A cewar rahoton sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin Allama Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta shirya tare da gudanar da taron tunawa da waki'ar Buhari. taron wanda aka gudanar da shi a dakin taro na Sayyida Zahra (SA) na Haramin Sayyida Ma'asuma an gudanar da shi ne da yammacin Juma'a, 12 ga Disambar 2025 inda manyan mutane daban-daban da suka hada da Wakilin Waliyul Faqih a Afirka, Hujjatul Islam Wal Muslimin Mehdivi-Pur, shugaban sashen al'adu na Jami'ar Al-Mustafa Hujjatul Islam Ridha'iy, Hujjatul Islam Sulaymany da sauran su suka halarta suka kuma gudanar da jawabai.
Hujjatul Islam Mehdivi-Pur, Wakilin Waliyul Faqih a Afirka yayin da yake gabatar da jawabinsa a taron, ya ce "Muna cikin ranakun haihuwar Sayyida Zahra (SA) wacce ita ce farkon shahidiyar kare wilaya".
A ci gaban jawabinsa ya bayyana cewa Musulunci da kuma hanyar Ahlul Bayt (AS) suna ci gaba ne da hasken shahidai wanda ya bayyana su a matsayin hasken da yake haskaka hanyar, tun daga kan A'immatu Ahlul Bayt musamman shugaban shahidai, Imam Hussain (AS) zuwa ga sauran shahidan wannan tafarki wanda shahidan Zariya yanki ne daga cikin su.
Hujjatul Islam Mehdivi-Pur ya bayyana cewa ta hanyar jagorancin Jagora mai hikima, Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i da yawan al'ummar Afirka sun fahimci cewa ba wata ƙasa da take taimakon raunana da wadanda ake zalunta sai jamhuriyar Musulunci ta Iran, musamman ma bayan ta'addancin Isra'ila a Gaza da kuma yaƙin kwanaki 12. Duk da taimakon kasashen NATO da ma sauran ƙasashe amma Isra'ila ta kasa yin nasara a kan jamhuriyar Musulunci, wanda ya nuna dakewar shahidai kuma karfin soji da takanolojin Iran a idon duniya.
Ya kuma bayyana Allama Sayyid Ibraheem Yaaqub Zakzaky (H) a matsayin wata shaksiyyar da irin ta nada qarancin samuwa a tarihi; mtum ne da ya kore a shugabanci, gudanarwa, tsari da kuma sadaukarwa. Wanda ya sadaukar da 'ya'yansa shida a wannan tafarki. a karshen jawabin sa, ya yi addu'a ga Jagoran da kuma Harkar Musulunci a Nijeriya da fatan ta cimma hadafofinta ta kuma kara yaɗuwa ba kawai a Nijeriya ba har ma da sauran ƙasashen Afirka.
Shahada ba Mutuwa ba ce, Ci gaban rayuwa ce
Hujjatul Islam Abdulkadir Salati, a nasa jawabin ya yi nuni da ayar Alkur'ani da take nuni da cewa su shahidai ba sa mutuwa, sai dai suna wuri kebantacce da Allah ya ware musu. Shahada ba tana nufin karshen rayuwa ba ne, ci gaba da rayuwa ne a wurin na musamman tare da azurtawa daga Allah. Hujjatul Islam Abdulkadir Salati ya kawo tarihin waki'ar ta Buhari, inda ya bayyana yadda sojojin Nijeriya suka kai hari kan 'yan kasa wadanda basu dauke da komai da suka hada da mata masu ciki, masu shayarwa da kuma kananan yara, sama da mutum dubu, suka yi musu kisa na gilla ba tare da laifin komai ba. Dokta Abdulkadir Salati, ya nuna kamanceceniyar Gaza da Zariya, inda ya ce a Gaza, haramtacciyar kasar Isra'ila ta so ta kashe kowa da kowa ne, ya zama ba wanda ya rage, kamar yadda a Zariya ma abin da suka so su yi kenan amma Allah bai ba su nasara ba.
Sayyid Zakzaky (H); Misdakin Rihbaniyyun a Wannan Zamanin
Shi kuwa a jawabinsa, Hujjatul Islam Sulaimaniy, ya fara da karanta ayar
وَكَأَيِّنْ مِنْ نَبِيٍّ قَاتَلَ مَعَهُ رِبِّيُّونَ كَثِيرٌ فَمَا وَهَنُوا لِمَا أَصَابَهُمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَمَا ضَعُفُوا وَمَا اسْتَكَانُوا ۗ وَاللَّهُ يُحِبُّ الصَّابِرِينَ
"Kuma da yawa daga wani Annabi wanda ya yi yaki, akwai jama´a masu yawa tare da shi, sa´an nan ba su yi laushi ba ga abin da ya same su a kan hanyar Allah, kuma ba su yi rauni ba kuma ba su sad da kai ba. Kuma Allah yana son masu hakuri". (3:146)
Hujjatul Islam Sulaimaniy da yake fassara ma'anar 'rahbaniyyin', ya kawo ma'anar da Allama Tabataba'i ya bawa kalmar; sune wadanda suka sallama komai nasu ga Allah kadai. Hujjatul Islam Sulaimaniy ya ce misalin 'rahbaniyyun' a wannan zamanin Imam Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ne, shi ne wanda ya sadaukar da komai nasa ga Allah, kuma duk abin da ya same shi bai samu rauni ba, yayi hakuri ya kuma dake a kan hanyar.
Hujjatul Islam Sulaimaniy, da yake magana a kan shahidai, ya ce; abin da shahidai suke so daga gare mu shi ne dakewa da kuma kin sallamawa azzalumai. Ya ce akwai wahala da jarabawowi kamar yadda ya gabata a baya, amma idan aka dake aka jure akwai nasara a gaba. Daga karshe Mallamin ya karanta wasu baitoci ga shugabar matan duniya da lahira ya kuma sadaukar da ladan ga shahidan gwagwarmaya, musamman na Harkar Musulunci a Nijeriya.
Hujjatul Islam Belem, wanda ya gudanar da jawabinsa da Larabci, ya bayyana saƙifa a matsayin tushe na duk wasu matsalolin da al'umma suka tsinci kansu a ciki, ciki har da waki'ar Buhari. Sheikh Belem ya bayyana Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) a wacce ta nuna wa duniya yadda ake yin kira zuwa ga Musulunci ba tare da makami ba, akasin yadda aka kirkiri wasu kungiyoyi na ta'addanci da sunan masu kira a komawa tsarin Muslunci, misalin wadannan kungiyoyi ita ce Boko Haram. Ya ce amma dakewar Harkar Musulunci ya fito da ainihin fuskar Musulunci ta gaskiya, ta yadda sai da jini yai nasara a kan takobi (bindiga).
Wakilan kungiyoyin gwagwarmaya daga Iraqi da Bahrain ma sun gabatar na su jawaban, ga mahalartan. A nda suaka jaddada jajensu a madadin qasashensu akan wannan taadancin na Azzaluma Gwamnattin Najeria akan farar fula yan qasa da basuyi laifinkomai ba, tare da qarin addua'a ga shuhaa baki daya.
Daga karshe an gudanar da waken juyayi na tunawa da shahidan waki'ar ta Buhari, kana aka yi addu'a aka sallami jama'a. taron yayi armashi matuka.






























Your Comment