Sunday 30 November 2025 - 12:55
Dogaro da Ƙarfin Cikin Gida, Sirrin Nasarar Jamhuriyar Musulunci

Hauza/ A yayin da yake jawabi dangane da nasarar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yakin kwanaki 12, limamin juma'ar Mishigan, Hujjatul Islam Sayyid Basam al-Shera ya nuna cewa karfin cikin gida da kuma jagorancin jagora mai hikima Ayatullah Sayyid Ali Khamne'i (DZ), su ne sirrin nasarar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A cewar rahoton sashen kasa-da-kasa na kamfanin dillancin labaran Hauza Hujjatul Islam Wal Muslimin Sayyid Basem al-Shara a cikin jawabinsa ya jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta hanyar dogaro ga samar da kayayyaki a cikin gida, yanke shawara cikin hikima, da kuma shugabancin Ayatullah Khamenei, ba tare da dogaro ga manyan ƙasashen waje ba, ta samu nasarar dakile barazanar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Ya kira wannan nasarar, wacce ta tabbatar da matsayin Iran a fagen yanke shawara cikin basira, a matsayin nasara mai haske. Ya yi ishara da cewa an kewaye Iran ta fuskar tattalin arziki tsawon shekaru arba'in, inda ya bayyana wannan nasarar a matsayin wata alama mai kyau ta karfin Iran.

Hujjatul Islam Sayyid Basem al-Shara ya kuma soki wasu tsoffin jami'ai da bayan kammala aikin su, suke fara kokarin nuna raunin jagorancin, inda ya jaddada cewa haɗin kai da kuma marawa Jagoran baya, shine ainihin tushen ƙarfin Jamhuriyar Musulunci.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha