Bisa ga rahoton wakilin ofishin yada labaran Hauza, Ayatullah Sayyid Hashim Husayni Bushahri a cikin hudubanr sallar Jumu’a ranar 5 ga Disamba 2024 da aka yi a Masallacin Juma'ar Qom, ya yin ambaton haihuwar Sayyida Zahra (AS), ya ce: Haihuwar Sayyida Zahra (AS) ta zo dai-dai da haihuwar wanda ya kafa tsarin juyin juya halin Musulunci (Imam Khumaini). Haka kuma an kira wannan rana, ranar mata da uwa, domin Sayyida Zahra (AS) ita ce ’ya, mace da kuma uwa abar kwatance. Sayyida Fatima (AS) mayakiya ce a fagen gwagwarmaya, ma'abociyar tsafta da ado, jaruntaka, mai kariya ga Amirul Muminina Ali (AS) da kuma khalifanci.
Limamin Jumu’ar na Qom ya bayyana cewa: Sayyida Fatima ta haɗa halaye daban-daban, wadanda suka sanya ta zama a kan kololuwa, kuma Annabi (SAW) ya bayyana ta cewa, "Tun daga farko zuwa karshen duniya, ba za a samu wanda ya fi Fatima ba."
Yana mai nuni da cewa Sayyida Fatima (AS) tana da hali wanda kowa zai iya koyi da ita, ya kara da cewa: Imamin Zamani (AJ) dangane da Fatima (AS) ya ce: "A tattare da ’yar Manzon Allah (SAWA) akwai abin koyi mai kyau a gareni."
Shugaban kungiyar Malamai na Hauzar Qom ya bayyana cewa: Sayyida Fatima (AS) ta jure wa wahala kuma ta yi gwagwarmaya da azzalumai. Tana da juriya. Mu a matsayin mabiyanta, dole ne mu bi hanyarta.
Yana mai jaddadawa cewa dole ne matan al’ummu su yi koyi da Sayyida Zahra (AS), ya bayyana cewa: Duniyar yamma tana kallon mata a matsayin kayan talla, ba a matsayin mutum mai karamci ba. Ranar da ƙasashen yamma a cewar su suka bai wa mata ‘yanci, don inganta masana’antunsu ne, inda suka shigar da mata cikin masana’antu da albashi maras kyau.
Limamin Jumu’ar na Qom ya tunatar cewa: Matan Musulmi mabiya Sayyida Fatima (AS) ne. Duniyar jari-hujja, ‘yancin kai da fafutukar mata ba su daraja mata ko kadan, da sun yarda da hakkin mata, da ba za a sami irin wadannan abubuwan da suka faru a Gaza da Lebanon ba. Wannan sabani yana nuna cewa su magana kawai suke yi, ba sa aiki.
Mai yin huduba a sallar Jumu’a yana mai nuni da wajibcin kula da tsafta da hijabi, ya ce: Damuwa game da tsafta da hijabi na da matukar muhimmanci. Bai kamata a cikin tsarin Jamhuriyar Musulunci mu rinka ganin wasu abubuwa ba.
Ayatullah Husayni Bushahri a wani bangare na jawabinsa, yana mai nuni da girman kan Amurka, ya ce: Manufarmu game da al’amuran nukiliya a bayyane take. Amurka tana matsawa don yin tattaunawa amma abin dariya ne, domin tun da farko tana ba da umarni cewa a rage yawan sarrafa makaman nukiliya zuwa sifili, makamanku na rokoki kar ya wuce kilomita 300, kuma ku katse dangantakarku da yan gwagwarmaya.
Ya jaddada cewa: Jama’a ku kasance masu wayo, wannan ba tattaunawa bace, a’a tattaunawa ita ce yin magana ne don cimma yarjejeniya amma wannan tilastawa ne. Kada ku yi zaton cewa ta hanyar tattaunawa za a cire takunkumi. Muna tsakiyar tattaunawa ne suka fara kai mana hare-hare.
Your Comment