A cewar rahoton cibiyar Labaran Hauza, Sheikh Ali Abbasi ya bayyana wannan batu yayin wata ganawa da baƙin ƙasashen waje a taron marigayi Mirza Na’ini (r.a), wanda aka gudanar a Jami’ar Al-Mustafa.
Ya jaddada cewa, makarantun hauza tun da daɗewa suna zama cibiyar da ake haɓaka manyan malamai masu tasiri da haske a fagen ilimi. Ya ce: Marigayi Mirza Na’ini yana daya daga cikin fitattun malamai da suka fito daga hauza kuma abin alfahari ne ga mu gaba ɗaya. Muna fatan Jami’ar Al-Mustafa a ci gabanta ta haifar da irin waɗannan malamai masu tasiri da ɗorewa.
Shugaban jami’ar ya bayyana wannan cibiyar a matsayin ci gaban ƙasa da ƙasa na hauzar ilimi, inda ya ce: "Bayan juyin juya halin Musulunci a Iran, matasa daga sassan duniya sun nuna ƙwarin gwiwa wajen zuwa karatu a hauza. Saboda haka wannan cibiya ta ilimi ta kafa tushe tun bayan nasarar juyin juya halin, kuma ta ci gaba da ayyukan ta a matakin ƙasa da ƙasa.
Ya ƙara da cewa: A halin yanzu, fiye da dubban ɗalibai daga ƙasashe sama da 130 suna karatu a Jami’ar Al-Mustafa, wanda hakan ya nuna irin bambancin ƙabilu da ƙasashe da ake da shi -a duniyar musulunci. Wannan ci gaba, a cewarsa, ya zama cikar burin tsoffin malamai wajen yaɗa asalin ilimin Musulunci da na Ahlul Baiti (A.S) a duniya baki ɗaya.
Sheikh Abbasi ya kuma bayyana cewa jami’ar tana da hulɗa da ƙungiyoyi da cibiyoyi na ilimi, addini da al’adu sama da 400, ciki har da makarantun da ba na Musulmai ba. Ya ce, misali, ana gudanar da taron ilimi tare da Jami’ar Yunnan ta ƙasar Sin duk bayan shekaru biyu.
A ƙarshe, ya jaddada cewa: Yanzu ne mafi dacewa da a nuna wannan muhimmancin - na magabatan mu, don hauza da makarantu na addini su yaɗa aƙidar Ahlul Baiti (A.S) a matakin duniya. Duk da cewa an samu ci gaba, har yanzu akwai tazara, kuma ana bukatar ƙoƙari sosai domin isa matsayi mafi dacewa.
Your Comment