Monday 5 January 2026 - 17:40
Muhimman Siffofi Guda Uku Na Gwamnatin Sarkin Muminai (AS) A Idon Wani Mai Bincike Dan Ahlus-Sunna

Hauza/ Maulawi Ruhul Amin, a cikin jawabin da ya yi, ya jaddada cewa tarihin rayuwar Sarkin Muminai Sayyidina Ali (AS) ya wuce kawai labarin tarihi; babban abin koyi ne a aikace ga adalci, daukar nauyi, da kuma yakar zalunci ga shugabancin yau.

Bisa rahoton sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, Maulawi Ruhul Amin, mai binciken addinin Musulunci kuma shugaban gidauniyar "AIMAY" ta kasar Indiya, a yayin tattaunawa da Ofishin Yada Labaran Hauza, ya jaddada cewa rayuwa da tarihin Sarkin Muminai Sayyidina Ali (AS) sun wuce kawai abin alfahari na tarihi, a'a, za su iya zama jagoran aikace-aikace ga shugabanci da tafiyar da al'umma a yau.

Ya kara da cewa: Mayar da hankali kan adalci, sauke nauyin da aka rataya a wuya, da kuma tsayin daka a gaban zalunci, sune fitattun koyarwar da ke cikin littafin Nahjul Balagha kuma misalai ne wadanda ba su da tamka na wannan tsari na shugabanci.

Tambaya: Yaya za ka bayyana Sarkin Muminai Sayyidina Ali (AS) a matsayin "Madubin Shugabancin Musulunci"?

Ruhul Amin: Da farko, ina mika godiyata ga Ofishin Yada Labaran Hauza saboda samar da wannan dama. Sayyidina Ali (AS) ba kawai shugaban siyasa ba ne; shi wani rayayyen samfuri ne na shugabanci da ya ginu a kan adalci da tsoron Allah (takawa). Akwai siffofi guda uku fitattu a cikin gwamnatin sa da ya kamata a yi nazari a kansu:

1. Shugabanci a kan Tushen Tsoron Allah (Takawa): Sayyidina Ali (AS) ya sha jaddada cewa "shugabanci dole ne ya kasance tare da zurfin tsoron Allah," kuma kowane mataki da za a dauka, dole ne ya kasance a cikin tsarin kiyaye dokokin Allah da adalci.

2. Alaka ta Kurkusa da Mutane: Shi kansa ya kasance yana fita zuwa kasuwa, yana duba farashin kayayyaki, kuma yana binciken matsaloli da bukatun mutane da kansa. Wannan hulda ta kai-tsaye tana ba shi damar yanke shawarwari na adalci da kuma amsa bukatun al'umma cikin gaggawa.

3. Jajircewa da Sauke Nauyi: Sayyidina Ali (AS) ya taba fada cewa: "Kafin shugaba ya ji kukan wani rauni (talaka), ya kamata ya yi murabus daga mukaminsa." Wannan mahanga tana nuna irin nauyin da ya dauka a wuyansa da kuma yadda yake kula da halin da al'umma take ciki.

Tambaya: A cikin gwamnatin Sayyidina Ali (AS), har zuwa wane mataki ne adalci ya kasance babban ginshikin siyasarsa?

Ruhul Amin: Adalci shi ne kashin bayan gwamnatin sa. Daya daga cikin fitattun takardu na tarihi, ita ce wasikar da Sayyidina Ali (AS) ya aike wa Malik al-Ashtar, wacce a cikinta ya fito fili ya ce: "A cikin al'amuran da ba ku da ilimi a kai, ku guji tsoma baki." Wannan wasika tana nuna cewa ana kiyaye adalci ba kawai a tsakanin abokai da mabiya ba, har ma ga makiya.

Misali, akwai lokacin da aka tsinci sulken (rigar yaki) Sayyidina Ali (AS) a shagon wani Bayahude. Lokacin da aka gabatar da maganar a gaban kotu kuma aka kasa tabbatar da akasin haka, koda yake alkali na daya daga cikin wadanda Sayyidina Ali (AS) ya nada ne, sai alkali ya yanke hukunci da bawa Bayahuden nasara. Shi kuwa Sayyidina Ali (AS) ya amshi hukuncin ba tare da wata jayayya ba. Wannan babban misali ne na kiyaye adalci dari bisa dari da kuma girmama doka.

Gwamnatin Sayyidina Ali (AS) wani misali ne da ba shi da tamka na shugabanci mai kwarjini da sanya karsashi, kiyaye tsoron Allah, tuntuɓar mutane kai-tsaye, da kuma jajircewa kan adalci. Wannan salon shugabanci ba wai kawai a tarihin Musulunci ba, har ma a duniyar yau ana kallonsa a matsayin cikakken samfuri na shugabanci na gari da mutuntaka. Wannan salon mulki yana nuna cewa adalci da dabi’un kwarai a fagen siyasa za su iya zama ginshiki mai karfi na gina al'umma mai albarka da adalci.

Tambaya: Yaya Sayyidina Ali (AS) yake kiyaye daidaiton tattalin arziki da adalcin zamantakewa a cikin gwamnatinsa?

Ruhul Amin: Sayyidina Ali (AS) ya sha jaddada cewa: "Dukiyar kasa amana ce daga wajen Allah." Da wannan mahanga ne ya samar da tsarin raba dukiya na adalci daga asusun gwamnati (Baitul-Mali). Har ma a lokacin da ake ware kason kudi ga mambobin iyalansa, ya kasance yana kiyaye wadancan ka'idoji na adalci.

Misali, lokacin da dan uwan Sayyidina Ali (AS) ya nemi a kara masa kaso (fiye da na kowa), sai ya tambaye shi: "Shin kana so ne a tauye hakkin mutane?" Ya ware kaso na musamman ga rukunin mutane masu rauni a cikin al'umma kamar matalauta, marayu, da zawarawa, sannan ya tabbatar da adalci da gaskiya a dukkan matakan shugabanci.

Tambaya: A ra'ayinka, har zuwa wane mataki ne koyarwar tattalin arziki da zamantakewa ta Sayyidina Ali (AS) take da amfani a yanayin duniyar yau, musamman a ƙasashen Musulmi?

Ruhul Amin: Waɗannan koyarwa suna da matuƙar amfani da kuma samar da mafita. Idan har shugabannin gwamnati a yau za su karanta wasiƙun tsare-tsaren siyasa na Sayyidina Ali (AS) kuma su yi aiki da su, za su iya rage cin hanci da rashawa, mulkin kama-karya, da rashin daidaito matuƙa. Shi kansa (AS) yana cewa:

"Idan shugaba ya kasance mai mulkin kama-karya, ƙasa za ta lalace; kada ka ci amanar amincin mutane, in ba haka ba faɗuwarka tabbas ce." Waɗannan ƙa'idoji saƙonni ne na duniya baki ɗaya ga shugabannin yau, kuma suna nuna cewa shugabanci ba zai dore ba muddin ba a kiyaye adalci da ɗabi'un ƙwarai ba.

Tambaya: A ra'ayinka, wace siffa ce ta musamman a halayen Sayyidina Ali (AS) wacce shugabannin yau za su iya amfana da ita?

Ruhul Amin: Akwai halaye guda uku na musamman na Sayyidina Ali (AS) wadanda a koda yaushe za a iya yin koyi da su:

1. Ilimi da Hikima: Sayyidina Ali (AS) an san shi da "Babul-Ilm" wato "Kofar Ilimi". Dukkan shawarwarin da yake yankewa a gwamnatinsa yana yin su ne tare da dogaro da ilimi, fadakarwa, da tunani mai zurfi. Wannan mahanga tana nuna muhimmancin ilimi a fagen shugabanci da tafiyar da al'umma.

2. Jajircewa da Tsayin Daka a Gaban Rashin Adalci: Jajircewar sa wajen tunkarar zalunci da rashin adalci ba ta da tamka. Misali, a yakin Siffin, lokacin da dakarun makiya suka tare hanyar ruwa har sojoji suka fara jin kishirwa, Sayyidina Ali (AS) ya bayyana cewa: "Ruwa hakki ne na kowa." Wannan shawarar babban misali ne na jajircewa a fannin dabi'u da kuma tsayuwa kan adalci koda a lokacin tsananin tashin hankali ne.

3. Adalci da Halin Dattaku: Mahangar Sayyidina Ali (AS) game da adalci da halayensa na dattako, babban abin koyi ne ga shugabancin yau. Kiyaye adalci da girmama hakkin wasu, har ma a yayin fuskantar makiya, yana ba da darussa masu muhimmanci ga manajoji da shugabannin duniya, kuma yana nuna cewa iko ba tare da adalci da dabi’un kwarai ba, ba zai dore ba.

Tambaya: Ta yaya matasa za su iya yin koyi da rayuwa da tarihin Sarkin Muminai Sayyidina Ali (AS)?

Ruhul Amin: Da farko, ya kamata matasa su karanta littafin Nahjul Balagha, wanda yake daya daga cikin fitattun littattafan adabi da falsafa a duniya. Sayyidina Ali (AS) a koda yaushe ya kasance "abokin matasa", kuma ya yi amanna da iyawa, baiwa, da kuzarin matasa. Za a iya koyan darussa guda uku na asali daga rayuwarsa:

1. Shugabanci Nauyi Ne, Ba Shakatawa Ba: Mulki da iko ba su taba zama hanyar samun jin daɗin kai ba; a'a, shugabanci yana tafiya ne tare da jajircewa da kuma bayar da amsa ga mutane.

2. Hikima Ce Sharadin Samun Iko: Idan babu ilimi da hikima, iko na iya kaiwa ga mummunar barna da lalata.

3. Mafi Girman Jihadi Shi Ne Tsayuwa A Gaban Zalunci Da Kare Gaskiya: Tunkarar zalunci da mulkin kama-karya yana bukatar jajircewa da kuma riko da dabi’un kwarai.

Maganar Ƙarshe

Tsarin shugabanci da gwamnatin Sayyidina Ali (AS) ba kawai wani labari ne na tarihi ba; jagora ne na aikace-aikace kuma mai muhimmanci ga siyasa da tafiyar da al'umma a duniyar yau. Tarihin rayuwarsa yana nuna cewa gwamnatin Musulunci za ta dore kuma ta yi nasara ne kawai idan aka tafiyar da ita tare da hadin gwiwa tsakanin adalci, son dan adam, da kuma hikima. Koyarwar Alawiyya tana tabbatar da cewa shugabanci na Ubangiji da na dabi'un kwarai zai iya zama samfuri mara tamka wajen samar da al'umma mai adalci, mutuntaka, da cigaba.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha