Wednesday 3 December 2025 - 21:13
Ƙasashe Masu Da'awar 'Yanci, a Aikace Ba Sa Yin Komai Face Yaudarar Jama'a.

Hauza/ Ayatullah Modarressi ya bayyana cewa: Matan da suke kiyaye hijab ɗin su, a haƙiƙa suna kare 'yancin kai da mutuncin su, kuma suna 'yantar da kansu daga sha'awa da kallon da bai dace ba. Mazaje ma, ta hanyar bin iyakokin Allah, suna janyo wa kansu alkhairan duniya da lahira.

A cewar wakilin ofishin dillancin labaran Hauza daga Tehran, an gudanar da bikin rufe taron kasa da kasa na "Hakkokin Al'umma da 'Yancin Da'a a Tsarin Tunanin Mai Girma Ayatullah Khamene'i" a yammacin ranar 2 ga Disamba, 2025 a cibiyar tarurrukan kasa da kasa ta gidan talabijin da rediyon Kasar Iran

An gudanar da taron kasa da kasa kan hakkokin al'umma da 'yancin da'a a tsarin tunanin Mai Girma Ayatullah Khamene'i da manufofi uku: Na ɗaya, sake nazartar tunani da kuma sirar Mai Girma Ayatullah Khamene'i a fagen hakkokin al'umma da 'yancin da'a. Na biyu, zayyana tsarin da ya dace da hakkokin al'umma da 'yancin da'a dangane da tunanin Mai Girma Ayatullah Khamene'i. Na uku, tabbatar da hakkokin al'umma da 'yancin da'a da kuma yadda za a haɓaka su bisa ra'ayoyin da tunanin Mai Girma Ayatullah Khamene'i.

A cewar rahoton, Ayatullah Sayyid Mohammad Reza Madaressi Yazdi, mamba a hukumar kula da tsare tsarin mulki, yana mai nuni ga matsayin shawara a Musulunci, ya ce: Amirul Mu'minina Ali (AS) ya ce: "Kada ku dena faɗin gaskiya ko ba da shawarar adalci."

Shawara; ɗaya ce daga cikin ka'idojin tushe na Musulunci

Mamban na hukumar kula da tsare tsarin mulki ya ce: Shawara ɗaya ce daga cikin ka'idojin tushe na Musulunci wacce take zama ginshiƙin gudanar da al'ummomi. Allah a cikin Kur'ani mai girma ya ce: "Kuma a al'amuransu suna shawara a tsakaninsu." Wato, a al'amuran jama'a ya kamata su yi ta hanyar shawara da sa hannun junansu. Hatta Annabi Muhammad (SAWA) wanda shine cikakken mai hankali, an umurce shi da ya yi shawara da jama'a.

Da yake ba da misalai daga halayen Annabi (SAWA), ya bayyana cewa: A yaƙin Badar da Uhud, duk da cewa ra'ayin Annabi (SAW) ya sha bamban da na mafi yawan jama'a, matukar ra'ayinsu bai saba wa hukuncin Allah na ƙaddara ba, Annabi ya yarda da ra'ayin mafi rinjaye ne. Tabbas, a lokuta da hukuncin Allah ya bayyana kuma ya ƙaddara, Annabi (SAWA) yana aiki bisa umarnin Allah ne.

Ayatullah Modarressi Yazdi ya ci gaba da cewa: Bisa ga al'adar masu hankali, a cikin shawarwari ra'ayin mafi rinjaye shine ma'auni na aiki. A cikin wani hadisi daga Amirul Mu'minina Ali (AS) ya ce: "Ku yi shawara da masu ra'ayi sannan ku bi su." Wannan biyayya tana nufin ra'ayin gama kai na mafi rinjaye. Musulunci irin wannan addini ne. Addini wanda ya ba da cikakken 'yanci mafi girma ga 'yan Adam, kuma ya tsara wasu dokoki ne domin kare 'yancin tunani mai kyau na mutane; ko 'yancin siyasa ko tattalin arziki da sauran fagage.

Da yake kafa hujja da dogaro da ayoyin Kur'ani mai girma, ya bayyana cewa: Allah game da Annabi (SAWA) ya na cewa, ya umarnin mutane da aikata kyakkyawa, kuma yana hana aikata mummuna, kuma yana halatta abubuwa masu kyau a gare su, kuma yana haramta abubuwa marasa kyau. Yawancin tsauraran ƙa'idodi da hani da aka dora wa al'ummomin da suka gabata, an cire su a Musulunci.

Sukar da'awar neman 'yancin ƙasashen Yamma

Mamba na hukumar kula da tsare tsarin mulki ya soki da'awar neman 'yancin ƙasashen Yamma, yana mai bayyana cewa: Ƙasashen da suke sanar da kansu a matsayin cibiyar 'yanci, a aikace ba su yi kome ba face yaudarar jama'a. Suna nuna wani samfurin 'yanci ga duniya amma gaskiyar lamarin ta bambanta. A yau halin da Syria, Labanon da Gaza ke ciki shaida ne cewa yadda waɗannan masu da'awar 'yanci, a tsawon shekaru suna sanya wa waɗannan al'ummomin bam, da wawashe tattalin arziki. Shin wannan ba take hakkin ɗan Adam ba ne a fili?

Ya ce: Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ma, da taken 'yancin ɗan adam da haƙƙin mata, suna matsa wa al'ummomi da gwamnatoci, amma a aikace ba wani labari na kare hakkin ɗan Adam da gaske.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha