Saturday 31 January 2026 - 00:09
Jinin Shuhada Ba Zai Tafi a Banza Ba

Hauza/ Harkar addini ta ruhaniya a Rasha mai suna "Ka Kasance Mai Tunawa da Hussain" yayin gaisuwar ta'aziyya ga al'ummar Iran ta roki neman kariyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga wurin Allah.

A cewar rahotanni daga sashin harkokin ƙasa da ƙasa na Ofishin Yada Labaran Hauza, Harkar addini ta Ruhaniya ta Rasha "Ka Kasance Mai Tunawa da Hussaini" ta fitar da wata sanarwa a sakamakon abubuwan da suka faru na baya-bayan nan sannan kuma da nuna goyon bayanta ga al'ummar Musulunci ta Iran wadda ta bayyana kamar haka:

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

Harkar addini ta Ruhaniya ta Rasha "Ka Kasance Mai Tunawa da Hussaini" cikin tsananin baƙin ciki da zuciya mai cike da makoki, tana mika ta'aziyyar ta mafi zafi daga cikin zuciya zuwa ga shugaban zamani, Imam Muhammad Mahadi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), babban jagoran juyin juya halin Musulunci, Imam Sayyid Ali Khamenei (Dz), da kuma ga daukacin al'ummar Musulunci ta Iran mai neman kusanci da Allah, a kan shahadar masoyan Ahlul Baiti (AS) wadanda suka yi shahada a sakamakon ayyukan ta'addanci da tarzomar zubar da jini.

Zukatan muminai suna cike da zafin ganin sake zubar da jinin tsarkakan mabiyan gidan Annabi Muhammad (SAWA) a kasa; wadanda babban laifinsu shine riko da gaskiya, biyayya ga Ahlul Baiti (AS) da tsayin daka a gaban maƙiyan da maciya amanar ƙasarsu. Waɗannan shuhadan, su ne masu ci gaba da tafarkin Imam Husaini (AS) kuma shahadarsu ita ce shaida mai rai akan cewa, bangaren Yazid a kowane lokaci maƙiyin bangaren Husaini (AS) ne kuma zai ci gaba da Kasancewa.

Muna da yaƙini cewa jinin shuhada ba zai zuba a banza ba, kuma zai zama tushen wayewa, haɗin kai da juriya mafi girma ga al'ummar Musulunci. Muna roƙon Allah Maɗaukaki Ya karɓe su a matsayi mafi girma a Aljanna tare da Imam Husaini (AS), sahabbansa masu aminci da duk shuhadan Musulunci; Ya bai wa iyalansu haƙuri, kuma Ya ba wa wadanda suka jikkata lafiya cikin sauri.

Muna roƙon Allah Maɗaukaki Ya kiyaye Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ya ƙarfafa zukatan muminai, Ya lalata makircin maƙiyan Ahlul Baiti (AS), kuma Ya kusanto da ranar cin nasarar adalci a ƙarƙashin tutar Imam Mahadi (AS).

"Daga Allah muke, kuma gare shi zamu koma."

Amincin Allah ya tabbata ga shuhada, kunya ta tabbata ga maciya amana, kuma nasara ta har abada ta tabbata ga tafarkin Husaini (AS)!

Harkar Addini ta Ruhaniya ta Rasha "Ka Kasance Mai Tunawa da Hussaini (AS)"

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha