Tuesday 27 January 2026 - 20:46
Tabbataccen Imani Mai Zurfi, Shi Ne Kadai Inshorar Mutum Lokacin Hujumi

Ayatullah Shabzandedar, a taron daliban Hauza, ya bayyana cewa babban aikinsu a matsayinsu na ɗalibai shi ne "gina kai mai zurfi" da kuma "shiryar da al'umma da imani da basira" ya ce: "Dalibai sun fi fuskantar shakku, canje-canjen fikira da hujumi daga makiya, kuma abin da kawai ke zama kariya shi ne tsayayyen imani kuma mai zurfi."

Ofishin Yada Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Ayatullah Muhammad Mahdi Shabzandedar, sakataren majalisar koli ta makarantun Hauza, a taron malaman makarantun Hauza da dalibai, yayin da yake taya murnar bukukuwan watan Sha'aban, yana mai jaddada irin karfin da dalibai suke da shi na ci gaban ruhi da kuma rawar da suke takawa a zamantakewar al'umma, babban aikin su shi ne karfafa imani, inganta basira, kididdige zuba jari na Ubangiji da kuma canzawa zuwa abin koyi a aikace, ya bayyana cewa: Hauza zata kai ga matsayinta na hakika ne kawai lokacin da dalibai tare da iko, muhimmantarwa, da sani suka bi hanyar neman yardar Allah da kuma hidima ga mutane."

Mamban kwamitin Shari'a na majalisar kare kundin tsarin mulki da yake bayyana aikin dalibai da kuma muhimmancin gina kai ya ce: "Matukar mutum bai damfara kansa da gaskiya ba, ba zai yi niyya zuwa gare ta ba; Haka nan, idan dalibi bai san matsayinsa na ilmi ko na ruhi ba, ba zai taba cimma wannan matsayi nasa ba. Sharadi na farko don motsawa zuwa ga buri shine sha'awa da nuna kulawa ga shi."

Haka nan kuma yayin da yake ishara da addu'o'in watannin Rajab da Sha'aban, ya kara da cewa: "Wadannan addu'o'in suna fadakar da jama'a irin girman da suke da shi da kuma karantar da su cewa za su iya samun matsayi na ruhaniya. Wannan kulawa ita ce mafarin motsin ɗan adam da kuma daukakarsa."

Ayatullah Shabzandedar ya jaddada cewa: "Manufar dalibai ba wai kawai ta takaita ne ga ci gaban mutum daya kadai ba. Tare da imani da takawa da ruhi, su zama abin koyi a aikace ga al'umma kuma da wannan babban rabo na Ubangiji su rike hannun mutane da shiryar da su zuwa ga tafarkin gaskiya da daukaka."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha