Friday 5 December 2025 - 14:27
Jagora Sayyid Ibarahim Zakzaky (H) Ya Tura Da Wakilai Don kara yinTa'aziyyar Rasuwar Shehu Dahiru Usaman Bauchi

Hauza/ A yau Alhamis, 13 ga Jimadal Thani 1447 (4/12/2025), wanda ya dace da kwanaki bakwai da rasuwar Shaikh Dahiru Usman Bauchi, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya tura da tagawar musamman don kara  yin ta'aziyya ga iyalai da almajiransa.

Acewar kafar watsa labarai ta Hauza, Sayyid Badamasi Yaqoub, wanda yake ƙane shaƙiƙi ga Jagora, ya karanta ta'aziyyar Jagora Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) ga iyalan Shehin Malamin, tare da bayyana rashinsa a matsayin rasa wani bangon jingina ga duniyar Musulmi, a matsayinsa na mahaddacin Alkur'ani, kuma mai hidima ga Alkur'ani a tsawon rayuwarsa.

Ta bangaren iyalan mamacin, Khalifa Shaikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi, ya nuna godiyarsu ga ta'aziyyar, tare da bayyana rashin Shehin a matsayin abin yima juna ta'aziyya gabadaya. Ya bayyana irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky da marigayi Shaikh Dahiru Usaman Bauchi din, inda ya bada misali da irin lokutan da Shaikh Zakzaky ya rika ziyartan Shehin a baya, har Shehi kan gabatar da shi ya ja su Sallah.

Tawagar wakilan diai ta hada da babban ɗan Jagora (H), Sayyid Muhammad Zakzaky, da 'yan uwan Jagora na jini, tare da ba'adin wakilan 'yan uwa daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

An gabatar da addu'o'i na musamman ga Shehin, dafatan Allah Ta'ala Ya jaddada masa rahama da jinkai.

Daga Sayyid Zakzaky Office.

photo_2025-12-04_19-22-31.jpg

photo_2025-12-04_19-22-31-4-.jpg

photo_2025-12-04_19-22-31-3-.jpg

photo_2025-12-04_19-22-31-2-.jpg

photo_2025-12-04_19-22-30.jpg

photo_2025-12-04_19-22-30-4-.jpg

photo_2025-12-04_19-22-30-3-.jpg

photo_2025-12-04_19-22-30-2-.jpg

photo_2025-12-04_19-22-30-4-.jpg

Jagora Sayyid Ibarahim Zakzaky (H) Ya Tura Da Wakilai Don kara yinTa'aziyyar Rasuwar Shehu Dahiru Usaman Bauchi

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha