A cewar wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza, Hujjatul Islam Ghulamali Safa'i Bushahri, wakilin waliyul faqih a lardin Bushahr (kudancin Iran) a yayin ganawa da dalibai a ranar dalibi ta Iran, bayan ya yi bayani kan sabbin yanayin duniya da kuma matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wannan fanni, ya jaddada cewa: Iran a yau babbar kasa ce daga cikin masu tsara tsarin duniya na nan gaba, kuma abokan gaban juyin juya halin Musulunci ta hanyar amfani da hanyoyi iri-iri na hade-haden dabaru, suna kokarin dakile tafiyar al'ummar Iran.
Hujjatul Islam Ghulamali Safa'i Bushahri yayin da yake bayyana halin da ake ciki a wannan zamani, ya ce: "Duniya na cikin wani "juyi mai muhimmanci" kuma yawancin manyan kasashe masu iko musamman Amurka, suna sake tsara dabarunsu da shirinsu na dogon lokaci."
Ya kuma jaddada cewa: "Rushewar tsarin mulkin duniya mai karkata zuwa wata kasa daya (Amurka), ya sa Iran tare da dogaro da karfin wayewarta, dimokuradiyyar addini, da karfin cikin gida, ta zama wata kasa mai tasiri wajen tantance tsarin duniya na gaba."
Wakilin waliyul faqih a lardin Bushahr da yake magana kan bambancin Iran da sauran manyan kasashe na yankin da na duniya, ya bayyana cewa: "Iran sabanin yawancin kasashe, tana da abubuwan da suka hada da karfi daban-daban da kuma bangarori daban-daban; tun daga shugabancina addini da kuma al'umma masu kumaji da iyawa, har zuwa basirar kimiyya, tarihin wayewa, yanayin kasa mai muhimmanci, da tunanin siyasa mai dogaro ga adalci da kuma ruhi. Wannan abubuwan ne suka sa Iran ke da wani matsayi mai muhimmanci a canje-canjen yankin da na duniya."
Ya kara da cewa: "Wannan karfin ya sa manyan kasashen yammacin duniya suke ta kokari ta hanyar mulkin mallaka iri-iri wanda ya hada da matsin lamba na tattalin arziki, yakin kafofin watsa labarai, ayyukan tunani, raunana al'adun al'umma da kuma kai hari ga amincewar jama'a, don dakile tafiyar Iran."
Hujjatul Islam Safa'i Bushahri lokacin da yake magana kan canje-canjen tsaro da na siyasa na baya-bayan nan, ya ce: "Masu tsarin mulkin duniya tare da shirye-shirye masu yawa a yankin da kuma samar da wasu tunanuka a cikin kasar, suna neman kifar da gwamnati, raunana karfin makaman nukiliya da kuma haifar da rashin zaman lafiya, amma basu cimma burinsu ba. Jamhuriyar Musulunci a filin ta kasance a shirye kuma ta tilasta abokan gaba ja da baya."
Your Comment