Thursday 23 October 2025 - 18:57
Mata suna da tasiri kuma suna da gudumowa a fagen zamantakewar Musulunci ya shata tafarki madaidaici game da martabar mata

Hawza/ Ayatullah Subhani a cikin saƙonsa ga taron ƙasa na farko mai take "Mace da Iyali; binciken Wahayi da hankali" da aka yi a Kermanshah, ya ɗauki wannan taron a matsayin wani mataki da ya dace kuma ya lissfashi a matsayin abin koyi ga al'ummar Musulunci.

A cewar wakilin kamfanin dillancin labarai na Hawza, an gudanar da bikin rufe taron ƙasa na "Mace da Iyali; Wahayi da bincike na hankali" tare da saƙon mai girma Ayatullah Subhani a ranar Alhamis 16 ga watan Oktoba a ɗakin taro na cibiyar bunƙasa ilimin yara da matasa da ke Kermanshah (yammacin Iran). Ga Nassin saƙon Jagora Ayatullah Subhani kamar haka;

Da sunan Allah, Mai rahama mai jinƙai.

"Ya ku mutane, ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halicce ku daga rai guda ɗaya, kuma ya halitta mata matar ta daga gare ta, kuma Ya fitar da mazaje masu yawa daga gare ta da kuma mata" (Nisa'i: 1).
A wajen Musulunci, mace wata halitta ce ta Ubangiji wadda take a fage ɗaya da namiji a cikin halitta, kuma abokiyar tarayya a cikin aikin ɗorewar halittar dlɗan Adam, Alkur'ani ya jaddada cewa, dukkan biyun an halicce su ne daga rai guda; "Ni ne na halicce ku daga rai guda ɗaya, kuma na halitta mata matarta daga gare ta", don tunatar da cewa babu wani bambanci a tsakanin su a zahirin bil'adama da kuma iya samun kamala.

Cibiyar Musulunci ta hanyar gabatar da Sayyida Fatima Zahra (as) a matsayin abin koyi ga mace mumina kuma mai tunani, ta tsara tafarki madaidaici ga darajar mace. Ita wannan baiwar Allah, yayin da ta kasance mai tsafta da tawali’u, ta kasance majagaba a fagen ilimi, imani, kariya ga wilaya, da tarbiyyar al’ummar muminai, don haka ta nuna cewa “mata” na iya zama tushen shiriya da farkar da al’umma.

Dangane da wannan gaskiyar, makarantun jari-hujja da al'adun Turawan yamma, ta hanyar yanke kansu daga wahayi, da yanayi, da tsantsar hankali, sun takaita matsayin mata a cikin farfajiyar iyakokin jin daɗi da riba, kuma sun kore tsarin iyali daga tsarki da ma'anarsa. Sakamakon irin wannan ɗabi’a shi ne rugujewar alaƙa ta ɗa’a da raunana tushen iyali a cikin al’ummomin yau.

Kamar yadda addinin Musulunci ya koyar, mata ma suna da tasiri da kuma taka rawa a fagen zamantakewa. Don haka, mata da maza dukkansu su ne masu samar da bukatu na zamantakewa kuma dukkansu su yi wa al’umma hidima; sai dai fa'idar hidimar daga duka biyun ta bambanta, kuma yarda da wadannan nau'ukan bambance-bambancen da ƙoƙarin girmama su, shi ne babbar hidima ga mata - ta basu matsayinsu, da -kuma baiwa maza matsayin su, kuma shi ne adalci.

A yau, ganin yadda ake ci gaba da yawaitar tambayoyi da maida hankali kan al’amuran “mata da iyali”, al’ummar Musulunci, fiye da kowane lokaci, tana buƙatar sabunta nazari abisa ilimi kan “haƙiƙa da matsayin mata da iyali” bisa koyarwar Alƙur’ani da hikima mai tsafta.

Gudanar da taron ƙasa na "Mace da Iyali; Bincike na Wahyi da Hankali" a birnin Kermanshah wanda ya shahara a duniya, wani mataki ne da ya dace kuma mai ban sha'awa kan wannan al'amari. Babu shakka tattaunawa ta ilimi da nazari mai zurfi a bisa tunani, idan aka tsara ta bisa dalilai na hankali da wahayi, #za su iya zama fitila da kuma abin koyi ga al'ummar Musulunci.

Ina mika godiyata ga dukkan masu tunani, malamai, masu bincike, musamman zaɓaɓɓun mata masu ilimi da suka tsunduma cikin wannan taro domin yin tunani a kan "Mata da Iyali", ina mai matuƙar jinuna daga birnin zuciya, kuma ina fatan sakamakon wannan tattaunawa ya zama tushen albarkar ilimi da al'adu ga al'ummar musulmi, kuma zai yi tasiri wajen karfafa cibiyar iyali mai tsarki da kuma daukaka matsayin mata musulmi..

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ba duk wanda ke da hannu a wannan yunƙuri mai ƙima, ya ƙara samun nasara kuma ya sanya kowa ya samu nasarar hidimar Alkur'ani da zuriya da kyawawan daɓi'u na iyali.

Assalamu alaikum, wa rahamatullahi wa barkatuhu.

Jafar Sobhani

Hauza Qum

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha