A cewar rahoton wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza daga Bushehr, Hujjatul Islam Wal-Muslimin Ghulam-Ali Safayi Bushehri, a yayin ganawarsa ta yau da Nasser Abu Sharif, wakilin kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinu a Iran, ya yi ishara da sunnonin Ubangiji a cikin halitta inda ya ce: "A tsarin halitta, akwai wata tabbatacciyar ka'ida, ita ce rayuwa, daukaka, da nasarar kowane abu ya dogara ne ga jajircewa. Wannan dokar Ubangiji ce da ta shafi komai tun daga kan dabi'a har zuwa ga al'ummomin bil-Adama. Idan babu jajircewa, babu wata halitta da za ta iya dorewa."
Ya kafa hujja da ayoyin Alkur’ani da tarihin annabawa inda ya kara da cewa: "Dukkan annabawan Allah, tun daga kan Annabi Ibrahim, Musa, da Isa (A.S) har zuwa kan fiyayyen halitta Manzon Allah (S.A.W.A), sun sami nasara ne ta hanyar jajircewa akan azzalumai da masu girman kai. Allah ya yi alkawarin cewa zai taimaki addininsa ta hanyar muminai masu jajircewa, kuma taimakon Allah yana tabbata ga wadanda suka tsayu akan gaskiya."
Wakilin Waliyyul Faqih a jihar Bushehr, yayin da yake tsokaci kan batun Falasdinu, ya bayyana cewa: "Abin da ya sa al'ummar Falasdinu take raye kuma take tsaye a yau, ba makamai na zamani ba ne, a'a, imani ne, da hadin kai, da kuma jajircewar al'umma. Yana yiwuwa makiya su kasance suna da fifiko ta fuskar kayan yaki, amma al'ummar da take tare da Allah, ba za ta taba shan kaye ba."
Ya jaddada cewa: "Babu wani bambanci a tsakanin al'ummomin musulmi; Falasdinawa, 'yan Lebanon, 'yan Iran, da kowane musulmi da yake tafiya akan tafarkin Musulunci da kare wanda aka zalunta, duk suna sahu daya ne. AlKur’ani mai girma da sunnar Manzon Allah sun bayyana cewa duk wanda bai damu da al’amuran musulmi ba, to baya cikinsu."
Hujjatul Islam Wal-Muslimin Safayi Bushehri, yayin da yake yin ishara da abubuwan da suka faru a tarihi, ya ce: "A farkon Musulunci, musulmi sun yi nasara a yakin Badar duk da karancin yawansu saboda sun jajirce, amma sun sha kaye a yakin Uhudu saboda rauni wajen tsayin daka. A yake-yaken zamanin nan ma, duk inda aka samu jajircewar al'umma, to ana samun nasara, duk kuma inda aka kawar da mutane aka bar su a gefe, to ana samun kaye da rugujewa; kamar yadda Tarayyar Sobiyet (Soviet Union) ta ruguje duk da karfin da take da shi a zahiri, saboda ba ta da goyon bayan al'umma."
Ya kara da cewa: "Isra'ila da masu mara mata baya, musamman Amurka, sun ginu ne akan rudun iko. Wannan gwamnati (Isra'ila), sabanin yadda take tallata kanta, ba ta da wanzuwar gaske, kuma tana nan ta ruguje a gaban nufin al'ummomi masu jajircewa."
Daga karshe, Hujjatul Islam Wal-Muslimin Safayi Bushehri ya jaddada muhimmancin hadin kan al'ummar musulmi, inda ya bayyana cewa: "Batun Falasdinu, batu ne na dukkan musulmi da dukkan 'yantattun mutane na duniya, kuma kare birnin Kudus (Quds) wani nauyi ne na addini, na dan adamtaka, kuma na Ubangiji."
Wakilin Waliyyul Faqih a Jihar Bushehr:
Jajircewa (Mukawama) Ita Ce Sirrin Dorewa da Nasarar Al’ummar Falasdinu
Hauza/Wakilin Waliyyul Faqih a jihar Bushehr ya bayyana cewa: "Jajircewa ita ce sirrin dorewa da nasarar al’ummar Falasdinu."
Your Comment