Sunday 14 December 2025 - 23:59
Taron Mauludin Sayyida Fatima Zahra (SA) a Bangladesh Ya Kayatar

Hauza/Sakamakon munasabar Mauludin Sayyida Fatima Zahra (SA), an gudanar da kayataccen taron mauludin a Bangaladesh wanda manyan malamai, masana da kuma ɓangarori daban-daban na al'umma suka halarta. An gabatar da jawabai akan tarihinta, da jaddada yadda za a ɗaga darajar kyawawan dabi'u da mutuntaka a cikin al'umma.

A cewar rahoton sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, an gudanar da kayataccen taron mauludin Sayyida Zahra (SA) a makarantar koyar da kirkirar kyale-kyale dake garin Jashur na Bangaladesh. Taron ya samu halartar Mallamai, masana da kuma mutane daga ɓangare daban-daban. A yayin taron an bayyana sirar wannan mai mace girma, sannan kuma aka jaddada wajibcin gabatar da ƙimar kyawawan dabi'u da mutuntaka a tsakanin al'umma.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha