Friday 28 November 2025 - 10:46
Jamhuriyar Musulunci ta nuna cewa ita ce cibiyar iko da ƙarfi / Ku tsaya tare da juna a gaban abokan gaba, kamar yadda kuka yi a yaƙin kwanaki 12

Hawzah/ Ayatullah Khamene'i ya bayyana dangane da al'amurran yankin gabas ta tsakiya da kuma yaƙin kwanaki 12, ya ce: A yaƙin kwanaki 12, al'ummar Iran ba shakka sun yi nasara a kan Amurka da kuma Yahudawan Sahayoniya. Sun zo ne don yin ashararanci, amma an doke su kuma sun koma hannu wofi, ba su cimma ko ɗaya daga cikin burinsu ba, wannan shi ne ainihin kaye a gare su.

A rahoton kafar watsa labaran Hawza, Ayatollah Khamenei, Jagoran juyin juya halin Musulunci, da maraicen ya yayi magana ta talabijin ga daukacin al'ummar Iran, tare da jaddada mahimmancin ƙarfafawa da ci gaba da nuna ƙarfin Basij ga tsatso masu zuwa a matsayin "wata babbar dukiya, motsi na gama-gari, da kuma abin da ke haɓaka ƙarfin ƙasa," kasa cimma ko ɗaya daga cikin hadafin hare-haren da Amurka da Sahayoniya suka kai wa Iran, alamar kaye ce ba tare da wata shakka ba a cewar Jagoran. Ya kuma yi kira ga dukan jama'a da ƙungiyoyin siyasa su kiyaye da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Ya yi nuni da wajibcin da ya rataya a wuyan mahukunta don girmama ƙungiyoyin agaji (Basij), ya bayyana ƙungiyoyin Basij a matsayin wani muhimmin motsi na ƙasa mai ɗauke da manufa ta Allah da kuma na lamiri, mai dogaro da kai da kuma kishin ƙasa, ya kara da cewa: Tsatso na huɗu na ƙungiyoyin Basij, ma'ana matasa masu daraja a duk faɗin ƙasar, suna shirye don aiki da ƙoƙari, kuma wannan motsi mai muhimmanci da daraja dole ne a ci gaba da yaɗa shi a cikin tsatso a cikin ƙasa, a ci gaba da inganta shi kuma a ƙara masa ƙarfi.

Jagoran ya bayyana cewa irin wannan motsi na ƙungiyar Basij yana da amfani kuma abu ne da ya kamata ga kowace ƙasa, ya kara da cewa: Ƙasa kamar Iran, wacce a fili take tsayawa ta tunkari tunkahon duniya tare da sadaukar da kai fiye da kowace kasa, tana buƙatar ƙungiyar Basij fiye da kowace ƙasa.

Ayatullah Khamenei, ya yi nuni da wajibcin yin Muƙawama domin taka birki ga masu shisshigi da kuma kutse, masu mulkin mallaka, ya ce: Babban abin da ke taimakawa al'ummomi su tsaya tsayin daka, wanda aka kafa a Iran kuma ya bunkasa, a yau yana bayyana a cikin taken goyon bayan Falasɗinu da Gaza a sassa daban-daban na duniya, ciki har da ƙasashen yamma har ma da Amurka, ita ce gwagwarmaya.

Ya bayyana cewa, a wanzuwar Basij da kuzarinta yana haifar da ci gaban tsayin daka na al'ummomi a kan azzalumai na duniya, ya kara da cewa: Raunanan duniya, ta hanyar gwagwarmaya da muƙawama, suna jin an goyi bayansu tare da samun ƙwarin gwiwa.

Jagoran, a yayin bayanin abin da ake nufi da Basij, ya ce: "Basij a tsarinta, a matsayin wani ɓangare na Rundunar Sojojin Tsaro, tana da fuska mai ƙarfi a gaban abokan gaba, kuma tana da fuskar bauta wa jama'a. Amma mafi muhimmanci, kasancewar ta ko'ina cikin ƙasar, kuma a cikin kowane mutum da ƙungiya mai kishin ƙasa, wadanda suke a shirye don aiki, masu  kuzari da kuma bege a fannonin tattalin arziki, masana'antu, kimiyya, jami'a, Hawza, sadarwa, yanayin kasuwanci da sauran fagage.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa, "Basij, da wannan ma'anar ta gama gari," tana kawar da shirin abokan gaba a fannonin soja, tattalin arziki, sadarwa, fasaha da duk wani fanni, ya kuma ce: Manyan masana kimiyya waɗanda suka yi shahada a yaƙin kwanaki 12, masu ƙira, masu ginawa da kuma masu harba makamai masu linzami, duk wanda yake da tunani mai ƙarfi da kuma iya bayani, sun tunkari masu yada jita-jita, wasiwasi da kuma tada hankali, ta hanyar warware shirin su a saukake, kuma suna kan yi, likita da ma'aikacin jinya masu sadaukarwa waɗanda ba su bar asibiti ba a lokacin yaƙi, da kuma jaruman wasanni a bangarori daban-daban, waɗanda a filayen wasa na duniya suke nuna biyayya ga Allah, addini, kishin ƙasa da kuma al'umma, ko sun kasance ɓangare na Basij ko a'a, duk sun zama yan Basij.

Ya kara da cewa: Imam (Khomeini) ya kasance yana alfahari da kasancewarsa ɗan Basiji, wanda ya zama babban abin koyi ga Basij, Basij ba ta kasance ta wani ɓangare na musamman ba kawai, ta ƙunshi dukkan kabilu, masu sana'a da ɓangarori.

Jagoran, a cikin maganarsa ta ƙarshe game da Basij, ya jaddada wa dukkan jami'an hukumomin gwamnati cewa: Ku kasance kamar ƴan Basij, ku cika ayyukanku da imani, himma da kishin ƙasa.

Ayatullah Khamene'i, a wani ɓangare na maganarsa, ya bayyana game da al'amurran yankin gabas ta tsakiya da kuma yaƙin kwanaki 12, ya ce: A yaƙin kwanaki 12, al'ummar Iran ba shakka sun yi galaba akan Amurka da kuma Yahudawan Sahayoniya. Sun zo ne don yin ashararanci, amma sai suka sha duka,  suka koma hannun Rabbana, ba su cimma ko ɗaya daga cikin burinsu ba, wannan shi ne ainihin kaye a gare su.

Yayin da yake nuni da wasu maganganun da ke nuna cewa yahudawan mulkin mallaka sun shirya yaƙi na shekaru 20 da Iran, ya ce: Sun shirya wani yaƙi da za su yi kokarin harzuƙa al'umma, domin yin fito-na-fito da gwamnatin Musulunci, amma sai al'amarin ya koma akasin haka, har ma masu saɓani da gwamnati sun tsaya tare da gwamnatin, kuma an sami haɗin kai na gama gari a cikin ƙasar.

Jagoran juyin juya halin ya ce: Tabbas mu ma mun sami wasu hasarori, kamar yadda ake a al'adar yaƙi, mun rasa rayukan da suke da daraja, amma Jamhuriyar Musulunci ta nuna cewa ita cibiyar azama da ƙarfi ce, kuma tana iya tsayawa da ƙarfi ba tare da tsoron komai da kowa ba, kuma ta yanke shawara. Domin hasarar da aka yi wa abokan gaba ta fi tamu.

Ya kuma yi nuni da babbar hasarar da Amurka ta samu a yaƙin kwanaki 12, inda ya kara da cewa: Amurka ta yi hasara sosai a wannan yaƙin, domin duk da yin amfani da mafi kyawun makaman roka na kai hari da na tsaro, ba ta iya cimma burinta na yaudarar al'umma da kuma sa su zama tare da ita ba, a'a sai ma haɗin kan al'umma da ya ƙara ƙarfi, kuma suka hana Amurka cin nasara.

Ayatullah Khamene'i, ya yi nuni da rashin mutunci da kuma babban abin kunya ga yahudawan mulkin mallaka a Gaza, a matsayin ɗaya daga cikin mafi munin bala'o'i a tarihin yankin, ya kara da cewa: Amurka a wannan al'amari ta tsaya ƙafa da ƙafa tare da ƴan mulkin mallaka, kuma ta jawa kanta abin kunya da ɓata suna sosai, domin mutanen duniya sun san cewa yahudawan mulkin mallaka ba za su iya yin irin wannan ɓarnar ba idan ba tare da taimakon Amurka ba.

Ya bayyana cewa, mutumin da aka fi ƙi duniyar yau shi ne firaministan Yahudawan Sahayuniya, ƙungiyar da ke mulki da aka fi ƙi a duniya ita ce Sahayuniya, ya kara da cewa: Kasancewar Amurka tana tare da su, ya yada ƙiyayyar yahudawan mulkin mallaka zuwa ga Amurka.

Shugaban, ya bayyana kutsen da Amurka ke yi a sassa daban-daban na duniya a matsayin wani dalili na matsalar da ake fama da shi a yau, ya ce: Kutsen da Amurka ke yi a kowane yanki, shi ke haifar da yaƙi ko kuma kisan kiyashi, ɓarna da kuma gudun hijira.

Ya bayyana yaƙin Ukraine wanda yake cike da hasarori da kuma rashin sakamako a matsayin misalin kutsen da Amurka ke yi, ya kara da cewa: Shugaban Amurka na yanzu wanda ya ce zai kawo karshen wannan yaƙin cikin kwanaki uku, a yanzu bayan kusan shekara guda, yana tilasta karbar wani shiri na abubuwa 28 ga ƙasar da su suka shigar da ita cikin yaƙi.

Ayatullah Khamene'i ya bayyana hare-haren da yahudawan mulkin mallaka ke kaiwa Lebanon, kutsawa Syria da kuma laifuffukansu a yammacin Kogin Jodan da kuma halin da ake ciki na ban tausayi a Gaza a matsayin wasu misalan bayyanannun goyon bayan Amurka ga yaƙi da kuma laifuffukan mugayen mulkin mallaka, ya kuma ce: Tabbas suna ƙirƙirar jita-jita cewa gwamnatin Iran ta aika wa Amurka sako ta wata ƙasa, wannan ƙarya ce, kuma babu irin wannan magana kwata-kwata.

Ya kara nuni da cin amanar da Amurka ke yi har ma ga abokanta don goyon bayan yahudawan mulkin mallaka da masu laifi da kuma ƙoƙarin tada yaƙi a duniya saboda man fetur da albarkatun ƙasa, wanda a yau ya kai ma Latin Amurka, ya ce: Irin wannan gwamnati, tabbas ba ita ce gwamnatin da Jamhuriyar Musulunci ke neman haɗin kai da kuma alaƙa da ita ba.

Ayatullah Khamene'i, a ɓangaren ƙarshe na maganarsa, ya bada wasu shawarwari da yawa ga al'umma, wanda na farko shi ne kiyayewa da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Ya ce: Ana samun saɓani tsakanin ɓangarori da ƙungiyoyin siyasa, amma abu mai muhimmanci shi ne, a gaban abokan gaba, kamar yadda muka yi a yaƙin kwanaki 12, mu kasance tare, wannan haɗin kai shi ne babban abin da ke haifar da ƙarfin ƙasa.

Jagoran, ya ba da shawara marawa  shugaban ƙasa baya da kuma gwamnatin, ya ce: Aikin gudanar da ƙasa yana da wuya kuma yana da nauyi, kuma gwamnati ta fara wasu ayyuka masu kyau, ciki har da ci gaba da ayyukan da shahid Ra'isi ya bari, wanda al'umma za su ga sakamakonsu, in sha Allah.

Kaurace wa ɓarna a duk abubuwa, da suka hada da biredi, gas, man fetur da kayan abinci, shi ne shawara ta uku da shugaban ya bai wa al'umma. Ya bayyana almubazzaranci a matsayin ɗaya daga cikin mafi munin hatsarori da kuma hasara ga iyalai da ƙasa, ya kuma ce: Idan aka kiyaye wannan almubazzarancin, ba shakka halin da ƙasar ke ciki zai fi kyau.

Shawarar ƙarshe da Jagoran ya baiwa mutane ita ce ƙarfafa alaƙa da Allah da kuma yin addu'a kan komai, ciki har da ruwan sama, tsaro da kuma lafiya, domin Allah Ya bada hanyoyin gyara al'amura da falalarsa.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha