Friday 28 November 2025 - 19:02
Manyan Maraji'an Najafi da Qum a yau su ma kamar Na'ini, katanga ce mai ƙarfi a gaban harin masu girman kai ga Iraki, Iran da duniyar Musulmi

Hawzah/ Shugaban Hawzar Iran ya ce: Na'ini sau da yawa ya tsaya tsayin daka a gaban Birtaniyya, kuma a duk lokacin da 'yancin Musulunci da darajar al'ummar Musulmi suka kasance cikin haɗari, manyan malaman Najafi, Qum da sauran manyan makarantun ilimi a duniyar Musulmi, suna kare shi da rayukansu da kuma ƙarfinsu. A yau kuma manyan maraji'anmu masu daraja a Najafi da Qum, katanga mai ƙarfi ne a gaban harin masu girman kai ga Iraki, Iran da duniyar Musulmi.

A cewar wakilin kamfanin dillancin labaran Hawzah daga Iraki, Ayatullah Arafi a taron kasa da kasa kan masanin bincike Mirza Na'ini a  Najaf Ashraf wanda aka gudanar a dakin taro na Alawi na ginin Alawi a birin Najaf Ashraf kuma tare da halartar manyan mashahuran malamai na Hawzah, ya bayyana manyan halayen mutumci na Mirza da kuma rawar da ya taka a fagen ilimi, zamantakewa da siyasa, sannan ya jaddada matsayinsa na musamman a tarihin manyan makarantun ilimin addinin Islama.

 Shugaban na Hawza bayan ya yi maraba da masu halarta da baƙi na taron da kuma malamai, masana, da wakilan manyan maraji'an addini a Najaf Ashraf da Qum da kuma gidan (iyalan) Imam Khomeini (R), da ofishin jagoran juyin juya halin Musulunci da gidan Ayatullah Mai Girma Sistani da ofisoshinsa a Najaf da Qum da musamman ma Atabar Imam Ali da imam Husain (AS) masu tsarki da sakataren janar na taron da wakilin iyalan Ayatullah Na'ini da duk wadanda suka halarci taron da kuma nuna godiya ta musamman ga goyon bayan Ayatullah Sistani na gudanar da taron da dai sauransu, ya jaddada cewa gudanar da irin wannan taro, baya ga girmamawa da kuma sanin manyan mashahuran malaman Hawzah da mashahuran masu tunani da gyara a tarihin Musulunci da Shi'a, har ga gabatar da manyan makarantun ilimin addinin Islama (Hawza) ga mutanen duniya da tsatso masu tasowa da jami'o'i.

Ya bayyana cewa: Baya ga haka, zai ƙarfafa tushen asalin Musulunci da na Hawzah a cikin Hawzah da kuma cikin al'umma masana. Haka kuma zai zama abin koyi ga sabbin tsatso na malaman Hawzah, domin zai sanar da su game da jihadin malaman Hawzah a fagagen ilimi da jihadin zamantakewa da siyasa, kuma zai zama kamar fitila mai haske a gaban malaman Hawzah zuwa ga makoma mai haske.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha