A rahoton kamfanin dillancin labaran Hauza, Ayatullah Najamuddin Tabasi a wani taro na musamman kan nazarin abubuwan da suka faru bayan wafatin Annabi Muhammad (S.A.W.W.) har zuwa lokacin da aka kashe Sayyida Fatima (A.S), wanda gungun masu binciken addini suka shirya a zauren tarurruka na gidan al’adu da ke tsangayar Alkur’ani da Ahlul Baiti a jami’ar Qom, yana mai nuni ga tushen tsarin mulki a Musulunci ya bayyana cewa: Tsarin mulkin na nuna cewa zaɓen khalifa bayan annabta ba ɗan adam ne ya ke zaba ba. Alkur’ani mai girma a aya ta 68 cikin suratul Qasas “وَرَبُّکَ یَخْلُقُ مَا یَشَاءُ وَیَخْتَارُ” ya yi ishara ga wannan batu. Hakazalika Sayyida Fatima (A.S) ita ma ta kafa hujja da wannan. Tsarin mulkin Musulunci haka yake. Mu ma a yanzu muna gaskata cewa tsarin mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran karkashin jagorancin Jagoran juyin juya hali a matsayin wakilin Imam, hukumar Allah ce, wato Imam Mahadi (A.J) shine Imam na gaskiya kuma Jagoran juyin juya hali shi ne wakilin Imam.
Wannan sashen kuma na jawabin Ayatollah Muroji Tabasi an fassara shi zuwa Hausa kamar haka:
Memba na Majalisar Malamai ta Hauzar Qom ya ci gaba da cewa: Tsarin mulkin da ya biyo bayan Annabi Muhammad (S.A.W.W) ba tsarin da ɗan adam ke da hannu ko ikon zaɓensa ba ne, a’a, al’amari ne na Allah kawai. Lamarin da ya faru a Ghadir Khum ya shafi wannan bangare na zaɓen shugaba daga wurin Allah. Idan muka duba hudubar Ghadir Khum, Annabi Muhammad (S.A.W.W) ba kawai ya naɗa Amirul Mu’minin Ali (A.S) ba ne, har ya naɗa dukkan Imaman da suka zo daga wurin Allah har zuwa ƙarshe domin jagorancin mulki da addinin Allah.
Ayatollah Muroji Tabasi, ya yin nazarin ayyukan masu adawa da masu kwace khalifancin Ahlul Baiti (A.S), ya ce: Waɗannan mutanen me suka yi? Sun kasance suna neman canza tsarin mulki da tsarin da na Allah ne. Abin da suke nufi da su mika mulki ga jama’ar musulmi, shi ne kansu, ba kowa ba, mutum biyu ko uku ko aƙalla huɗu. Tabbas, zan buga littafi da zai yi bincike kan dukkan ɓangarorin halayensu, domin kowa ya san su da kuma masu waɗanne halaye ne suka riƙe mulki da jagorancin al’umma bayan wafatin Annabi Muhammad (S.A.W.W), alhali ba su cancanta ba.
Malamin Hauza ilmiyyar ya ƙara da cewa: Waɗannan mutanen suna son su canza hanyar mulki daga ta Allah zuwa ta ɗan adam. Abin takaici ne cewa mutanen da suka riƙe mulkin musulmi ba su da tarihi mai kyau da fice a cikin Musulunci. Da ma an yi Allah wadai da muni, ko da sun iya yin wannan aiki mai girman gaske. Da ma suna da tarihi mai daraja. Da ma sun nuna jaruntaka a yaƙe-yaƙe. Da ma ba a yi musu rajista na gudu daga yaƙi ba. Da ma ba a yi musu rajista na kura-kurai ba. Duk da wannan mummunan tarihin, waɗannan mutanen ne suka riƙe mukamin mulki a cikin al’ummar Musulunci, suka riƙe sarƙaƙƙiyar al’amuran musulmi. Waɗannan mutanen ne suka canza hanyar khalifancin Annabi (S.A.W).
Memba na Majalisar Malamai ta Hauzah ilmiyyar Qom ya bayyana cewa: Sayyida Fatima Zahra (A.S) da dukan ƙarfinta ta tsaya tsayin daka domin fuskantar masu kokarin canza hanyar khalifanci daga ta Allah zuwa ta ɗan adam, kuma ta biya farashi mai tsada domin kare gaskiyar al’amarin khalifancin.
"Wayar da kan jama'a da Sayyida Zahra (A.S) ta yi na kare al'amarin khalifanci ya zama misali mai dorewa."
Yayin da ya ke nuni da mubarazar da Sayyida Zahra (A.S) ta yi da ma'abota kwacen mulki, ya ce: abin da Sayyida Fatima (A.S) ta yi ya ƙunshi gwagwarmaya da wadannan mutanen kuma ta shirya biyan kowanne irin farashi a kan ahaka, domin kawai ayar "Yā ayyuhā ar-rasūlu balligh mā unzila ilaika mir rabbik" (Ya kai Manzon Allah! Ka isar da abin da aka saukar maka daga Ubangijinka) kada ta rikide zuwa wani abu na marar daraja kamar Saqifah, inda aka yi iƙirarin cewa akwai ijma'i na musulmi, a zahiri kuma Khalifan farko ya samu khalifanci ne tare da amincewar wasu mutane kaɗan ba tare da ijma'i ba. A zahiri, wannan hanyar zaɓen khalifa ba kawai ba bisa ga nufin Allah ba ne, har ma ba bisa ga nufin jama'a ba ne. Sun sanya wa ra'ayinsu suna ijma'i, sun sanya masa suna alkawari da yarjejeniya. Amma idan muka duba gaskiya, shin naɗin khalifan farko ya kasance ijma'i? Su kansu sun ce mutum ɗaya ne. Shin naɗin khalifa na biyu ya kasance ijma'i? Su kansu sun ce mutum ɗaya ne kuma da yawa sun yi adawa da haka. A gefe guda, fito-na-fito da Hazrat Zahra (A.S) ta yi ya kasance saboda wannan batun na sauƙaƙe wannan al'amari daga na Allah zuwa na shawara. Zahra'u Dahira ta wayar da kan jama'a a kan mutanen da suke son su canza hukuncin Allah.
Malami a manyan matakan karatun Hauzar ta Qom ya yi nuni ga martani ga khalifofi da wayar da kan jama'a da Sayyida Zahra (A.S) ta yi, ya ce: Tabbas duk wanda ya jefa duniyarsu cikin haɗari, za su yi masa abin da suka saba. A cikin littatafan Ahlus-Sunnah ya bayyana cewa khalifofi ba su ba da izinin sukar su ga masu adawa ba.
Ya bayyana sarai cewa: Sayyida Zahra (A.S) ta hanyar sadaukarwa domin kishiyantar sabbin abubuwan da aka ƙirƙira (bid'a), ta bayyana hanyar gaskiya ga al'ummar Musulmi. Ta yi gargaɗi ga al'ummar Musulmi kan karɓar mulkin da ba na Allah ba da dukan sadaukarwa. Tabbas, ya kamata a sani cewa tsananin danniya a wancan lokacin ya yi yawa har babu wanda ya isa ya fito ya wayar da kan jama'a, kuma lokacin da Sayyida Zahra (A.S) ta fara wayar da kan jama'a, masu kwacen mulkin ba su iya jurewa ba, sai suka kai hari gidanta, suka haifar da waɗannan al'amuran masu ɗaci.
Ayatullah Muroji Tabasi ya yi nuni ga tasirin wayar da kan jama'a da Sayyida Zahra (A.S) ta yi, ya ce: Bayan jawabin Fatima (A.S) a masallaci, jama'a gaba ɗaya suka yi ta kururuwa: "Ba mu son kowa face Ali!" Masu kwacen mulkin sun ji tsoron kada mulki ya kubuce daga hannunsu, saboda haka sun gane lamarin Fatima Zahra (A.S.) ba lamari ne mai sauƙi ba. Sayyida da dukan ƙarfinta ta yi yaƙi da sabbin abubuwan da aka ƙirƙira na kauce hanya, da kuma bayyana gaskiya ga jama'a. Ko da yake a wancan lokacin, mutane yan kaɗan ne kawai suka amsa kirayenta, amma a yau miliyoyin mutane a duniya suna amsa kiran Sayyida Zahra (A.S).
Your Comment