A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Khamenei ya aika da sako zuwa taro na 59 na taron shekara-shekara na kungiyar dalibai musulmi dake Turai. A sakon nasa, ya yi ishara da yadda aka doke farmakin sojin Amurka da kawayenta a yankin sakamakon jarumta da sadaukarwar matasan Iran. Ya jaddada cewa: "Babban dalilin dake sanya azzalumai masu barna cikin rudani ba wai batun nukiliya ba ne, face daga tutar yakar tsarin zalunci na duniya da Iran ta yi, da kuma kiran da take yi na samar da tsarin musulunci mai adalci."
Ga cikakken sakon Jagoran:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
Ya ku matasa ababen kauna!
A wannan shekarar, kasarku ta samu sabon kima da daraja a idon duniya albarkacin imani, hadin kai, da yarda da kai. Farmaki mai tsanani na sojin Amurka da kawayenta (zailun) ababen kunya a wannan yanki, ya fuskanci rashin nasara a gaban fasaha, jarumta, da sadaukarwar matasan musulmi na Iran. An tabbatar da cewa al'ummar Iran, ta hanyar amfani da karfin kanta a karkashin inuwar imani da ayyuka nagari, tana iya tsayawa tsayin daka a gaban masu girman kai, azzalumai, da masu barna, kuma tana iya isar da kiran dabi'un musulunci zuwa ga duniya da murya mafi daukaka fiye da kowane lokaci.
Bakin ciki mai zurfi na shahadar wasu daga cikin masana ilimi, janar-janar din soji, da wasu daga cikin al'ummarmu ababen so, bai taba iya hana matasan Iran masu himma ci gaba da tafiya ba, kuma ba zai taba iyawa ba. Iyalan wadannan shahidai kansu suna sahun gaba a wannan tafiya.
Maganar ba batun nukiliya ba ce ko makamancin hakan. Maganar ita ce fuskantar tsarin rashin adalci da mulkin kama-karya na masu takama da iko a duniyar yau, da kuma komawa zuwa ga tsarin musulunci mai adalci a matakin kasa da kasa. Wannan shi ne babban da'awar da Iran ta musulunci ta daga tutarsa, wanda kuma ya tada wa azzalumai masu barna hankali.
Ku dalibai, musamman wadanda kuke kasashen waje, kuna da kasonku na wannan babban nauyi a wuyanku. Ku mika zukata zuwa ga Allah, ku gano karfin da kuke da shi, sannan ku sanya kungiyoyinku su nufi wannan bangare.
Allah yana tare da ku, kuma nasara cikakkiya tana jiran ku insha Allah.
Sayyid Ali Khamenei
Your Comment