A cikin rahoton da sashin fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza ya bayar, Ayatullah Hafiz Sayyid Riyad Hussain Najafi, Shugaban Kungiyar Makarantun Shi’a na Pakistan, a yayin hudubar sallar Juma’a a Masallacin Jami’i Ali (AS) da aka yi a birnin Lahore na kasar Pakistan, ya bayyana tasiri marar misali na Mai Martaba Abu Dalib (AS) wajen karewa da kuma yada addinin Musulunci. Ya ce: “Musuluncin yau, yana godiya ga ƙoƙarin Mai Martaba Abu Dalib (AS), sannan kuma da sadaukarwar ’ya’yansa masu tsarki. Addini ya kafu ne da ƙoƙarinsa, kuma ya ci gaba da sadaukarwar zuriyar Abu Dalib (AS).”
Da yake nuni ga tarihin farkon Musulunci, ya ce: “Bayan Mai Martaba Abdul-Muttalib, kulawar Manzon Allah (SAWA) yana da shekaru takwas ya zama alhakin Mai Martaba Abu Dalib (AS), kuma ya kasance mai tausayi da kulawa ga Annabi (SAWA) har ma ya fi kula da shi fiye da ’ya’yansa. Wanda ya fara yin waka da yabo ga Annabi (SAWA) shi ne Abu Dalib (AS), kuma littafin wakokin Abu Dalib ya ƙunshi fiye da dubun baiti na wakokinsa. Ayatullah Riyad Najafi ya kara da cewa, Abu Dalib (AS) ya ci gaba da tarbiyya da goyon bayan Annabi (SAWA) har tsawon shekaru arba’in, kuma Alkur’ani mai girma ma ya yi ishara ga wannan kariya da kulawar.”
Ya ci gaba da jawabinsa yana mai nuni ga sukar Nasibawa, ya ce: “Laifin Abu Dalib (AS) a wajen wannan rukuni shi ne cewa shi ne mahaifin Amirul Muminina Ali (AS). Kuma tun da Amirul Muminina (AS) ya kasance a duk lokaci a kan gaskiya kuma yana adawa da ƙungiyoyin bata, sai makiyan suka kai wa mahaifinsa hari, suka yi masa karya da kiran shi kafiri.”
Shugaban Kungiyar Makarantun Shi’a ya kuma yi nuni ga babban matsayin kakannin Annabi (SAWA) ya kara da cewa: “Daga cikin manyan ayyukan Hashim, akwai ciyar da mahajjata, kuma bayansa, Mai Martaba Abdul-Muttalib ya kasance fitaccen mutum wanda ya taka muhimmiyar rawa a lokacin harin Abraha da 'As'habul fil'. Shi ma ya kafa wasu al’adu waɗanda daga baya Alkur’ani mai girma ya tabbatar da su, ciki har da haramcin auren matar uba, wajibcin biyan khumusi da kuma ɗawafi a Ka’aba.”
A ƙarshe, Ayatollah Hafiz Riyad Najfi da yana nuni ga sahihan hadisai ya ce: “Bayan rasuwar Mai Martaba Abu Dalib (AS), Annabi (SAWA) ya ce: ‘Allah da ni, mu biyu mun tabbatar da lada da sakamakonsa.’”
Your Comment