A cewar rahoton sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, an gudanar da taron daga tutar ne a safiyar yau Lahadi (8 ga watan Rajab, 1447 H / 29 ga watan Disamba, 2025) a babban haramin Imam Ali (AS) karkashin taken "Ala Hubbi Aliyyun" (Akan soyayyar Ali). Wannan taro shi ne mafarin shirye-shiryen "Makon Walidul Ka'abah" domin taya murnar haihuwar Sarkin Muminai Imam Ali (A.S).
A wurin taron, Sayyid Isa al-Khurasan, babban daraktan haramin, ya halarta tare da mataimakinsa, mambobin hukumar amintattu, shugabannin sassa, da kuma gungun malamai da fitattun masana da shugabannin al'umma.
An gudanar da taron ne tare da karatun ayoyin Al-Kur'ani mai girma, jawabi daga Haidar al-Isawi, mamba a hukumar amintattu, kan batun sabunta alkawari da biyayya ga Imam Ali (A.S), tare da rera wakokin yabo na addini
A cewar rahoton, "Makon Walidul Ka'abah" zai kunshi jerin shirye-shirye na addini, al'adu, da bukukuwan murna na jama'a. Haka kuma, za a kaddamar da wasu ayyukan jin dadin jama'a da dama a fadin lardin Najaf mai alfarma a yayin wannan mako.
Your Comment