Thursday 4 December 2025 - 16:44
Me ya sa Allah baya hana zalunci?

Hauza/ Allah Maɗaukaki Ya ba wa mutum hankali da ‘yanci (ikhtiyār), kuma abin da ke tattare da ‘yanci shi ne mutum ya iya zaɓar alheri ko sharri — ko da wannan zaɓin zai kai ga zaluncin - kai ne.

Kafar watsa labarai ta Hauza ta Labarta cewa, Allah ya ga dama mutum ya zama mai inci da zabi, hakan kuma yana nufin an bashi damar yin abin da yake son yin.

Tambaya: Wani mutum yana cewa: “Bambanci tsakanin ni da Allahantaka shi ne: idan ni ina da iko, da na hana duk wani wanda zai zalunci yara; ba zan tsaya in kalli abin ba, in ce daga baya zan hukunta shi.” ya lamarin yake?

Amsa: Wannan mai tambaya yana nufin cewa: domin a duniya akwai zalunci, wasu mutane suna zaluntar wasu, to saboda haka babu Allah, domin baya hana zalunci da mugunta.
Wato yana nufin cewa idan tabbas Allah Maɗaukaki yana nan, to ya kamata ya hana duk wani zalunci da abin da zai cutar da mutane.

Bayanin Farkon: Allah Maɗaukaki ya fara halittar mala’iku, waɗanda ba su da sha’awa ko fushi ; saboda haka ba sa saba wa Allah, kuma ba sa yin zunubi. Suna yin biyayya ne kawai.
Bayan haka, ya halicci dabbobi, waɗanda aka hana musu ni‘imar hankali.

Sai tsarin halitta mafi kyau ya buƙaci cewa a halicci wani halitta da yake tsakanin wadannan biyun — yana da hankalin mala’iku da kuma buƙatun jiki irin na dabba.
Don haka Allah ya halicci mutum wanda yake da aƙida (fitra) da sha’awa da fushi (sha’wa da gābi) a cikinsa. Kamar yadda Allah Ya ce:

"فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَاهَا"

"Ya bayyana mata hanyar mummunan aiki da ta kyauttare.” (Ash-Shams: 8)

Allah ya bayyana mata hanyar mummunan aiki da ta kyauttawwla.

Saboda haka Allah Ya ba wa mutum ‘yanci da zabin (ikhtiyar) kansa – domin ya iya zaɓar hanyar rayuwarsa, ya bi ta alheri ko kuma ta mummuna. Kamar yadda Allah Ya ce:

"إِنَّا هَدَيْنَاهُ السَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرًا وَإِمَّا كَفُورًا"


"Mun shiryar da shi hanya, domin ya zama mai godiya ko mai kafirci.” Al-Insān: 3)

Allah ya nuna cewa Mun shiryar da shi hanya, domin ya zama mai godiya ko mai kafirci.

Ma’ana: mutum yana da ‘yancin zaɓi; shi ne zai zabi hanyar da ta dace ko ta bata.

Allah ya aiko manzanni da Littafi: Allah Mai Hikima bai bar mutum shi kaɗai ba; Ya aika manzanni da waliyyai domin su taimake shi wajen samun haɓakar ruhaniya da kamala. Allah Ya ce:

"وَإِنْ مِنْ أُمَّةٍ إِلَّا خَلَا فِيهَا نَذِيرٌ"

“Babu wata al’umma face wani mai gargadi ya zo cikin ta.” (Fāṭir: 24)

Wannan yana nuna cewa Allah ba ya barin mutane cikin duhu; sai dai yana ba su jagora don su san daidai.


Amma Me Ya Sa Allah Baya Hana Zalunci?
1.
Abin da ‘yanci ke nufi shi ne mutum ya iya aikata duk abin da yake so — ko da zalunci ne.
Idan Allah zai hana duk wani mugun aiki ta hanyar azabtarwa nan take — misali idan mutum ya so ya zalunci yaro sai dutse ya faɗo masa daga sama — wannan ba zai zama ‘yanci ba, kuma mutum ba zai zama halitta mai zaɓi ba.
Don haka Allah Ya bar wannan ‘yanci don mutum ya zabi abin da ya so, sannan ya ɗauki sakamakon zaɓinsa.

2. Gwaji da Sakamako, a cikin Aljanna da Jahannama, matsayin -samun rahma, da azaba sun ta’allaka ne da aikace-aikacen mutum.
Zaɓin mutum — ko alheri ko sharri — shi ne asasin lada ko azabarsa. Idan ba zai iya aikata mugunta ba, to ma’anar gwaji da sakamako ba ta da tushe.

3. Manufar Halitta: Manufar halittar mutum ita ce samun kamala (cikawa) ta hanyar bauta ga Allah da biyayya gare shi. Wannan cikawa ba ta samuwa sai an ba shi ‘yanci ya iya aikata dukkan matsayin na alheri— ko mummuna ko mafifici.
Don haka mutum yana iya kaiwa ga mafi ƙasƙanci na mugunta, ko kuma mafi girma na kyautatawa — wannan ne zai nuna gwajin gaskiya.

Kammalawa: Saboda haka, Allah Maɗaukaki baya hana zalunci kai tsaye ba don ya nuna rashin iko ba, amma saboda hikimarsa da tsarin gwaji - suka hukinta hakan.
Da haka ne Ya nufa mutum ya kasance halitta mai ‘yanci, domin ya ƙirƙiro Aljannarsa ko Jahannamarsa da hannunsa; ta hanyar zaɓinsa da aikinsa.

Manazarta: Cibiyar kirkirar bayanan kafafen sadarwa ta Tabligin Hauzozin Ilimi.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha