Kamfanin dillancin labaran na Hawza, ya bayar da rahoton cewa, Ayatullah Araki ya bayyana a taron da wakilai da jami'an farfagandar Hawza suka halarta cewa: "Mafi samun nasara acikin makaman maƙiya, shi ne makamin yaƙin tunani.
A fagen fama na soja, maƙiya su ne masu hasara, kuma idan aka faɗaɗa yaƙin zuwa fagen fafatawa, to mu ne za mu yi nasara. Abin da ke hana samun nasara shine ayyukan yaƙin tunanin da maƙiya ke aiwatarwa kafin a ƙwama.
Ya ƙara da cewa: "Maƙiya suna raunana mu da yaƙin tunani, haifar da ruɗani, tsoro, raunana ra'ayi, da kuma sanyaya gwiwar mutane, kayan aikin maƙiya kenan." Daya daga cikin manyan ayyukanmu a fagen yaɗa saƙonni shi ne, yaƙi da wannan yaƙin na tunani. Dole ne maƙiya su sani cewa muna da ƙarfi da gaske.
Ayatullah Araki ya ci gaba da cewa: Wajibi ne mu bayyana juyin juya halin Musulunci da dacewa da kuma nasarorin da ya samu ga al'umma, musamman ma matasa, wajibi ne matasa su san dalilin da ya sa maƙiya suke ƙiyayya da wannan juyin, wajibi ne mu bayyana tushen ƙiyayyar -maƙiya-, ta yadda imani da basira za su ƙara ƙarfi a cikin sabbin - hanyoyin zamani.
Yayin da yake fito da misalan irin wulaƙancin da wasu gwamnatoci suka yi wa Amurka, dan majalisar ƙoli ta Majalisar Dattijai ya bayyana cewa: Taron na Sharm el-Sheikh ya bayyana ƙarara na wulaƙanta wasu shugabannin ƙasashe ga Trump, inda ya wulakanta shugabannin ķasashen musulmi, yayin da su kansu suke aiki tuƙuru cikin hidimar sahyoniyawa da Amurka, shugaban ƙasar Masar wanda ya kwashe shekaru da dama yana ƙoƙarin kawar da Gwa'gwarmayar, a wajen Trump ba shi da wani mutunci ya sha wulaƙanci.
Ayatullah Araki ya ƙara da cewa: Ƙasashen duniya baki daya sun yabawa Iran da rashin halartar wannan taro, wannan karramawa ita ce abin girba daga imani da 'yancin kai na al'ummarmu, wajibi ne mu yi nazari kan irin ayyukan da muka yi a fagen yaƙin tunani da irin matakan da ya kamata mu ɗauka.
Your Comment