Wednesday 17 December 2025 - 23:59
Masu Itikafi Su Yi Addu’ar Neman Ceto Ga Musulmi Daga Mawuyacin Halin Da Suke Ciki

Hauzah/Ayatullah Subhani ya bayyana cewa: "Abin da ke faruwa da musulmi a yau ba a cika ganin irinsa ba a tarihi, kuma halin ko-in-kula da duniya ta nuna ga wadannan masifu yana kara nauyin addu'a, tawassuli, da farkawar al'ummar musulmi."

A cewar Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Subhani, a yayin ganawa da mambobin kwamitin ilimi da shugaban babban kwamitin itikafi, ya yaba da ayyukan da ake yi wajen yada al'adar itikafi, inda ya jaddada muhimmancin ruhi a cikin hakikanin rayuwar dan Adam.
Ya bayyana cewa: "Wani babban sashi na mutumtakar dan Adam yana komawa ne ga ruhaniyarsa, idan aka zare ruhaniya daga jikin dan Adam, gaskiyar mutumtakarsa za ta raunana. Neman Allah da karkata zuwa ga madaukacin Sarki yana cikin dabi’a (Fidra) da jigon dan Adam, kuma tunanin cewa neman sanin Allah ba shi da alaka da asalin dan Adam kuskure ne na fahimtar gaskiyar dabi’ar Ubangiji da aka halicci mutum akai."
Wannan Marja'in ya yi ishara da matsayin ibadu a Musulunci wajen shiryar da mutum zuwa ga ruhaniya, inda ya kara da cewa: "Daya daga cikin muhimman ibadu da ke sanya mutum ya karkata zuwa ga madaukacin Sarki shi ne Itikafi. Ibadar da mutum yake samun damar komawa ga Allah, da dabi'arsa, da kuma cikin ransa ta hanyar yanke alaka da shagaltuwar yau da kullum da al'amuran duniya. Muhimmancin itikafi ya kai matsayin da Manzon Allah (S.A.W.A), bayan da bai sami damar yin sa ba a shekarar yakin Uhudu, a shekara ta gaba ya yi itikafi na kwanaki ashirin, kuma akwai ruwayoyi daban-daban kan tsawon lokacin itikafinsa."
Ayatullah Subhani, yayin da yake ishara da halin da duniya take ciki a yau da kuma rinjayen hangen abin duniya (materialism) a rayuwar dan Adam, ya bayyana cewa: "Duk yadda muka sami damar karkatar da mutane zuwa ga ruhaniya ta hanyoyin da suka dace, na hankali, da inganci, to matsaloli da dama na daidaikun mutane da na zamantakewa za su kau, rayuwa za ta yi dadi, sannan wutar yake-yake da son kai za ta mutu."
Daga karshe, Ayatullah Subhani ya yi ishara da halin da duniyar musulmi take ciki, inda ya bukaci masu itikafi da su yi amfani da kwanakin itikafin wajen yin addu'ar neman ceto ga musulmi daga mawuyacin halin da ake ciki, da neman hadin kan al'umma, da kuma kau da zalunci. Ya kara da cewa: "Abin da ke faruwa da musulmi a yau ba a cika ganin irinsa ba a tarihi, kuma halin ko-in-kula da duniya ta nuna ga wadannan masifu yana kara nauyin addu'a, tawassuli, da farkawar al'ummar musulmi."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha