Hauza - A cewar rahoton, wannan taron kimiyya an shirya shi ne domin nazarin tunani, ra’ayoyi, da tasirin addini da zamantakewar manyan jagororin Shi’a, tare da halartar malamai, masu bincike da masoyan ilimin addini. Wannan taron ya zama dama ta musamman wajen fahimtar tasirin jagororin Shi’a a ci gaban addini da zamantakewa.
A yayin taron, Hujjatul Islam Sayyid Muhammad Yusuf Mahdi, mataimakin shugaban sashen bincike na Cibiyar Bincike da Koyarwa ta Shi’a ta Myanmar, ya gabatar da cikakken nazari game da tunani da falsafar manyan malamai da shugabannin Shi’a. Haka kuma ya tattauna kan ra’ayoyinsu game da wayewar Turawa (Western Civilization) da dabarunsu na zamantakewa da siyasa, tare da bayyana rawar da suka taka wajen jagorantar al’ummar Shi’a da tsayawa kyam a kan kalubalen zamani.
Hujjatul Islam Sayyid Nasser Husain, malamin addini a Myanmar, ya yi bayani kan rayuwa, ayyukan kimiyya da jihadin addini na Ayatollah Sayyid Abul Qasim al-Khoei (R.A.), Imam Khomeini (R.A.), da Shahid Sheikh Nimr Baqir al-Nimr, inda ya jaddada rawar da suka taka wajen jagoranci, wayar da kai, da tsayin daka wajen adawa da zalunci da mulkin kama-karya.
Haka kuma, Hujjatul Islam Sayyid Ja’far Ja’fari, limamin Babban Masallacin Magu a Myanmar, ya bayyana tarihin rayuwa da ayyukan jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah al-Uzma Sayyid Ali Khamenei da Ayatollah al-Uzma Sayyid Ali al-Sistani, tare da nazarin matsayin su na addini, siyasa da shugabanci a cikin al’ummar Musulmi A gefe guda, Zaynab Madina Beik, shugabar sashen tarbiyya a Cibiyar Bincike da Koyarwa ta Shi’a ta Myanmar, ta yi jawabi kan rawar da mabiya Shi’a – musamman mata – ke takawa a cikin al’ummar Musulmi. Ta bayyana irin gudunmawar su wajen ilimi, addini da sadaukarwa, tare da jaddada muhimmancin halartar mata –fagen zamantakewa a ci gaban al’umma ta addini.
A ƙarshe, Hujjatul Islam Sayyid Muharram Husain ya gode wa masu shirya taron da mahalarta, sannan ya kammala taron da addu’a da roƙon albarka. Wannan taron ya zama wata dama mai muhimmanci domin karin fahimta game da tunani, rayuwa da gudunmawar manyan jagororin Shi’a, tare da yada karantarwarsu zuwa ga sabbin ƙarni na Musulmai.
Your Comment