Akbari, babban daraktan hulda da jama'a na Jami'ar Al-Mustafa a cikin wani jawabi yayin da yake mika ta'aziyya a ranar tunawa da rasuwar Mai girma Ummul Banin (AS), ya bayyana cewa: Yanar gizo na da matukar mahimmanci wanda har jagoran juyin juya halin Musulunci ya dauke shi a matsayin filin gwagwarmaya. Ya kuma ambaci cewa muhimmancin wannan fanni daidai yake da juyin juya halin Musulunci.

Ya kara da cewa: "Wannan yana nuna muhimmancin waɗannan shirye-shiryen da kuma samun ƙwarewar da ake bukata don shiga cikin yanar gizo mai tasiri. Filin mimbari da kuma wa'azi fuska da fuska har yanzu suna da muhimmanci amma amfani da sabbin kayan aiki na iya samun masu sauraro miliyoyi daga ko'ina cikin duniya kuma waɗannan kayan aikin a yau suna shirye, alhakimmu ne mu samar da abubuwan da suka dace a cikinsu don mu kai ga masu sauraro."

A ƙarshe babban daraktan hulda da jama'a ya lurar da cewa: "Al-Mustafa na alfahari da kasancewa mai masaukin baki a gare ku, kuma tare da hadin kan ku dalibai musamman a nahiyar Afirka, muna gudanar da waɗannan shirye-shiryen na horar da ƙwarewa domin, in sha Allah, mu nufi samar da samfurin kyawawan sakamako."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha