Monday 2 February 2026 - 20:56
An Gudanar da Taron Kasa da Kasa na Mataimakan Imam Mahdi (Ansarul Mahdi) a Masallacin Jamkaran

Hauza/ Taron kasa da kasa na Ansar al-Mahdi ya gudana a Masallacin Imam Mahdi na Jamkaran, tare da halartar tarin dalibai da masu bincike daga kasashe da dama na duniya.

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, taron kasa da kasa na Ansarul Mahdi ya gudana ne a daidai lokacin bikin maulidin Hazrat Baqiyatullah al-Azam (Ajtfs), kuma a cikin yanayi na ruhaniya da kuma nishadi, tare da halartar dalibai da malaman addini da 'yan kasashen waje daga kasashe daban-daban.

A yayin wannan taron, Shugaban masallacin na Jamkaran,Hujjatul Islam wal-Muslimin Ajaqnejad, yayin jawabin sa, ya yi ishara ga muhimmancin ranar Nisfus Sha'aban da kuma rawar da Juyin Juya Halin Musulunci ke takawa a matsayin shirye-shiryen zuwan Mahdi, sannan ya jaddada bukatar tarbiyantar da masu imani da kwarewa domin taimakon Imamuz Zaman (Ajfs).

Haka kuma, Hujjatul-Islam wal-Muslimeen Rafi'i, a jawabin sa, ya bayyana cewa imani da bayyanar Mahdi (Imam Mahdi) yana daya daga cikin aƙida ta gama-gari a tsakanin addinan Allah, kuma ya bayyana ayyukan masu jira (Muntazirun) a matsayin sanin ya kamata, soyayya, da kuma himma, tare da jaddada rawar da makarantun Hauza ke takawa wajen yada al'adar Intizar 

Wannan taron ya kasance tare da shirye-shiryen al'adu da na ruhaniya da suka hada da karanto musibar da ta samu Ahlul Baiti, rera wakokin yabo, waka, da addu'o'i, sannan mahalarta sun bayyana soyayyar su ga Hazrat Waliyul Asr (Ajtfs), tare da bayyana shirin su na taka rawa a hanyar shirya zuwansa.

Taron Ansarul-Mahdi an yi shi ne domin karfafa dangantakar dalibai na kasa da kasa da al'adar Mahadawiyya da kuma bayyana wazifar masu jira (Muntazirun)a zamanin Gaba.

An Gudanar da Taron Kasa da Kasa na Mataimakan Imam Mahdi (Ansarul Mahdi) a Masallacin Jamkaran

An Gudanar da Taron Kasa da Kasa na Mataimakan Imam Mahdi (Ansarul Mahdi) a Masallacin Jamkaran

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha