Sunday 2 November 2025 - 13:56
Wasan Roblox daya daga cikin wasanni ne na shaidan kuma ɗaya daga cikin kayan yaƙin Ruwan sanyi, (yaƙin da bada makami ba)

Hauza/ Hojjatul Islam wal Muslimin Sayyid Sadruddin Qubanji ya bayyana cewa: Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Iraki ta haramta sabon wasa mai suna Roblox — wasa ne na yara amma mugun wasa ne wanda yake wakiltar mugunta mai zurfi.

A cewar Hukumar Fassarorin Jaridar Hawza, Hojjatul Islam wal Muslimin Sayyid Sadruddin Qubanji, Limamin Juma’ar Najaful Ashraf, a cikin hudubar Juma’a da ya gabatar a Husainiyya Al‑Aʿẓam Fāṭimiyya a Najaful Ashraf din, ya ce: “Dangane da zaɓen majalisar dokoki mai zuwa, muna da ra’ayin cewa harshen kabilanci ko sekta ba harshen kundin tsarin mulki bane kuma ba harshen mika ikon mulki cikin lumana bane. Kundin tsarin mulki ya ginu bisa rinjayen siyasa ne, don haka dole ne a yi la’akari da ra’ayin mafi rinjaye. Ya ƙara da cewa: don haka, muna roƙon mafi rinjaye su bayyana ra’ayinsu ba tare da amfani da kalaman bangare ba. Muna ganin cewa masu fadi tseren siyasa ne ke amfani da harshen bangare, wanda ba bukatar mu bane mu.

Limamin Juma’ar Najaful Ashraf ya ci gaba da cewa: Muna kuma ganin cewa jama’armu sun shirya sosai don wannan zaben mai matuƙar muhimmanci, kuma ina tsammanin wannan zaɓen shi ne mafi dauke da tausayi da a tsarin hankali, duk da ƙoƙarin wasu wajen tayar da fitina ta bangare da rashin hankali.

A cikin wani bangare na hudubar, Sayyid Qubanji ya bayyana cewa: Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Iraki ta haramta sabon wasa mai suna Roblox; wasa ne na yara amma na shaidan wanda ke nuna mugunta mai zurfi, kuma yana ɗaya daga cikin kayan yaƙin ruwan sanayi (soft war) wanda ya fi yaƙin da ake yi da makami haɗari.

Ya ci gaba da cewa: Yaƙin da ake yi da makami yana buƙatar sojoji, zubar jini da makamai masu ƙarfi, amma yaƙin ruwan sanyi, baya buƙatar sojoji, baya buƙatar makamai masu ƙarfi, kuma baya buƙatar tayar ma da maƙiyi hankali kai tsaye. A maimakon haka, yana jan hankalinsu ba tare da sanin su ba, harma sukan riƙe shi da kauna.

Limamin ya kara da cewa: Muna godiya ga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida saboda haramta wannan wasa mai cutar da iyalai da suka yi. Muna kuma godiya da kokarinta wajen rushe ƙungiyoyin ƙarya na bara, ƙungiyoyin sihiri da keɓantattun ƙungiyoyin masu bautar ga shaidan.

A bangaren hudubar addini, Hojjatul Islam wal Muslimin Qubanji ya yi magana game da Sayyida Fāṭimah az‑Zahrāʾ (SA), inda ya ce: Muna da Gajeruwar tattaunawa game da Sayyida Fāṭimah (SA), kamar yadda muke girmama ranar shahadarta bisa ruwayar ta biyu. Ya kawo labari daga ‘Allāmah Aminī, marubucin littafin al‑Ghadīr, wanda muke tuna ranar rasuwarsa a shekara ta 1390 Hjri.

A cewar Qubanji, Allāmah Aminī a cikin wata tattaunawa da malaman Ahlus‑Sunnah a Bagadaza yayin cin abinci da aka tambaye su: “Menene ra’ayinku game da hadisin Annabi (SAW) wanda ya ce: “Duk wanda ya mutu ba tare da bai’a ga shugaba ba, ya mutu mutuwar jahiliyya?” Sai Suka ce: “Eh, haka ne.” Sai Aminī ya tambaye su: “Menene ra’ayinku game da hadisin Annabi (SAW) wanda ya ce: ’Yata Fāṭimah shugabar mata ce a duniya?”

Suka ce: “Eh.” Sai Aminī ya ce: “Sayyida Fāṭimah (SA) ba ta yi bai’a ga Khalifa na farko da na biyu ba; ta mutu cikin fushi da su. Shin hakan na nufin ta mutu mutuwar jahiliyya?” Sai duk suka yi shiru, suka kasa amsawa.

A ƙarshe, Limamin Juma’ar ya ambaci hadisin Annabi (SAW) da ke cewa: “Duk wanda ya reni ‘ya’ya mata uku, aljanna ta tabbata a gare shi.” Wannan yana tabbatar da ra’ayin rahama da tausayi da Musulunci ke koyarwa.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha