Friday 12 December 2025 - 05:45
Fatima Zahra (AS), Babbar Abin Koyi a Tsarki da Taƙawa

Hauza/ Matsayin Mai girma Fatima (AS) ya wuce bayanin ɗan adam, amma tafarkinta da tsarkinta, taƙawa, irin tarbiyya da kuma kasancewarta abin koyi ga kowa darasi ne ga kowa. Tsarkin zuciya, dawwamammiyar lura, tuba da kuma istigfari su ne hanyoyin kusanci ga wilaya da kuma koyi da wannan babbar mata.

Kamar yadda Ofishin Yada Labaran Hauza ya ruwaito, saboda munasabar bikin mauludin Sayyida Fatima (SA), za a gabatar muku da wasu zaɓaɓɓun kalaman Jagoran juyin juya hali game da girman shugabar duniya da lahira.

Gazawar Harshe Wajen Bayyana Girman Matsayin Siddiƙatul Kubra (SA)

Game da Sayyida Fatima (SA) - ba don cewa mutum yana so ya faɗi abin da aka saba faɗa ba - da gaskiya kuma da adalci mu masu rauni ne, mun yi ƙanƙanta da mu iya magana game da wannan babban matsayi; game da hakikanin hasken wannan babba da misalanta cikin Imamai masu tsarki, harshenmu, bayaninmu, fahimtarmu ba su kai mu iya yin magana a wannan fannoni ba.
"Allah Ya halicce ku masu haske, kuma Ya sanya ku kewaye da Al'arshinsa."; Al'amarin hasken Imamai masu tsarki (SA) haka yake; to yanzu mene kuma muke so mu ce?
Amma a fagen koyi da tafarkin waɗannan manya da halayensu da kasancewarsu abin koyi a matsayin ɗan adam, akwai maganganu da yawa.
An faɗi abubuwa da yawa; kamar yadda wasu ’yan’uwa kuma kuka yi ishara a cikin waqoqinku na yau. Filin yin magana ma yana da yawa. A wannan fagen, zan faɗi ’yan jimloli.
Abin Da Zai Iya Zama Abin Koyi a Gare Mu

Dole ne mu kalli Sayyada Fatima (AS) ta fuskar ta ta biyu, wato ta zama abin koyi da samfuri.

Allah (SWT) a cikin Alkur'ani ya buga misali ga muminai game da mata biyu a matsayin samfuri, da mata biyu a matsayin samfurin kafirai: "Allah ya buga misali ga waɗanda suka yi imani: matar Fir'auna..." (At-Tahrim: 11). Sannan bayan ayar: "Da Maryama 'yar Imran..." (At-Tahrim: 12). Ya buga misali kuma ya kawo samfuri biyu ga muminai – ba ga mata masu imani kawai ba, amma ga maza da mata.

Da wannan hangen ne za mu iya kallon waɗannan manyan mutane a matsayin samfuri, kuma mu koya daga gare su. To, Fatimatu Zahra (AS) ita ce As-Siddiqatul Kubra a cikin siddiqai maza da mata. "Kubra" tana nufin mafi girma, wannan mai girma ita ce babba a siddiqai.

Yanzu muna so mu koya daga gare ta; mata su koya, maza su koya; kowa da kowa - mai ilimi ko jahili - ya koya.

Siffofin Fatimatu Zahra (AS)

Bari mu kalli wannan mai girma a cikin kalamun A'imma masu tsarki, menene abin da aka ambata na yabonta. A cikin ziyarar Imam Ridha (AS), idan aka zo ga Sayyada Fatima domin a yi mata sallah (a cikin wannan ziyarar da ta cika da salati), ana cewa: "Allahumma salli 'ala Fatimata bint nabiyyik" (Ya Allah, ka yi wa Fatima 'yar Annabanka Salati). Wannan siffa daya ce.

To, wannan siffa ce mai matukar muhimmanci. Hakika ba za a iya kiyastawa ba; ba kowa ne zai zama 'yar Annabi ba. Amma nasabta ta da Annabi a matsayin 'yarsa, yana nuna girman matsayi.

"Wa zaujati waliyyik" (Kuma matar waliyyinka). Wannan ita ce ta biyu. Hakika wannan ma ba zai iya samuwa ba, ba kowa ce zata iya zama matar Waliyyin Allah ba. Amma yana nuna girman matsayi, girmancin daraja da ɗaukakar wannan babbar mace.

"Wa ummis-sibtainil-Hasani wal-Husaini sayyiday shababi ahlil Jannah" (Kuma uwar jikoki biyu, Hasan da Husain, shuwagabannin matasan Aljanna). Bangaren abin koyi da amfana na wannan siffa, ya fi na siffofi biyu da suka gabata. Bangaren abin koyi da amfana na tarbiyyar jikoki biyu.

Jikokin nan biyu waɗanda suke "sayyiday shababi ahlil Jannah" (shuwagabannin matasan Aljanna), mahaifiyarsu ita ce wannan babbar mai girma. Wannan uwa mai tsarki ce ta samu damar tarbiyyarsu. Wannan shi ne abin da zai iya zama samfuri, abin koyi a gare mu.

Sai kuma, "At-Tuhratit-Tahiratil-Mutahharatit-Taqiyyat an-Naqiyyat ar-Radiyyat az-Zakiyyah" (Tsarkakakkiyar, Mai tsarki, Wadda aka tsarkake, Mai taqawa, Mai tsabta, Yardajjiya, Mai tsarki). Duk waɗannan suna da bangaren aiki-ko-koyarwa. Tsarki, da furuci uku (Tuhr, Tahirah, Mutahharah) waɗanda a hakika suna da ɗan bambanci a ma'anarsu.


Hakika dukkan kalmomin uku suna nufin tsarki da tsabta: tsarkin ruhi, tsarkin zuciya, tsarkin hankali, tsarkin jiki, tsarkin dukkanin rayuwa.

To, wannan ma yana da ɓangaren da zamu iya amfana, wannan darasi ne a gare mu. Dole ne mu yi ƙoƙari mu tsarkake kanmu, dole ne mu tsarkake kanmu. Ba tare da tsarkin ruhi ba, ba za a iya kaiwa ga manyan matsayai ba; ba za ma a iya kusantar waliyyancin waɗannan manyan mutane ba; tsarkin ruhi ya zama dole.

Tsarkin ruhi, yana tare da taqawa, da kiyayewa, da lura. Lura akai-akai da kiyaye kai akai-akai shi ne ke samar da tsarki.

Hakika ɗan adam yana da kurakurai, kuma zai iya yuwuwa a sami kuskure da zunubi tare da mu. Amma hanyar tsarkake waɗannan zunubai, Allah (SWT) ya nuna mana, ya koya mana: Tuba, Istigfari. Mu yi istigfari. Istigfari, yana nufin neman gafara. "Astaghfirullah" yana nufin "Ya Allah, ina neman gafara, ina neman uzuri".

Da gaske, da zuciya ɗaya, mu nemi uzuri daga Allah (SWT). Wannan shi ne istigfari, wannan zai tsarkake wannan zunuban da wannan ɗigon. To, "At-Tuhratit-Tahiratil-Mutahharah. At-Taqiyyah" (Mai tsarki, Mai taqawa), wato taqawar. "An-Naqiyyah" (Mai tsabta), wato tsabtar ruhi da zuciya. Waɗannan sune siffofin Fatimatu Zahra (AS). Dole ne mu ɗauki waɗannan a matsayin abin koyi, a matsayin samfuri, mu kuma kusanta kanmu da su.

-Jawabin ganawa da mawakan gidan Annabta (AS), 30 ga Maris, 2016

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha