A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, an gudanar da taron bude cibiyar da fara ayyukanta na bincike na "Cibiyar Binciken Ilimin Kalam ta Imam Ja'afar al-Sadiq (A.S)" a safiyar yau a dakin taro na gidauniyar Imam Ja'afar al-Sadiq (A.S) da ke Qum. A wajen taron, Ayatullah Ja'afar Subhani, daya daga cikin manyan maraji'a, ya yi bayani kan dabi'u guda biyu na dan adam, inda ya bayyana ra'ayin Musulunci game da daukakar tunani da ta dabi'u.
Jaddada Bangarorin Tunanin Dan Adam da Sha'awace-sha'awace daga Mahangar Musulunci
Ya bayyana cewa: "Allah Madaukakin Sarki yana cewa a cikin Kur'ani mai girma: 'Kuma a cikin kasa akwai ayoyi ga masu yakini, da kuma a cikin kawunanku, shin ba kwa gani?' Dan adam ya kunshi bangarori guda biyu ne: bangaren tunani da kuma bangaren sha'awace-sha'awace. Masana falsafa suna girmama bangaren tunani na dan adam inda suke kiransa da 'Dabba mai magana' (mai tunani), sannan malaman tarbiyya da dabi'u (akhlak) su ma suna mayar da hankali kan bangaren dabi'unsa. Musulunci kuwa yana bayar da muhimmanci ga duka bangarorin biyu; wato bangaren tunani da kuma bangaren dabi'u."
Ayatullah Subhani ya ci gaba da kafa hujja da ayoyin Kur'ani inda ya ce: "Allah yana cewa a cikin Kur'ani: 'Lallai a cikin halittar sammai da kasa da sauyawar dare da rana, akwai ayoyi ga masu hankali', sannan a wata ayar kuma yana vcewa: 'Da rai da abin da Ya daidaita shi, sai Ya sanar da shi fajirancinsa da takawarsa'. Don haka, makarantar Musulunci cikakkiya ce domin tana kula da duka bangarorin biyu; tana rainon tunani sannan tana jagorantar sha'awace-sha'awace ta hanyar da take daidai."
Bincike mai Tasiri; Shi ne Babban Ma'aunin Bincike a Makarantun Hauza
Wannan Marja'in, yayin da yake ishara zuwa ga ayyukan sabuwar cibiyar bincike ta ilimin Kalam ta Imam Ja'afar al-Sadiq (A.S), ya bayyana cewa: "Wannan zama a zahiri yana da alaka ne da bangare na farko, wato bangaren tunani da bincike. A wajen bincike, dole ne a kiyaye wannan ka'ida a koyaushe; cewa a zabi jigon bincike ta yadda zai kasance mai tasiri ga al'umma kuma ya zama mai amfani gare ta."
Ya kara da cewa: "Idan akwai wasu jigogi wadanda ba sa taimaka wa ci gaban tunanin al'umma ko kuma ba a bukatar su a halin yanzu, to ya kamata a sanya su a matsayin abubuwan da za a duba a nan gaba. Dole ne bincike ya kasance mai amfani ta fuskar ruhi da kuma fuskar rayuwa ta zahiri."
Bukatar Bayar da Muhimmanci ga Ilimin Kimiya da na Ruhi a Bincike
Wannan malamin na Hauza ya ci gaba da bayani game da fadin bincike a Musulunci, inda ya ce: "Kowane mai tunani da mai bincike dole ne ya yi tunani game da al'amuran halitta (kimiya) domin ya bunkasa su, sannan kuma ta fuskar ilimi da tunani ya dukufa ga al'amuran ruhi. Don haka, ginshikin tunani da bincike dole ne ya kunshi bangarorin biyu: tattaunawa kan abubuwan halitta da kuma bangarorin ruhi da na tunani."
Ci gaba na Gaskiya ya Dogara ne ga Kula da Ilimin Kimiya Bisa Tafarkin AlKur'ani
Wannan Marja'in ya yi nuni da gafalar da Musulmi suka yi a daruruwan shekarun farko game da ma'anonin kimiya da ke cikin Alkur'ani, inda ya bayyana cewa: "Ci gaba na gaske na kowace al'umma ya dogara ne ga kula da abubuwan halitta da kuma amfani da su ta hanyar da ta dace."
Ayatullah Subhani, yayin da yake kafa hujja da ayoyin Kur'ani wadanda suke cike da ishara zuwa ga abubuwan halitta, ya bayyana cewa: "Abin takaici, Musulmi a daruruwan shekarun farko ba su ba da muhimmanci sosai ga bangarorin halitta da na kimiya na ayoyin Alkur'ani ba.Alhali Alkur'ani yana tattaunawa kan al'amuran halitta (nature) daki-daki. Ci gaban al'umma yana bukatar ta tashi zuwa ga fagen binciken halitta kuma ta yi amfani da shi domin kyautata rayuwa."
Gargadi game da Kwaikwayon Yamma da Jaddada Dogara ga Kai
Wannan Marja'in ya bayyana cewa babban sharadin ci gaba shi ne kula da ilimi bisa ka'ida, inda ya yi gargadi: "Dole ne mu shiga fagen ilimi ta hanyar da take daidai, kuma kada mu kasance masu tsananin sha'awar bin Yamma. Mu kanmu muna da ingantattun tushen tunani. Dole ne mu kasance da 'yancin kai na tunani da na ilimi, kuma kada buri da bin salon Yamma ya yi tasiri ga al'umma."
Sake Nazarin Gadon Tunani na Musulunci da Sukar Kwaikwayo Tsantsa
Ayatullah Subhani ya kawo misali daga tarihin falsafar Yamma inda ya ce: "Misali, mutanen Yamma suna yaba wa Descartes sosai wanda mafarinsa shi ne kokonto na gaba daya. Wannan ra'ayi an riga an bayyana shi a cikin ayyukan masana falsafar Musulunci tun kafin shi kuma ta hanyar da ta fi zurfi. Dole ne mu shigo ta hanyoyin da aka koya mana a cikin falsafa da tunani na Musulunci."
Ya ci gaba da cewa: "Sake nazari akan gadon ilimi da falsafa na wayewar Musulunci, tare da bayar da muhimmanci ga ilimin kimiya a karkashin tsarin koyarwar Alkur'ani, shi ne babban dabarar samun ci gaba ta kowane fanni."
Jarin Rayuwa da Hankali: Lambun da Ya Kamata a Yi Amfani da Shi
Yayin da yake nuni ga ni'imomin Ubangiji, ya ce: "Dan adam yana da jarin da ake kira 'Rayuwa' da 'Hankali'. Kamar yadda ake tsinkar 'ya'yan itace daga bishiya, haka ma ya kamata a tsinki fa'idodin ilimi da na aiki daga wannan babban jari."
Ya kara da cewa: "Al'ummomin yau, ko a fagen ilimin kimiya ko a fagen ilimin hankali, ba su iya tsinkar wadannan 'ya'yan itace yadda ya kamata ba, kuma ba su samu sakamakon da ake bukata daga wannan jari da Allah Ya ba su ba a aikace."
Alkur'ani Mai Girma Littafin Shiriya ne Zuwa Ga Tunani
Malamin ya bayyana Alkur'ani a matsayin littafin da yake shiryarwa zuwa ga tunani mai amfani, inda ya kafa hujja da ayar da ke cewa: "…da muryar dare da rana, da jiragen ruwa wadanda suke gudana a cikin teku da abin da yake amfanar mutane, da abin da Allah Ya saukar daga ruwan sama sai Ya raya kasa da shi bayan mutuwarta… lallai akwai ayoyi ga mutane wadanda suke yin hankali." Ya bayyana cewa Alkur'ani bai takaita ga ambaton abubuwa kawai ba, a'a, yana nuna hanyar tunani da kuma sakamakon tunanin wanda shi ne sanin Allah.
Muhimmantar da Matsalolin da Suka Shafi Al'ummar Musulmi a Yau
Wannan Marja'in ya bayyana ga malamai da masu bincike cewa: "Ina rokon dukkan mahalarta da su zabi jigogi da matsaloli domin bincike wadanda a yau, ko kuma a nan gaba kadan, suke zama 'matsala' ga al'ummar Musulmi. Magance matsalolin da ba su da muhimmanci na gaggawa, a bari zuwa wani lokaci."
Barazanar Yau; Daga Shubuhohin Wahabiyanci Zuwa Yakin Ruhi na Yanar Gizo
Ayatullah Subhani, yayin da yake nuni ga misalan wadannan barazana a fili, ya kara da cewa: "A yau, muna fuskantar matsin lamba daga bangaren kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi kamar Wahabiyanci, wadanda ta hanyar karkatattun fassarori suke kin wasu daga cikin sahihan koyarwar Musulunci. Haka nan kuma muna fuskantar matsaloli da shubuhohi masu yawa da ake yadawa a yanar gizo. Wadannan su ne jigogin bincike na gaggawa da ya zama dole a mayar da hankali kansu tare da yin bincike mai zurfi a kansu."
Daga karshe, yayin da yake bayyana fatansa ga bincike na makarantun Hauza, ya jaddada cewa: "Sakamakon wadannan bincike mai manufa dole ne a aiwatar da su tare da isar da su ta yadda al'ummar Musulmi za su amfana da 'ya'yan binciken a fili."
Your Comment