A cewar Kafar watsa Labaran ta Hauza, Kalmar "Salama", wannan abin da ɗan Adam ke nemansa a koyaushe ne, kalma ce da ke ratsa zuciyar kowane mutum, amma ma'anarta koyaushe tana kasancewa cikin duhu da sarƙakiya. A cikin duniya - a yau za'a ga yadda sarƙakiya da hayaniyarta ke ƙara fitowa fili a kowace rana, wannan tambaya mai tushe tana bayyana fiye da kowane lokaci: Menene ke kawo wa ɗan Adam Salama?
Wannan tambaya mai sauƙi, amma mai zurfi, ita ce farkon buɗe taga zuwa ga tunani mai tsabta.
A cikin wannan mahallin, mun tattauna da Hujjatul Islami wal-Muslimin Hadi Hussein Khani, ɗaya daga cikin masana a fannin ɗa'a - da kyautata dabi'u, domin jin ra'ayinsa game da salamar ɗan Adam.
Bayan mun yi godiya da jinjina a gare ku saboda damar da kuka ba kafar yada Labarai ta Hauza, za mu ci gaba da jigon tattaunawar ta hanyar wannan tambaya mai muhimmi:
“Menene ke kawo wa ɗan Adam salama?”
Bismillahir Rahmanir Rahim
Akwai dalilai da yawa da ke taka rawa a cikin salamar ɗan Adam. Ɗaya daga cikin waɗannan dalilai da aka ambata a cikin Alƙur'ani mai girma shi ne samun mata (ma'aurata).
Allah Maɗaukakin Sarki ya ce a cikin Suratul Rum mai albarka
(Aya ta 21):
{وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ}
"Kuma daga cikin ayoyinSa akwai Ya halicce muku matan aure daga jinsinku domin ku natsu zuwa gare su, kuma Ya sanya a tsakaninku soyayya da rahama. Lalle, a cikin wancan akwai ayoyi ga mutanen da suke tunani."
Wannan salama, nau'i ne na musamman da ba a samunta sai ta hanyar aure na shari'a da kuma dangantaka mai kyau. Sabanin haka, mummunar dangantakar da abin takaici ta yaɗu a cikin ƙasashen Yamma har ma da wani ɓangare a cikin al'ummarmu, ba zai taɓa kawo wa ɗan Adam salama ta hakika ba.
Abin da ake samu a cikin dangantaka marasa kyau, kawai kwantar da hankali ne na ɗan lokaci ga buƙatun ɗan Adam na halitta; kwantar da hankali wanda ba na hakika ba ne, kuma ba mai kawo salama ba ne. A gaban haka akwai Tunawa da Allah Maɗaukakin Sarki; don samun - Salama Ɗaya Tilau Mai Dorewa.
Tunawa da Allah Maɗaukakin Sarki
Ɗaya daga cikin hanyoyi na asali don kai ga salama shi ne tunawa da Allah Maɗaukakin Sarki. Kamar yadda Allah Ya ce, ackin (Suratul Ra'ad, Aya ta 28):
{أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ}
"To, da ambaton Allah ne zũkãta ke natsuwa."
Babu shakka, abin da aka samu ta hanyoyi marasa kyau, kawai yana iya zama kwantar da hankali na ɗan lokaci ga buƙatun ɗan Adam na halitta; amma wannan kwantar da hankali, ba na hakika ba ne kuma ba ya kawo salama mai dorewa. Daga cikin wasu abubuwa da suke da gaske - suna kawo salama ga ran ɗan Adam, akwai tunawa da Allah Maɗaukakin Sarki.
Lokacin da ɗan Adam ya shiga cikin tsakiyar matsaloli da kuma guguwar wahalhalu, abin da ke ba shi salama shi ne wannan yaƙinin cewa Mai Taimakon sa Allah Maɗaukakin Sarki ne; wani dogaro mai ƙarfi wanda zai iya kawar da kowace matsala daga gaba da kuma cire kowane cikas daga hanya.
Idan mutum ya tuna da - kadai, Allah da kuma manyan siffofinsa, kamar Ilimi mara iyaka, Ƙarfi marar ƙarewa da Alheri da Darajarsa, sai ya gane cewa babu wata matsala da za ta dore kuma babu wani kunci da ba za a iya buɗewa ba a gaban nufin Allah.
Sallah, Magani Mai Warkar da Tashin Hankali
Daga cikin mafi girman alamun tunawa da Allah, akwai Sallah.
Allah a cikin Alƙur'ani mai girma ya yi nuni da wannan gaskiya, acikin (Suratul Baƙarah, Aya ta 45):
{وَاسْتَعِينُوا بِالصَّبْرِ وَالصَّلَاةِ ۚ}
"Kuma ku nẽmi taimako da haƙuri da salla..."
Sallah, mafaka ce da ke ɗaga ruhi zuwa sama kuma a cikin kariyarta, tana dawo da salama ga zukatansu masu damuwa. Don haka, wasu daga cikin manyan Malaman addini, idan suka fuskanci matsaloli, suna komawa ga Sallah kuma a cikin hasken wannan haɗin gwiwa na sama, Allah yana ba da salama ga rayukansu.
A zahiri, a gaban waɗannan abubuwan - dake kawo salama, akwai kuma abubuwan da ke haifar da rashin salama ga ɗan Adam.
Mantawa da Allah, ƙin aure da rasa dangantaka ta iyali mai kyau, da kuma ƙaunar duniya da kwaɗayi a kan dukiya, suna daga cikin waɗannan dalilai.
Duk yadda mutum ya yi kwaɗayi, maimakon samun salama, sai ya ƙara zama mai tashin hankali; domin koyaushe yana cikin tunanin yadda zai ƙara dukiyarsa da yadda zai kiyaye ta, kuma waɗannan tunane-tunanen maimakon kawo salama, suna kwace salamar daga gare shi.
Your Comment