Kamar yadda Ofishin Yada Labaran Hauza ya ruwaito, Mai girma Ayatullah Nouri Hamedani a cikin wani sako ga taron rufe bikin sabbin ƙirƙira a Tablig na 'Jannat' ya jaddada bukatar tallafawa ci gaba da haɓaka ayyukan tablig da kuma ɗaukaka matsayin tablig a tsakanin masana Hauza da kuma samar da kuzari da gano basirar masu tablig.
Ga rubutaccen sakon na mai girma kamar haka:
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai.
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsarki da kuma aminci ya tabbata ga shugabanmu kuma annabinmu Abul-Qasim Al-Mustafa Muhammad, da kuma iyalan gidansa masu tsarki, musamman ma Hujjar Allah a doron ƙasa (Aj), la’anar Allah ta tabbata kan maƙiyansu har zuwa ranar sakamako.
“Waɗanda suke isar da sakonnin Allah, kuma suna tsõron Sa, kuma bã su tsõron kõwa fãce Allah. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai hisãbi.” (Surah Al-Ahzab: 39)
Gaisuwa da girmamawa ga wannan taro mai daraja,
A yau daya daga cikin ayyukan Hauza shi ne batun tablig, kuma watakila manufa ta farko ga waɗanda suka yi fice (a Hauza) ita ce gudanar da aikin tablig. Sakamakon duk ƙoƙarin yana ƙunshe a cikin wannan batu; ma’ana, tun daga rana ta farko da aka shigamakarantun ilmin addinin Musulunci har zuwa lokuta na ƙarshe, a kowane mataki da matakan ilimin Hauza, aikin tablig ba ya rabuwa da mutum.
Sakamakon haka, ya kamata a lura da abin da ake buƙata don wannan aiki ya zama mai fa’ida. Ni, tare da la’akari da batutuwan zamani da ci gaban yanar gizo da sauye-sauye a hanyoyin tablig ko kuma samar da sabbin tsarin tablig, har yanzu ina da imani da wa’azi na gargajiya, wato wa’azi na ido da ido ko kuma ta hanyar mimbari.
Ina da wannan imanin cewa babu wata hanya da ta fi wannan irin wa’azin tasiri, ko da yake ba na musun tasirin hanyoyin sababbin wa’azi kamar shiga cikin yanar gizo ko ɗaukar faifai, ƙirƙirar shirye-shiryen hoto masu jan hankali da sauransu; domin yanayin da al’umma ke ciki yana nuni da tasirin irin wannan wa’azin. Amma tasirin wa’azin ta hanyar yanar gizo saboda raguwar yanayin wa’azin gargajiya ta hanyar ido da ido ne, wanda ya kamata ƙwararrun wannan fanni su bincika wannan batu.
Ya kamata masoya su lura cewa wa’azi wata fasaha ce da ke buƙatar ilimi mai yawa. A yau, a idanun wasu, ana kallon wa’azi a matsayin aikin da ya fi sauki, alhali kuwa wa’azi da jawabi da mimbari ayyuka ne mafi wahala, kuma idan muna son mu yi tasiri, shi ne aikin da ya fi kowane bukatar ƙwazo.
Mai wa’azi mai tasiri dole ne ya kware a matakai mafi girma na fannoni daban-daban, musamman ilimin adabin Farisanci da Larabci, gaba ɗaya ba tare da gibi ba. Dole ne mai wa’azi mai tasiri ya zama mai ladabi, kuma ya san yanayin zamani, ya sanya fahimtar masu sauraro a matakin farko na jawabi, kuma ya yi amfani da tushe masu inganci. Ya guji bayanin abubuwan da ba su da tushe, kuma kada ya ɗauki lokacin masu sauraro da ƙage da abubuwan da ba a san gaskiyarsu ba. Haka kuma, ya guji bayanin wasu maganganun da ba su dace da matsayin Ahlul Bait (AS) ba, ko da an ruwaito su a wani wuri. Ya lura da shakkun al’umma kuma ya ba da amsa da magana bayyananna da kuma bayanai masu tushe. Kada a yi watsi da batutuwan zamani na al’umma kamar batutuwan al’adu, siyasa da tattalin arziki saboda wai ana son tafarkin gargajiya; a’a, sai a gane cewa mai magana shi ma murya ce bayyananna a gare su.
Wani abu kuma da ya kamata a lura da shi shi ne cewa, a cikin aikin wa’azi, dole ne ya zama wata cibiya guda ɗaya ce ke gudanar da shi. Abin takaici a yau, cibiyoyi masu alaƙa da wa’azi da waɗanda ba su da alaƙa sun shiga cikin batun wa’azi, kuma wannan wata cuta ce.
Aiki ne na musamman, don haka ya kamata wata cibiya ta ɗauki alhakin wannan aiki, kuma a kawo karshen wannan halin da ake ciki.
Wani aikin da ya kamata a ba da muhimmanci shi ne, ƙwarewa a fannoni daban-daban na wa’azin kansa: dukkan masu tablig a yanar gizo, masu tablig da artificial intelligence, mai tablig ta hanyar ƙirƙirar wasan kwaikwayo mai motsi, mai wa’azi a rukunin yara da matasa. Wanda, haƙiƙa, Cibiyar Gudanarwa ta Hauzar Qom da Ofishin Tablig sun fara wasu ayyuka wanda wannan abin farin ciki ne.
A ƙarshe, ina jaddada bukatar tallafawa ci gaba da haɓaka ayyukan tablig da kuma ɗaukaka matsayin tablig a tsakanin masana cibiyoyin Hauza da kuma samar da kuzari da gano basirar masu tablig, haka kuma ina godewa duk waɗanda suka shirya wannan taro mai daraja wanda aka kira bikin sabbin ƙirƙira a tablig, ina neman nasara ga kowa daga Allah Maɗaukaki.
7 ga Disamba, 2025
Hussein Nouri Hamedani
Your Comment