A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, a ranar 'yancin ɗan adam ta duniya, an gabatar da zaɓaɓɓun kalamai daga jagoran juyin juya halin Musulunci game da karyar 'yancin ɗan adam na yammacin duniya ga masu hankali.
A yau, al'ummar Iran dole ne su kasance a farke kuma a waye; domin maƙiya da sunaye daban-daban - ciki har da sunan 'yancin ɗan adam - suna nufin yin gaba da cutar da juyin juya hali da Musulunci.
Kariyar da Amurka da ire-iren ta ke yi na 'yancin ɗan adam, ga kasashe da waɗanda ake zalunta a duniya, abin dariya ne kuma abin kuka. A gefe ɗaya, abin dariya ne kuma abin ba'a; domin su ne farkon waɗanda suke tauye hakkin ɗan adam, suna jefa dutsen 'yancin ɗan adam a ƙirji! Su wanene ke da'awar 'yancin ɗan adam? Waɗanda a yau jinin mutanen Falasɗinu ke zubo daga farcen hannunsu. Yanzu duk abin da suka yi a shekarun da suka gabata, a gabas da yamma - a Afirka da Asiya da sauran wurare daban-daban - suka lalata al'ummomi, suka kashe, suka take wa ɗan adam hakkinsa, wannan na nan ba a manta da shi ba.
A yau ma, gwamnatin Sahayoniyawan Isra'ila, tare da goyon bayan Amurka da ƙawayenta, tana danniya ga al'ummar Falasɗinu cikin mafi munin yanayi kuma tana azabtar da su, kuma akwai jinin mutane da shahidai na Falasɗinu a wuyanta. Irin waɗannan mutane, suke magana a kan 'yancin ɗan adam! Wannan ba abin ba'a da izgili ba ne?!
A gefe guda kuma, abin kuka ne. Ga ɗan adam, baƙin ciki babba fiye da wannan shi ne yadda ra'ayoyi da ƙimomin ɗan adam, suka faɗo cikin hannun waɗannan 'yan siyasa masu mugunta. Suna zargin Iran din Musulunci da tauye hakkin ɗan adam; alhali kuwa Musulunci shi ne babban mai kare hakkin ɗan adam.
Mu a matsayin al'umma, me yasa muke kare al'ummar Falasɗinu? Mu a matsayin juyin juya hali, me yasa muke kare al'ummomin da ake zalunta? Mu da mutanen Afirka ta Kudu, wane dangantaka muke da su?
Me ya sa muke kare waɗanda ake zaluntarwa a wurare daban-daban na duniya, saboda mulkin gwamnatocin mugaye - a zahiri masu mulkin dimokraɗiyya amma a aikace masu mulkin kama-karya - ba sa barin su kiyaye siffofin Musulunci?
Kun ga a Faransa, ba sa barin 'yar musulmi ta sa hijabi! Kun ga a Amurka, jami'an gwamnati suna dukan wani musulmi a idon jama'a don yayi ibada, me yasa ka yi salla a filin jirgin sama?! Me ya sa a duk inda wanda ake zaluntawa ya ɗaga murya ya yi kuka, muke jin wajibi ne mu taimaka masa ko akalla mu nuna muryarsa? Wannan saboda umurnin Musulunci na kare hakkin ɗan adam ne.
Ku ne shugabannin zalunci da girman kai, kuke tauye hakkin ɗan adam. Ku ne kuka dauki Majalisar Ɗinkin Duniya da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam da ra'ayoyin ɗan adam a matsayin abin yi wa ba'a, kuma kuna son kayan wasanku ku riƙe su cikin hannunku.
A gare mu, darajar ɗan adam da darajar haƙƙinsa, suna da yawa sosai da har muka shirya mu fafata da dukan manyan ƙasashe masu girman kai a duniya. Bayin Amurka da sauran ƙasashe masu girman kai, a cikin shekaru masu yawa, sun mulki wannan ƙasa, sun kashe ɗaruruwa, dubban mutane a kan wadannan tituna, sun zubar da jininsu a ƙasa.
A halin yanzu ma a wasu wurare, irin wannan lamari yana faruwa daga sauran bayin Amurka. Kurkukun su cike da mutane da ake zalunta; amma a tarukan duniya, babu wanda ke ɗaga murya!
Da kun kasance masu kare hakkin ɗan adam, me ya sa ba ku yi zanga-zanga ga gwamnatocin da suka koma baya, masu zalunci da mugunta, waɗanda ba su taɓa jin ƙamshin dimokuradiyya ba, kuma a ƙasarsu, alal misali, ba a taɓa sanya akwatin ƙuri'a ba?! Me ya sa kawai Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuke yi wa zanga-zanga, wadda take da 'yanci da kuma shigar da jama'a cikin al'amura, kuma tana gudanar da zaɓe na 'yanci akai-akai, kuma jama'a a tituna da tarukan jama'a, suna faɗin abin da ke zuciyarsu suna yin zanga-zanga?! Ku ba masu kare hakkin ɗan adam ba ne; ku masu goyon bayan rashin addini da kuma mamaya kan ƙasashe da al'ummomi ne. Kuna jin haushin yadda hannun muguntarku ya katse daga ƙasar Iran mai arziƙi da fadi, da kuma fargabar da kuke yi a sauran ƙasashe. Ku maƙiyan jini ne ga juyin juya hali.
Wannan juyin juya hali ya kawar da bayinku a nan. Kuna ƙiyayya da juyin juya hali; 'kuna fakewa da yancin ɗan adam ne. Me kuka sani game da ɗan adam da kuma hakkinsa? Al'ummar Iran dole su zama masu fahimta da sanin dukan ƙiyayyar wannan babbar ƙungiyar masu girman kai da maƙiyan Musulunci da juyin juya hali; kamar yadda mafi yawan mazauna wannan ƙasa, alhamdulillahi, suka fahimta kuma suka sani.
Jawabin ganawa da gungun 'yan sa kai (Basij) da ma'aikatan jinya da kuma ma'aikatan sojojin ruwa;
28 ga Nuwamba, 1990
Your Comment