A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Mohsin Araki ya bayyana hakan ne a lokacin taron I'itikafi na shekarar 1404 (2026) da aka yi wa lakabi da "Daukakar Imani". Taron, wanda aka gudanar a Masallacin Imam Hassan al-Askari (AS) dake birnin Qom, an kuma sadaukar da shi ne domin tunawa da shahid Janar Qasem Sulaimani da sauran shahidan gwagwarmaya.
Ya bayyana cewa asalin al'umma shi ne abin da yake janyo mata daukaka ko kaskanci. Ya ce kowace al'umma ana gane ta ne ta hanyar asalinta, kuma shi ne babban sila na samun 'yanci.
Memban Majalisar Koli ta Makarantun Addini (Hauza) ya bayyana cewa "Ba'iraniyye" ba wai suna ne kawai na yanki ba. Ya ce a tsawon tarihi, asalin dan Iran ya samo ma'ana ne ta hanyar kyakkyawar alaka da Imam Hussain (AS), Amirul Muminin (AS), da kuma al'adun Ahlulbaiti (AS).
Memban Majalisar Tantance Maslahar Kasa ya jaddada cewa juriya ita ce mafi mahimmancin siffa ta wannan asali. A mahangar addini, juriya na nufin tsayin daka domin tabbatar da gaskiya da yakar barna. Manufarta ita ce kare addinin Allah, daga tutar kadaita Allah, da kuma hana barna yin tasiri a rayuwar dan Adam.
Da yake ishara da koyarwar Alkur'ani game da rundunar muminai, ya bayyana cewa Alkur'ani ya gabatar da wani bangare (front) wanda ko raunuka ko matsaloli ba sa raunana shi, sai dai ma su zama silar kara karfi da kwarin gwiwa.
Your Comment