Saturday 6 December 2025 - 20:52
Masu Yada Rashin Hijabi da Tsiraici Yan Kutsen Maƙiya

Hauza/ Mai jawabi a Harami Mai Tsarki na Sayyida Ma'asuma (SA) ya bayyana cewa idan kamewar 'ya'ya mata ta lalace, iyali da tsatso masu tasowa za su halaka, ya ce idan mace ta kasance mai kiyaye hijabi, mai taƙawa da kiyaye addini babu wanda zai iya bautar da ita. Wasu mutane 'yan kutsen shaiɗan, suna yada fasadi a tattalin arziki da rashin hijabi domin su cutar da kasar, a rufe da sunan Musulunci.

Bisa ga rahoton wakilin ofishin yada labaran Hauza, Hujjatul Islam Wal Muslimin Murteza Aghatehrani, shugaban kwamitin al’adu na majalisar dokokin Iran, a wani taro na ilmantarwa game da rasuwar Sayyida Ummul Banin (S.A) a Harami Mai Tsarki na Sayyida Ma'asuma, ya yi nuni da rawar da uwa ke takawa a gaba daya al’umma da tsatso masu zuwa, ya bayyana cewa: Kasancewar Sayyida Zahra (S.A) uwar wannan al’umma ce, kuma mu mukan dauki kanmu al’ummar ta, akwai buƙatar hasken wannan Mai girma ya kasance a cikinmu.

Mai jawabi a Harami Mai Tsarki na Sayyida Ma'asuma, yayin nuni ga wata riwaya game da halittar Shi’a, ya kara da cewa: A cikin riwayar an ce, “Shi’atuna khuliqoo min fazili ɗinatina”, ma’ana Shi’armu an halicce su ne daga yalwar yumbunmu. Don haka kowannenmu yana da rabo daga Imam Sadiq, Imam Baqir, Amirul Muminina da Imam Mahdi (AS). Dole ne mu kula don kada mu rasa wannan haske.

Hujjatul Islam Wal Muslimin Aghatehrani ya ci gaba da cewa: A ranar kiyama, wata ƙungiya daga munafukai za ta ce wa masu imani: “Unzuroona naqtabis min noorikum”, ma’ana ku jira mu mu sha haskenku. Amma ana gaya musu: “Irji’oo wara’akum faltamiso noora”, ma’ana ku koma duniya ku nemi haske. Amma a can babu komawa, kuma dama ta ƙare. Don haka idan wani yana son ya sami haske, dole ne ya same shi a duniya.

Yana mai jaddadawa cewa khalifancin Allah hanya ce daya tilo ta samun haske, ya ce: Allah ne majiɓincin muminai, kuma dole ne mutum ya kasance ƙarƙashin khalifancin Allah da waɗanda Allah ya umarta; wato Annabi da Amirul Muminina. Duk wanda ba wannan ba dawagitai ne, kuma dagutu yana jawo mutum daga haske zuwa duhu. Wanda shi kansa yana cikin duhu, kamar Trump da Netanyahu, ta yaya zai iya su kai wasu ga haske?

Hujjatul Islam Wal Muslimin Aghatehrani ya yi nuni da cewa mutane masu haske ne kuma dole ne su kiyaye hasken, ya kara da cewa: Abin da ke kashe haske shi ne bin dagutu, Wasu mutane a duniya masu ƙirƙira ayyuka ne waɗanda ke wa abokan gaba aiki.

Yayin magana da mata, ya ce: Ku kula kada su ja ku zuwa ga rashin kiyaye hijabi. ’Yan mata masu fafutuka na duniya ba za su taɓa ɗaukar matsayin mata kamar yadda Musulunci ya yi ba. A Musulunci mace tana da matsayi wanda misalinsa shi ne Sayyida Zahra (S.A); babban abin koyi ga duniya da lahira.

Hujjatul Islam Wal Muslimeen Aghatehrani ya yin nuni ga halin Ummul Banin (S.A), ya bayyana cewa: Wannan mace da kanta ta ce tana ɗaya daga cikin bayin Sayyida Zahra (S.A). Lokacin da ta shiga gidan Amirul Mu’minina (A.S), ta ce wa ’ya’yan wannan mai girma: “Ban zo ne don in maye gurbin mahaifiyarku ba, a’a na zo ne in zama baiwarku.” Wannan abin alfahari ne da kuma girman irin na wannan mace.

Yana mai suka kan koyi da wasu matasa daga taurarin yamma, ya kara da cewa: Idan kamewar ’ya’ya mata ta lalace, iyali da tsatso masu zuwa za su halaka. Amma idan yarinya ta kasance mai kiyaye hijabi, mai taƙawa kuma mai addini, babu wanda zai iya bautar da ita. Tana iya a kama ta kamar Sayyida Zainab (S.A) a, amma ba za a taɓa wulakanta ta ba, kuma za ta tsaya ta tunkari abokan gaba.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha