Saturday 13 December 2025 - 21:41
'Ya'ya Mata da Maza Su Kasance Masu Godiya ga Dawainiyar Iyaye

Hauza/Babban Malamin addini, Ayatullah Jawadi Al-Amoli, ya yi gargadi ga 'ya'ya mata da maza da su kasance masu godiya ga dawainiyar (kokarin) uba da uwa.

A cikin rahoton da Ofishin Yada Labaran Hauza ya bayar, Ayatullah Jawadi Al-Amuli ya bayyana mahimmancin da mutunta iyaye ke da shi, yana mai cewa: "Dangane da uba da uwa, ko da yake wahalar (dawainiyar) da uba ke sha wajen samar da masauki, abinci da tufafi ba ƙarama ba ce, amma wahalar daukar ciki, haihuwa da shayarwa wahala ce mai tsanani. Wannan ya kamata a lura da shi domin 'ya'ya maza su yi godiya, kuma 'ya'ya mata su san cewa ita ma za ta fuskantar irin wannan hanya."

A cikin surar Alƙur'ani mai girma ta "Luƙman", a inda aka yi maganar shawara ga iyaye, an ambaci wahalar uwa. Aya ta goma sha huɗu (14) a surar "Luƙman" ta ce: "Kuma Mun yi wa ɗan adam wasiyya game da iyayensa," sannan ta ambaci wahalar uwa: "Uwarsa ta ɗauke shi cikin rauni a kan rauni, kuma ta yaye shi cikin shekaru biyu. "Ka yi godiya a gare Ni da ga iyayenka.""

(Hakazalika), ya kamata 'ya'ya maza su fahimci darajar uwa, kuma 'ya'ya mata su koyi al'adar zama uwa daga wannan labari.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha