Sashen Tarjima na kafar yada labarai ta Hauza ta ruwaito cewa, a ranar Lahadi, 7/12/2025 - 16/06/1447, an gudanar da taron a karo na farko tsakanin ɓangarorin biyu — Lijanuttablig Wattarbiya da Lijnar Fodiyya — domin ƙarfafa alaƙa da musayar kwarewa.
A wurin taron, an gabatar da takardu uku kamar haka:
1. Takarda ta farko:
Ta kunshi bayani game da Lijanuttablig Wattarbiya, inda ta yi nuni da:
Gabatarwa, Manufofin Lijanar, Tsarin gudanarwa, Manyan ayyukanta, Wasu daga cikin nasarorinta, Matsalolin da take fuskanta,Shawarwari don ci gaba, Da kuma kammalawa.
2. Takarda ta biyu:
Ta yi bayani kan Fodiyya, ta haɗa da:Tarihin kafuwarta. Ayyukanta, Nasarorinta,Tare da ambaton matsalolin da take fuskanta da kuma hanzozin da zäa bi a gyara.
3. Takarda ta uku:
Ta tattauna dangantakar da ke tsakanin Lijanuttablig da Lijnar Fodiyya, inda aka bayyana: Kamanceceniya ta ayyukan su Haduwar manufofinsu. Horaswa (Training), Tsarawa da shirya manhaja, Da kuma littattafan da suka dace da karatu (Mukarrar).
Manufar Taro
An bayyana manufar wannan taron da Lijanuttablig Wattarbiya ta shirya kuma ta gudanar a Markazin Imam Ridha (ع) Kano, a matsayin mataki na farko na samar da haɗin gwiwa tsakanin Lijnar Makarantun Fodiyya, ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky (H). Manufarsa ita ce kyautata alaƙa da haɓaka ƙwarewa a tsakanin ɓangarorin ilimi.
Jawabin Kammalawa
A ƙarshe, mahalarta taron sun bukaci a ci gaba da tsara irin wannan taro (Tadreeb) don ɗorewa da inganta alaƙar Lijanuttablig Wattarbiya da bayyana ayyukanta ga sauran lajnoni a sassa daban-daban na ƙasa, domin a cimma amfanin gabaɗaya.
— Daga Lijanuttablig Wattarbiya















Your Comment