Tuesday 28 October 2025 - 14:42
Masu wa'azi su shiga fagen da suke sanin batutuwan zamani da kuma sabbin kayan aiki

Hauza/ A cewar wakilin ofishin yada labarai na fannin addini Hujjatul Isalm wal Musulmi Akhtari, shugaban babban kwamitin majalisar duniya na Ahlul Bait (AS) ya ce: A yau abokan gaba sun shiga fage da kayan aikin yada labarai, sararin intanet da kuma tsare-tsaren shubuha. Ya zama dole masu wa'azinmu su shiga fagen da zasu suke sanin batutuwan zamani, da hanyar tattaunawa ta kimiyya, da hujja mai ma'ana, da kuma sabbin kayan aiki.

Labaran Hauza - kwamitin majalisar Ahlul Bait ta duniya, a ziyararsa zuwa Ahvaz a wani taro na "Jihadin Al'adu" na musamman ga masu wa'azin ofishin yada addini na lardin Khuzestan, yana magana kan matsayi mai girma na shahidai a fagen yada addini da juriya, ya ce: Masu wa'azi suna kan gaba a fagen jihadin al'adu da akida, kuma hanyarsu ita ce hanyar masu jihadi na gaskiya da annabawa. Yada addini, da karantarwar sa ci gaba ne da aikin manzannin Allah kuma yana bukatar haquri, ibada da kuma dagewa.

Ya kara da cewa: Wani lokaci amfanin wa'azinmu yana jimawa kafin ya bayyana, amma mai wa'azi bai kamata ya karaya ba. Annabi Nuh (AS) ya yi wa'azi na shekaru dari tara da hamsin, amma kaɗan ne kawai suka yi imani da shi, amma ya cika aikinsa gaba ɗaya.

Saƙo ga masu wa'azi: "Tashi domin Allah guda biyu ɗaya ɗaya”

Hujjatul Isalm wal Musulmi Akhtari, yana mai nuni ga ayar Alkur'ani mai girma "Ka ce: kawai abinda nake muku wa’azi ne da abu ɗaya, ku tashi domin Allah, guda biyu – biyu da ɗaya ɗaya," ya jaddada cewa: Tashin domin Allah bana taro ba ne kawai. Kowane mai wa'azi, ko da shi kaɗai ne, yana da alhakin yin aiki da kuma wayar da kan jama'a. Bayyanawa da shiryarwa, aiki ne na mutum ɗaya da taimakon Allah, ba ya dogara ga yanayi da goyon bayan - jamaa.

Tunawa da fagen gogewar wa'azi

Shugaban babban kwamitin majalisar Ahlul Bait (AS) ta duniya yana mai ambaton abubuwan da suka faru a shekaru a atarihin wa'azi. a Siriya da Lebanon, ya bayyana cewa: A cikin shekarun da babu wutar lantarki da ruwa da kayan aiki na farko, muna kawo ruwa daga tuluna daga nesa don gudanar da tarurrukan wa'azi. Babu wanda yake tallafawa, amma manufa, Allah ne da kuma hidima ga mutanen da suke ƙaunar Ahlul Bait.

Ya yi magana kan batun sabbin hanyoyin wa'azi ya kuma ce: A yau abokan gaba sun shiga fage da kayan aikin yada labarai, a sararin intanet da kuma tsare tsaren shubuha. Ya zama dole masu wa'azinsu su shiga fagen da zasu suke sanin batutuwan zamani, da hanyar tattaunawa ta kimiyya, da hujja mai ma'ana, da kuma sabbin kayan aiki.

Hujjatul islami wal Musulmin Akhtari, yana mai nuni ga cewa amsa tambayoyin shubuha, yana buƙatar nazari, tsarawa da kuma amfani da damar samari masu wayo, ya kara da cewa: Duk wata magana da jawabin wa'azi, da sauri yana watsuwa a sararin intanet. Saboda haka, dole ne a yi magana ayi amfani da wayo, da hankali da kuma ma'ana, tare da sanin yanayin zamani, domin maganar ta yi tasiri mai dorewa.

Shugaban babban kwamitin majalisar Ahlul Bait (AS) ta duniya, ya ɗauki jihadin al'adu a matsayin babbar ibada kuma ya nuna cewa: Allah zai taimaka wa waɗanda suke aiki a cikin hanyarsa. Muhimmancinsa shi ne, manufa ta kasance ta Allah kuma a bi hanyar bayyanawa da hankali da haquri. Wa'azi a yau, fagen fahimta ne da haquri ne, ba fagen rigima da hargitsi ba.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha