A cewar rahotannin ofishin yada labarai na Hauza, dubunnan mata da 'yan mata daga sassa daban-daban na kasar, da safe a ranar Laraba 12 ga watan Disamba, sun halarci Husainiyar Imam Khomeini (R) don ganawa da Ayatullah Khamene'i, Jagoran juyin juya halin Musulunci.
A wannan taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci sun bayyana Sayyada Fatima Zahra (AS) a cikin dukkan fannoni a matsayin mutum mai martaba wacce aka yi wa ado da halaye mafi girma. Ya fayyace ra'ayin Musulunci game da matsayi da haƙƙoƙin mata a cikin gida da al'umma, kuma ya bayyana abubuwan da ya kamata da abubuwan da bai kamata maza su yi wa matansu da mata ba a fannoni daban-daban.
Ayatullah Khamene'i ya yi nuni zuwa ga kyawawan halaye marasa iyaka na shugabar matan duniya da lahira biyu a "ibada da kushu'i" sadaukarwa da yafiya wa jama'a, juriya a cikin wahala da masifa, kare hakkin wanda aka zalunta da jaruntaka, wayar da kan jama'a da bayyana gaskiya, fahimtar siyasa da aikatawa, "gudanar da gida, kula da miji da tarbiyyar yara," da halartar muhimman abubuwan tarihi na farkon Musulunci" da sauran fage, ya ce: Matan Iran alhamdulillah suna koyi da kuma motsawa zuwa ga manufofinta daga irin wannan hasken rana wanda, kamar yadda Annabi (SAWA) ya ce, ita ce sarauniyar dukan matan duk zamani.
Mai girma, ya ce matsayin mata a Musulunci yana da matukar girma, kuma ya bayyana cewa: Ma'anonin Alkur'ani game da asali da halin mace, sune mafi kololuwa da girma.
Jagoran, ya yi nuni ga ayoyin Alkur'ani game da "daidaita mace da namiji a rayuwa da tarihin bil'adama da kuma daidaita mace da namiji a kan kai wa zuwa ga kamala ta ruhi da manyan muƙamai," ya ce: Duk waɗannan abubuwan suna cikin sabani da rashin fahimtar waɗanda ma'abota addini ne amma ba su san addinin ba da waɗanda gabaɗaya ba su yarda da addinin ba.
Yayin bayyana hujjar Alkur'ani game da haƙƙin mata a cikin al'umma, ya jaddada cewa: A Musulunci, a cikin ayyukan zamantakewa, kasuwanci, ayyukan siyasa, samun mafi girman mukaman gwamnati da sauran fagage, mace tana da haƙƙoƙi daidai da namiji, kuma a cikin tafiya ta ruhi da ƙoƙari da motsi na kashin kai da na al'umma, hanyoyin ci gabanta a buɗe suke.
Ayatullah Khamene'i, ya kuma yi nuni ga cewa rusasshiyar al'adar yammacin duniya da tsarin jari-hujja sun karkace gaba daya daga ra'ayin Musulunci, ya kara da cewa: A Musulunci, don kiyaye matsayin mata da kuma shawo kan sha'awar jima'i mai karfi da haɗari, akwai iyakoki da hukunce-hukunce a cikin "mu'amalar mace da namiji, tufafin mace da namiji, hijabin mace da kuma ƙarfafawa zuwa ga aure" waɗanda suka dace da yanayin mace da manufa da bukatun ainihin al'umma; yayin da a cikin al'adun yammacin duniya, shawo kan sha'awar jima'i mara iyaka da lalacewa ba a kula da su ko kaɗan.
Jagoran ya bayyana mace da namiji a Musulunci a matsayin abubuwa biyu masu daidaito tare da kamanceceniya da yawa da kuma wasu bambance-bambancen da suka samo asali daga jiki da yanayi, ya ce: Waɗannan "abubuwan biyu kammalallu" suna taka rawa wajen gudanar da al'umma, ci gaban zuriyar ɗan adam, ci gaban wayewa, samar da bukatun al'umma da gudanar da rayuwa.
Domin tafiyar da wannan aiki mai muhimmanci, ya bayyana samar da iyali a matsayin ɗaya daga cikin mafi muhimmanci, ya kara da cewa: Sabanin mantawa da cibiyar iyali a cikin kuskuren al'adun yammacin duniya, a Musulunci, ga "mace, namiji da yara" a matsayin abubuwan da ke samar da iyali, an tsara haƙƙoƙin juna.
A wani bangare na jawabinsa da ya shafi haƙƙin mata, Mai girma ya bayyana "adalci a cikin halayyar zamantakewa da na iyali" a matsayin haƙƙin farko na mata, tare da jaddada alhakin gwamnati da kowane mutum a cikin al'umma wajen tabbatar da wannan haƙƙin, ya ce: "Kiyaye tsaro, mutunci da daraja" su na daga cikin manyan haƙƙoƙin mata, sabanin tsarin jari-hujja na yammacin duniya wanda ke takaita mutuncin mace, Musulunci ya jaddada kiyaye mutuncin mace cikakke.
Da yake nuni da wata riwaya daga Annabi Muhammad (SAWA) wanda ya bayyana mace a matsayin "Fure", ba "yar aiki ko wanda ake umarni da yin ayyukan gida" ba, ya kara da cewa: A wannan hangen nesa, ya kamata a guje wa zagi da tsawa ga mata, a kula da su kuma a kare su kamar yadda ake kula da fure, domin su ma su samar da gida da launi da kuma kamshi.
Ayatullah Khamene'i, ya kawo misalin da Alkur'ani ya bayar na mata muminai biyu, Maryam da Asiya (matar Fir'auna) a matsayin misali ga dukkan maza da mata muminai da kuma nuna mahimmancin tunani da aikin mace. Ya ce: Haƙƙin zamantakewar mace kamar daidaita albashi da maza a aiki ɗaya, inshorar mata ma'aikata ko masu kula da gida, hutu na musamman na mata da sauran gomomin batutuwa, dole ne a kiyaye su ba tare da nuna bambanci ba, kuma a kiyaye su.
Mafi Muhimman Haƙƙi da Bukatar Mace a Gida Shi ne Ƙaunar Miji
Ya bayyana mafi mahimmancin haƙƙi da bukatar mace a gida a matsayin "Ƙaunar miji". Yayin da yake bayanin wata riwaya daga Annabi (S.A.W.A) wanda ke ba da shawarar maza su nuna soyayya da kuma bayyana ƙauna ga matansu, ya kara da cewa: Wani muhimmi kuma babban haƙƙin mace a gida shi ne "kin duk wani tashin hankali a kanta" da kuma guje wa cikakkiyar nisantar abin da aka saba a Yamma kamar kashe ko dukan mata daga maza da mazajensu.
Mace Ita Ce Manaja Kuma Shugabar Gida
Shugaban Musulunci ya bayyana "Guje wa tilasta wa mace aikin gida", "Taimakon miji ga mace wajen shawo kan matsalolin haihuwa" da "Bude hanya ga ci gaba na ilimi da na sana'a" a matsayin wasu haƙƙoƙin mata. Yayin da yake jaddada cewa mace ita ce manaja da shugabar gida, ya ce: Dole ne a yaba wa matan da duk da karancin kudaden shiga na mazajensu da tsadar kayayyaki, suke sarrafa gida cikin fasaha.
Ya yin bayyana banbanci tsakanin kallon tsarin jari-hujja da na Musulunci game da mata, ya bayyana cewa:
· A Musulunci, mace tana da 'yancin kai, iyawa, asali da damar ci gaba.
· Kallon tsarin jari-hujja kuma, bin sawu da narkewar asalin mace a cikin namiji ne da rashin kiyaye mutunci da kima na mace. Kuma yana kallon mace a matsayin kayan sha'awa da nishadi, wanda gungun masu laifi suke ta ihu a Amurka kwanan nan duk sakamakon irin wannan hangen nesa ne.
Ayatullah Khamene'i, ya bayyana "Rusa tsarin iyali" da samar da lahani kamar yaran da ba su san ubansu ba, raguwar dangantakar iyali, kungiyoyin farautar 'yan mata da kuma yada rikice-rikicen jima'i a matsayin 'yancin kai a matsayin manyan laifuffan al'adun jari-hujja a cikin karni daya ko biyu da suka gabata. Ya ce: Tsarin jari-hujja na Yamma, wadannan munanan ayyukan da yaudara, sun sama sunan "'yancin kai", kuma don yada shi har a kasarmu ma suna amfani da wannan take, yayin da wannan ba 'yancin kai ba ne, bauta ne.
Jamhuriyar Musulunci Ta Karyata Kuskuren Tunanin Yamma Game da Mata
Da yake ishara ga dagewar Yamma don fitar da munanan al'adunsu zuwa ga duniya, ya kara da cewa: Suna da'awar cewa iyakokin da aka kayyade ga mata game da hijabi, zai hana su ci gaba. Amma Jamhuriyar Musulunci ta karyata wannan kuskuren tunani, kuma ta nuna cewa mace musulma mai riko da tufafin Musulunci na iya tafiya da kowane fanni, fiye da wasu, kuma ta taka rawar gani.
Mai girma, ya kira nasarorin kimiyya, wasanni, tunani, bincike, siyasa, zamantakewa, lafiya da tsafta, fata a rayuwa da goyon bayan jihadi da hadin gwiwar matan shahidai masu daraja a matsayin nasarorin da ba a taba ganin irinsu ba na mata a cikin tarihin Iran.
Ya kuma bayyana cewa: A tarihin Iran ba a taba samun ko kashi daya cikin dari na wadannan mata masana, masu tunani da ra'ayi ba, kuma Jamhuriyar Musulunci ce ta haifar tare da haɓaka ci gaban mata a duk wadannan manyan fannoni.
Yayin bada wata muhimmiyar shawara, ya gargadi kafofin watsa labarai da su guji yada karkataccen tunanin tsarin jari-hujja na Yamma game da mata, ya kara da cewa: Idan aka tattauna batun hijabi da tufafin mata da hadin gwiwar maza da mata, kada kafofin watsa labarai na cikin gida su maimaita maganganun Turawan Yamma ko su bayyana su. A'a, dole ne a nuna girma da hangen nesa mai zurfi kuma mai amfani na Musulunci a cikin gida da kuma tarukan duniya. Wanda shi ne mafi kyawun hanyar yada Musulunci, kuma hakan zai haifar da sha'awar mutane da yawa na duniya musamman mata zuwa gare shi.
Kafin jawabin Shugaban Musulunci, "Matar Shahid Sardar Gholamali Rashid da mahaifiyar Shahid Amin-Abbas Rashid" da kuma 'yar Shahid Sardar Hossein Salami sun gabatar da batutuwa game da mata, ayyukansu da bukatunsu.
Your Comment