A cewar Ofishin Yada Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammadi Golpayegani, shugaban ofishin Jagoran Juyin Juya Hali, a cikin jawabin da ya yi a lokacin kaddamar da harabar Sayyidah Zahra (A.S) a haramin Imam Ali (A.S) da ke Najaf al-Ashraf, ya bayyana cewa:
"A wannan majalisi, ya zama dole in gode wa babban marji'i Ayatullahil Uzma Sistani kan sanarwar da ya fitar a lokacin yakin kwanaki 12, lokacin da Amurka ta yi barazana ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci; inda ya fitar da sanarwa wadda ofishinsa ya yada."
Wani bangare na rubutaccen bayanin Ayatullah Sistani da kuma kalaman Hujjatul Islam Muhammadi Golpayegani a wajen taron kaddamar da harabar Sayyidah Zahra (A.S) a Najaf al-Ashraf na cewa:
"Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai. Har yanzu, ina yin tir da kakkausan lafazi ga ci gaba da wuce gona da iri na soji ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma kowace irin barazana ta keta alfarmar rayuwar babban jagoran addini da siyasa na wannan kasa."
Ayatullah Sistani a cikin wannan sanarwar ya yi gargadi mai tsanani cewa:
"Kowane irin mataki na laifi makamancin wannan, baya ga kasancewa keta dokokin addini da na dabi'u a bayyane, da kuma keta ka'idoji da dokokin kasa da kasa, zai haifar da sakamako mai muni sosai ga daukacin yankin."
Wannan ita ce sanarwar Ayatullah Sistani. Ina so in bayyana muku cewa shi (Ayatullah Sistani) yana da irin wannan matsaya da ra'ayi (game da Jagora).
Godiyar Shugaban Ofishin Jagoran Juyin Juya Hali Ga Matsayar Ayatullahil Uzma Sistani Wajen Goyon Bayan Jagora
Hauza/Hujjatul Islam Muhammadi Golpayegani ya nuna godiyarsa ga matsayar da Ayatullah Sistani ya dauka na goyon bayan Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, inda ya bayyana cewa: "A tsakiyar yakin kwanaki 12 da barazanar Amurka ga Jagora, wannan babban marji'i ya fitar da wata sanarwa ta tarihi domin goyon bayansa."
Your Comment