Friday 5 December 2025 - 00:19
Ya Kamata Makarantun Ilimin Addini  Su Rika Amsa Bukatun Al’umma Cikin Sabon Salo

Hauza/ Sakataren Babbar Majalisar Juyin Juya Halin Al’adu ya ce: Makarantun ilimin addini (Hauza) a tsawon tarihi, a koyaushe sun kasance injin motsin tunani na al’adun Musulunci kuma a yau ma dole ne su rika amsa tambayoyin bukatun al’umma cikin sabon salo da kuma tsarin bincike da ya dace.

A cewar rahoton ofishin yada labaran Hauza, an gudanar da taron baje kolin littattafan fiqhu da kalam na zamani na farko mai taken “Matsayin bincike da nazarin makarantun ilimin addini (Hauza) a cikin wayewar Musulunci,” tare da halartar Hujjatul Islam Abdul-Hussein Khosropanah, Sakataren Babbar Majalisar Juyin Juya Halin Al’adu, da malamai, masu bincike, da daliban makarantun ilimin addini.

A wannan taron, Hujjatul Islam Abdul-Hussein Khosropanah a cikin jawabinsa ya yi ishara da mahimmancin binciken ilmi a Hauza da kuma rawar da suke takawa wajen samar da wayewar Musulunci.

Sakataren na Babbar Majalisar Juyin Juya Halin Al’adu ya bayyana cewa: Makarantun ilimin addini a tsawon tarihi, a koyaushe sun kasance injin motsin tunani da al’adun Musulunci, kuma yau ma dole ne su rika amsa tambayoyin bukatun al’umma cikin sabon salo da kuma tsarin binciken da ya dace.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha