A cewar Rahoton Cibiyar Labarai ta Hauza, a farkon jawabin nasa, ya bayyana cewa: Allah Maɗaukaki yana da sunaye dubu uku (3000), inda aka bayyana dubu ɗaya (1000) ga mutane kuma sun zo cikin Du’a al-Jawshan al-Kabir. Babu wani suna daga cikin wadannan da ke nuni da fushi ko azaba; dukkan su suna nuna kyawawan siffofi da ayyukan Ubangiji.
Malamin akhlaq na Hauza ya ce waɗannan sunaye duka suna komawa ga asali guda ɗaya ne, domin ba rarrabewa tsakanin siffofi da zatinsa. Wanda ya raba siffofi daga zati, to ya kusanci yin shirka.
Ya ƙara da cewa: daga cikin waɗannan sunaye, dubu ɗaya Allah ya koyar da Annabawa, yayin da dubu ɗaya kuma — da ake kira Asma’ al-Musta’thar — ke kasancewa sirrin Allah wanda babu wanda ya sani, kuma za su bayyana a ranar Kiyama.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce daga cikin waɗannan sunaye, akwai guda 99 da ake kira Asma’ul Husna, kuma akwai mutane da ke zama siffofin zahiri na waɗannan sunaye.
Imam al-Baqir (A.S) ya ce: “Allah ba shi da wata alama mafi girma daga gare ni.” Imam Ali (A.S) ma ya ce: “Ni ne mafi girman alamar Allah.” Haka kuma Annabi (S.A.W) ya ce: “Dukkan mutane daga bishiyoyi daban-daban suke, amma ni da Ali daga bishiya guda daya muke.”
Ansarian ya ce: cire Imam Ali (A.S) daga rayuwar Musulmi yana nufin dogaro da Annabta mara tushe, domin Annabta bata da rai idan babu Imama. Imam Ali (A.S) shi ne Asma’ul Husna a cikin mutum da kuma jagoran sanin Allah.
Ya ƙara da cewa: Banu Umayya da Banu Abbas sun ƙirƙiro wani, “Allah na ƙarya” ga mutane, alhali Allah na Ahlul Baiti shi ne Allah na Qur’ani wanda babu kamarsa. Duk wanda yayi nisa daga barin Allah, shaidan ne zai mamaye zuciyarsa, ya cike gurbin da ya cire Alla dag zuciar tasa ba tare da jinkirtawa ba.
Ya ce: Allah ne ke sanya wa halittu suna; ya sanya suna “Ard” ga ƙasa, Sama ga sararin samaniya, da Adam ga mutum na farko. Amma ba duk sunayen da mutane ke bayarwa ba ne Allah yake yarda da su. Imam Ali (A.S) ya ce: “Daya daga cikin hakkokin ɗa a kan iyayensa shi ne su zaba mashi suna mai kyau,” kuma wannan hakki na ubansa ne.
Ansarian ya ci gaba da cewa: Allah ne ya umarci Annabi (S.A.W) ya sanya wa ’yarsa suna Fatima. Kalmar “Fatima” tana nufin “wadda aka ware daga mugunta.” Ahlul Baiti (A.S) sun bayyana ma’ana uku don wannan suna, kuma dukkaninsu sun tabbata a cikin Sayyida Fatima (A.S).
Fatima Zahra (A.S) ta tsarkaka daga kowace irin najasa ta ruhaniya, hankali, ko aiki. Wannan ya tabbata cikin ayar Qur’ani mai cewa:
«إِنَّمَا یُرِیدُ اللَّهُ لِیُذْهِبَ عَنْکُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَیْتِ وَیُطَهِّرَکُمْ تَطْهِیراً.»
"Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa." (Ahzab (33).
Imam Baqir (A.S) ya ruwaito cewa: lokacin da Sayyida Khadija (A.S) ta yaye Fatima (A.S), Allah ya cika ta da ilimi, ta yadda har ta daina bukatar nono daga cikarta shekara biyu din. Daga baya ta gabatar da hudubobi biyu a gida da masallaci, waɗanda masana har yanzu suna nazari a kansu tsawon ƙarnuka 15.
A ƙarshe, Ansarian ya ce: Imamai (A.S) sun faɗa cewa Allah ne ya sanya mata suna Fatima, domin a ranar Kiyama za ta tsaya ta raba ’yan Shi’a na mahaifinta da mijinta daga wuta ta ce: “Waɗannan ba itacen jahannama ba ne.” Wannan yana nuna matsayinta mai girma da ikon da Allah ya ba ta don ceton ’yan Shi’a a ranar Kiyama.
Your Comment