Sunday 7 December 2025 - 20:34
Bayyanannun Alamomin Raguwar Ikon Amurka Daga Takardun Gwamnatin Trump ta Fitar

Hauza/Yaduwar takardar dabarun tsaron kasa ta Amurka a fili ta shaida cewa, ba kamar yadda shugabannin fadar White House ke bayyanawa ba, Amurka a duniyar yanzu ba ta da fifikon tattalin arziki da na soja, kuma ikonta na kan raguwa.

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, bisa ga imanin yawancin masana harkokin kasa da kasa, fitar da takardar dabarun tsaron kasa ta Amurka – wadda daya daga cikin muhimman takardu ce a fagen tsaron kasa da harkokin wajen Amurka, kuma ana fitar da ita ne sau daya cikin shekaru hudu – ta kasance babbar shaidar raguwar tasirin Amurka a sabon tsarin duniya fiye da kowane abu.

Gaskiya Mai Daci Ga Amurka Bisa Ga Abin da Wata Takarda ta Kunsa.

Dan jarida Mas'ud Barati, ya bayyana ra'ayinsa cewa: "A farkon takardar, gwamnatin Trump ta kira manufofin da Amurka ta bi a baya game da al'amuran duniya a matsayin kuskure, tana mai cewa sun wuce karfin Amurka. Sun yi tsari fiye da kima game da ikon Amurka na samar da kudade ga babbar gwamnatin jin dadin jama'a da kula da su da gudanarwa tare da babban tsarin soja, diflomasiyya, leken asiri da taimakon kasashen ketare. Takardar ta kuma kai hari kan 'Yancin kasuwanci' inda ta dora laifin lalata 'matsakaicin aji' da 'fifikon tattalin arziki da na soja' na Amurka a kan sa. A takaice dai, wannan takarda ta yarda cewa Amurka a duniyar yanzu ba ta da fifikon tattalin arziki da na soja."

Ya kuma nuna cewa: "Wadannan abubuwan da takardar dabarun tsaron kasa da gwamnatin Trump ta kira kuskure, sune ainihin abubuwan da suka kafa mamayar Amurka da tsarin Amurka bayan yakin duniya na biyu, musamman bayan rushewar Tarayyar Soviet. Takardar Trump a sarari a ko'ina tana mayar da Amurka cikin iyakokinta, kuma a bayyane yake cewa Trump baya ganin matsayin Amurka ya isa karfi da kuzari don ci gaba da bin manufofin da ta yi a baya. Ko a lokacin da take magana kan manufofin Amurka game da Yammacin Asiya (Gabas ta Tsakiya), tana nuna farin ciki cewa al'amuran yankin ba su kara mamaye manufofin ketare na Amurka ba, kuma yake-yaken 'gina al'umma' marasa iyaka sun kawo karshe."

Hanyar Kiyaye Ma'aunin Iko Ta Canza Gaba Daya

Ya kara da cewa: "A wani sashe na wannan takarda, an bayyana 'ƙarfafa ƙarfin masana'antu' a matsayin babban fifiko na manufar tattalin arzikin kasa, kuma abin sha'awa shi ne, gwamnatin Trump ta ɗauki hakan a matsayin abin da ake bukata don dawo da ƙarfin kasa na Amurka da aka rasa. Wannan maganar kanta tana nuna cewa Trump baya ganin ƙarfin masana'antu na Amurka na yanzu yana biyan bukatun Amurka a lokacin zaman lafiya da na yaƙi."

Barati ya kuma ce: "Wani muhimmin bangare na takardar shi ne fuskantar batun samun karin iko da wasu 'yan wasa ke yi a fagen duniya. A da, ana tunanin cewa Amurka tana nufin dakile yawan sabbin 'yan wasa ne. Batun da ake magana akai a cikin kalmomi kamar 'axis of authoritarianism', 'axis of change', ko 'crescent', amma a cikin wannan takarda an mai da hankali kan kula da 'ma'aunin iko', yayin da takardar ta jaddada cewa Amurka ba za ta iya barin kowace al'umma ta sami ikon da za ta jefa lamuran Amurka cikin haɗari ba, amma hanyar da takardar ta nuna ita ce haɗin gwiwa tare da abokan tarayya don kiyaye ma'aunin ikonta. A wannan fuskar ba ta mamaye su ba ne, ta yarda da samun karfin ikonsu da kuma mai da hankali kawai kan hana su mamayewa. A takaice dai, dole ne a yarda cewa Amurka ta yarda da canjin tsari da canjin ma'auni na iko a fagen duniya."

Canjin Tsarin Duniya da Ci gaba da Raguwar Iko

Dokta Fu'ad Izadi, masanin harkokin siyasar duniya, yana ganin cewa Amurka ba tun jiya ko yau ba ne ikon ta ya fara raguwa, sai dai, shekaru da dama kenan ikonta na raguwar, kamar yadda a cikin rahoton shekara-shekara na wasu muhimman taruka kamar taron Munich kai tsaye ko a kaikaice aka yi nuni ga wannan raguwar iko.


Da yake yin nuni ga kalaman mai girma jagoran juyin juya halin Musulunci da ya sha bayyana cewa raguwar ikon Amurka gaskiya ce kuma ba za ta iya komawa yadda take a baya ba, ya ce: "Gaskiyar lamarin ita ce, juyin juya halin Musulunci tun daga farko ya kasance yana adawa da mamayewar gabas da yamma, kuma a yau ma yana adawa da Amurka ba saboda kanta ba, a'a saboda manufofinta na zalunci da girman kai wadanda suke ci gaba da yi a kan kasarmu cikin kusan shekaru hamsin da suka wuce."

Mu Kula da Hadafin Yaƙin Kafafen Watsa Labaran Maƙiya

Izadi ya bayyana cewa, "yaƙin kafar watsa labaran maƙiya musamman daga shugabannin gwamnatin Amurka yana da nufin isar da rashin ingancin ayyukan Jamhuriyar Musulunci, kuma sakamakon haka shi ne sanya rashin fata game da gaba a tsakanin mutane da matasa," ya kara da cewa: "Abin da ke da muhimmanci shi ne, dole ne mu kiyaye kada mu fada cikin tarkon farfagandar da maƙiya da kafofin watsa labarunsu suke yi da gangan, kuma bincikenmu game da Amurka ya zama na gaskiya ne bisa abubuwan da suka faru a baya, duk da haka mu san cewa raguwar ikon Amurka bisa maganganun masu bincikensu lamari ne tabbatacce."

Alamun Gazawa da Rugujewa a cikin Amurka

Dokta Muhammad Sadiq Khursand, malami kuma mai bincike a fannin siyasa, ya yi nuni da cewa abin da ke faruwa a halin yanzu a fannoni daban-daban na Amurka ba raguwa kawai ba ne, a’a, alamomi ne na rugujewa. Ya bayyana cewa, duba da gargadin kai tsaye da kuma kaikaice daga masanan Amurka, akwai matsaloli da rikice-rikice na zamantakewa da yawa a cikin wannan ƙasa. Kamar yanda cibiyar bincike ta Majalisar Atlantika (Atlantic Council) ta bayyana a fili cewa, dangane da al’amuran zamantakewa, Amurka tana kan matakin mafi ƙasan tarihinta.

Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu, tsarin duniya bashi da jagora ɗaya kuma na musamman, amma yana da ƙasashe masu ƙarfi daban-daban. Ya ce tsarin duniya ya shafe matakai daban-daban har ya zuwa yanzu, kuma abin da ke da muhimmanci shi ne, ƙasashe da wayewa daban-daban bayan lokacin da suka yi tasiri, sai suka fara raguwa da rugujewa a hankali.

Ƙarin Rarrabuwar Al’ummar Amurka a Tsakaninsu

Mai nazarin al’amuran siyasa da na duniya ya kara da cewa, a fili akwai abubuwan da suka nuna cewa tsarin duniya na yau, ba tsarin mai mulki guda ɗaya ba ne (unipolar). A cikin wannan, dole ne a yi la’akari da kuma bincika batutuwan tattalin arziki, al’adu, siyasa, da sauransu. Cibiyar binciken Majalisar Atlantika kwanan nan ta gabatar da rahoto mai suna “Gwamnatin da ta Gaza” inda ta bayyana cewa, dangane da fagen zamantakewa da kauna a tsakanin jama’a, Amurka tana kan matakin mafi ƙasan tarihinta, kuma rarrabuwar kawuna na siyasa, zamantakewa, da al’adu a cikin ƙasar nan za su kara tsananta a nan gaba.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha