Bisa rahoton sashen fassarar ofishin dillancin labaran Hauza, rashin yarda da dawo da ƙimar Isra'ila sakamakon laifuffukan cin mutuncin ɗan Adam da ta yi a Gaza, ya sa wannan gwamnatin shan jini ta wuce gona da iri, take kokarin aiwatar da hare-hare kan Musulmi a wasu sassan duniya. Sakamakon wadannan mugun ayyuka zai iya shafar kowane ɓangare na al'umma.
Jama'ar Faransa har yanzu suna cikin rudani sakamakon binciken jin ra'ayin jama'a mai abin kunya da cibiyar binciken ra'ayin jama'a ta Faransa (Ifop) ta gudanar a kan al'ummar Musulmi, a karkashin kulawar Yahudawa masu tsattsauran ra'ayin, an fitar da wasu shaidun da ke nuna cewa hukumar leƙen asiri ta Mossad tare da taimakon masu tsattsauran ra'ayin Yahudanci da ke zaune a Farasa, na yin leƙen asiri da tattara bayanai daga Musulmi da yanayin ayyukansu da rayuwarsu, kana a mika wadannan bayanan da aka tattara zuwa Isra'ila.
Wasu hasashe sun nuna cewa ana tattara wadannan bayanan daga kowane ɓangare na al'umma.
A cewar Majalisar Musulmin Faransa, wannan binciken wasu mutane biyu ne ke kula da shi, ɗaya daga cikin su ma'aikacin Sahayoniya ne. An bayyana wannan binciken da "mai haɗari kuma mara misaltuwa," a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar kana an jaddada cewa an fallasa wadannan bayanan a lokacin da ya dace. Waɗannan ayyuka ana ci gaba da tsara su ne daga Sahayoniya, sannan a tura zuwa kafofin watsa labarai domin nuna wariya da kabilanci a kan Musulmi da Musulunci.
Majalisar Musulmin Farasa ce ta fitar da wannan sanarwar, kuma an yi ta yada wani bidiyo a shafukan sada zumunta, wanda a cikinsa wani mutum da ake iƙirarin cewa sunan sa Didier L'Ange ya fallasa cewa tun farkon shekarar 2023 yana bincike da aiki a kan al'ummar Musulmin Faransa da kuma kokarin haifar da rikici ta hanyar kafofin watsa labarai a kansu, kuma ya gana da Musulmai da yawa da ke da mukamai.
Tushen: An ɗauko daga ofishin labaran Al-Shorouk.
Your Comment