Tuesday 6 January 2026 - 08:23
Littafin "Al-Ghadir" Ya Toshe Kowace Kofa Ta Musanta Wilayar Sarkin Muminai Ali (A.S)

Hauza/ Hujjatul-Islam Khurrami Arani, yayin da yake ishara da littafin "Al-Ghadir" na Allamah Amini, ya bayyana shi a matsayin wani aiki na musamman kuma katanga mai karfi wajen kare karkata tarihin Musulunci.

A cewar Ofishin Yada Labaran Hauza a garin Sari, Hujjatul-Islam Hassan Aqa Khurrami Arani, a wata hira da ya yi da manema labarai yayin zagayowar ranar haihuwar Sarkin Muminai Ali (A.S), ya jaddada muhimmancin bayyana matsayin sa na tarihi da na akida. Ya bayyana cewa: "Gagarumin littafin nan mai dauke da mujalladai da dama wato 'Al-Ghadir' wallafar Allamah Amini, wani babban gadon ilimi ne da aka rubuta shi da nufin kare hakkin Sarkin Muminai Ali (A.S) da kuma tabbatar da halifancinsa na take (bayan Manzo). Babban abin lura shi ne cewa dukkan majiyoyi da littattafan da aka dogara da su a cikin wannan littafi, an dauko su ne daga littattafan malaman Ahlus-Sunna."

Wannan malami ya yi nuni da irin kokarin da ba shi da tamka na Allamah Amini wajen bincike, inda ya ce:

Marigayi Allamah Amini ya kasance yana yin bincike na tsawon sa'o'i 17 a kullum. Ya karanta kusan littattafai 10,000 daga farko har karshe. Ya yi nuni (reference) ga littattafai fiye da 100,000 akai-akai.

Tasirin wannan littafi ya kai ga cewa, an ruwaito cewa bayan wallafa mujalladi guda kacal a kasar Lebanon, adadi mai yawa na ‘yan uwa Ahlus-Sunna sun koma mazhabar Shi’a sakamakon hujjoji masu karfi da ke cikinsa.

Hujjatul-Islam Khurrami Arani ya kara da cewa: "Asalin tsarin littafin Al-Ghadir ya kunshi mujalladai 20, wadanda zuwa yanzu guda 11 ne aka buga, yayin da sauran guda 9 ba su fito ba tukuna. Allamah Amini da kansa ya nanata cewa asalin muhimman bayanai suna cikin wadancan mujalladai 9, sannan wadannan 11 da ake da su tamkar shimfida ce gare su."

Yayin da yake jaddada karfin ilimin littafin na Alghadeer bayyana cewa:" Duk da cewa bayanan littafin ba za su yi wa wasu dadi ba, amma saboda dogaro da majiyoyi ingantattu, a cikin kusan shekaru 60 da wallafa shi, babu wani mutum ko kungiya da ta iya yin raddi na ilimi ko da a shafi daya na littafin. Wannan aiki ya samu yabo ba kawai daga malaman Shi’a ba, har ma da manyan malaman fikihu, masana hadisi, da ma jiga-jigan siyasa na Ahlus-Sunna.

Malamin na Hauza ya bayyana cewa: "Allamah Amini ya toshe kowace kofa ta musanta ghadir wilayar Imam Ali (A.S). Sannan ya kafa wa kowa hujja ta hanyar fitar da hadisin Ghadir daga sahabbai 110, tabi’ai 84 da kuma masu ruwaya 360 daga littattafan Ahlus-Sunna tun daga karni na biyu har zuwa na goma sha hudu bayan hijira. Wannan yawan adadin hadisi ya sa hadisin ghadir ya zama mutawatir.

Hujjatul Islam Khurrami-Arani ya kara da cewa: "Allamah Amini ya kasance yana jaddada cewa a ranar kiyama zai yi koke da jayayya da makiya Sarkin Muminai Ali (A.S), domin sun cinye masa lokacinsa; domin kuwa da ba don haka ba (da ba don musantawar su ba), da ya karkata dukkan kokarinsa wajen yada kyawawan koyarwa da ilimomin Imam Ali ne kawai, maimakon ya tsaya kawai wajen tabbatar da asalin shugabancinsa (Imamanci). Lallai Allamah Amini wani babban mutum ne da ya tsaya shi kadai gaba-da-gaba da masu karkata tarihi, kuma da alkalaminsa mai karfi, mai ma'ana, kuma mai tasiri, ya bayyana hakikanin gaskiyar da aka boye a cikin duhun tarihi, inda ya tabbatar wa duniya baki daya halifancin Imam Ali (A.S) na take (ba tare da wani tazara ba)."

A karshe, Khurrami Arani ya yi nuni da hadisin Ghadir: "Duk wanda nake shugabansa (Maulahu), to wannan Ali shugabansa ne," yana mai jaddada cewa wannan lamari shi ne ginshikin tantance magajin Manzon Allah (S.A.W.A).

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha