Tuesday 2 December 2025 - 20:13
Me ya faru a ganawar Sheikh Al-Khatib da Paparoma Leo?

Hauza/Mataimakin Shugaban Babbar Majalisar Musulmin Shi'a na Labanon ya ce wa Paparoma: Al'adunmu na ruhi sun ginu ne a kan 'yan uwanci na ɗan adamtaka; mun ɗauki wannan al'ada ne daga ka'idojin Musulunci wanda bai yarda da bambanta tsakanin mutane ba.

A cikin rahoton sashen fassara na ofishin dillancin labaran Hauza, Hujjatul Islam Wal Muslimin Sheikh Ali Al-Khatib, Mataimakin Shugaban Babbar Majalisar Musulmin Shi'a na Lebanon, ya yi maraba da Paparoma Leo na goma sha huɗu a matsayin wakilin "Babbar Majalisar Musulmin Shi'a" da kuma al'ummar Shi'a gaba ɗaya, inda ya ce masa: Muna godiya da ziyarar da kuka kawo wa ƙasarmu, kuma muna daraja matsayinku a cikin wannan wahalar da ƙasarmu ke fuskanta, kuma muna maraba da ku da gaisuwar Musulunci wadda ta gaskata Annabi Isa (A.S) a matsayin manzo, annabi, mai ba da bushara, kuma mai shiryarwa.

A yayin ganawar tattaunawa tsakanin addinai da aka gudanar a dandalin Shuhada a tsakiyar birnin Beirut tare da haɗin gwiwar Paparoma Leo, ya bayyana cewa: Gaisuwa mai yawa zuwa gare ku daga Labanon mai rauni, wanda kujerar Bishop na Vatican ko yaushe ya ɗauke ta ba kawai ƙasa ce a gefen tarihi ba, amma a matsayin wani saƙo ga duniya. Daga wannan mahanga, tsananta fatan cewa ziyarar ku zuwa ƙasarmu za ta kasance tare da nasara kuma ta haifar da ƙarfafa haɗin kan ƙasa da ya raunana a cikin wannan ƙasa wadda, sakamakon hare-haren 'Isra'ila' akai-akai kan mutanenta da ƙasarta, ta cika da raunuka.

Sheikh Al-Khatib ya kara da cewa: Al'adunmu na ruhi sun ginu ne akan 'yan'uwanci na ɗan adamtaka; mun ɗauki wannan al'ada daga ka'idojin Musulunci wanda bai yarda da bambanta tsakanin mutane ba, kamar yadda Manzonmu mai girma Annabi Muhammad ɗan Abdullah (S.A.W) ya ce: "Babu wani fifiko tsakanin Baƙar fata bisa farar fata, ko farar fata bisa Baƙar fata, face bisa taƙawa." Haka kuma, mun ɗauki wannan al'ada daga tunanin magajinsa, Amirul Muminai Imam Ali ɗan Abi Talib (A.S), wanda da jimlarsa mai matuƙar ma'ana a kan ɗan adam, ya zana yanayin alaƙar da ke tsakanin mutane: "Mutane iri biyu ne; ko dai 'yan'uwanku ne a cikin addini, ko dai takwarorinku ne a cikin halitta."

Ya ci gaba da cewa: Mun ɗauki kanmu 'yan'uwa a cikin imani da kuma takwarori a cikin halitta, kuma ba mu bambanta tsakanin 'ya'yan ɗan adam face bisa ga taƙawa. Sabanin juna dabi'a ce ta mutane kuma alaƙar da ke tsakanin bambance-bambance tana bin tattaunawa, fahimtar juna, haɗin kai kan ayyukan alheri da taƙawa, kuma zaman tare cikin lumana tsakanin mabiya addinai daban-daban, ƙa'ida ce kuma tushe, kuma abin da ke faruwa a ƙarƙashin taken yaƙe-yaƙe na ƙarya da sunan addinai, baya bayyana hakikanin addini; addinin da da farko ya ginu akan mutuntawa da darajar ɗan adam.

Mataimakin Shugaban Babbar Majalisar Musulmin Shi'a na Labanon ya ce: Mun yarda da wajibcin kafa gwamnati, amma a rashin ta, ya sanya mu dole mu kare kanmu ta hanyar muƙawama da kasar mamayar da ta kai wa ƙasarmu hari. Ba mu son ɗaukar makamai da sadaukar da 'ya'yanmu. Bisa matakan da ke sama, muna dora batun Labanon a hannunku, tare da la'akari da damar da kuke da ita a tsakanin kashen duniya, da fatan kasashen duniya za su taimaka wa ƙasarmu ta kubuta daga rikice-rikicen da suka taru a kanta, da kuma hare-haren 'Isra'ila' da sakamakonsa ya bayyana ga ƙasa da al'ummarmu.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha