Sunday 23 November 2025 - 05:59
Zuwa ga Al’umma Ta Gaskiya: Muhimmancin Imam a Musulunci

Hauza/ Shi’a suna da cikakken imani cewa bayan annabawan Allah, musamman Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), hanyar shiriya da jagoranci ga bayin Allah tana ci gaba ne ta hanyar Imamanci na Imamai (a.s.). Kuma duniya ba ta taɓa zama babu wakilin Allah (Imam) wanda yake da alhakin jagorantar bayinsa zuwa ga shiriya ba. Amma tambayar da take tasowa anan ita ce: tunda akwai Al-Kur’ani da Sunnar Annabi (s.a.w.), me yasa ake buƙatar Imam?

Acewar cibiyar labaran Hauza, wannan jerin tattaunawa mai taken “Zuwa ga Al’umma Ta Gaskiya” an shirya shi domin yada ilimi da koyarwa masu alaƙa da Imam Mahdi (a.t.f.s.), domin amfanin malamai, ɗalibai, da masu neman sani.

Dalilin buƙatar Imam

Akwai dalilai masu yawa da suka nuna muhimmancin kasancewar Imam, amma mu za mu takaita ga bayani mai sauƙi kuma gajere. Dalilin da ya tabbatar da buƙatar Annabi shi ne dai dalilin da yake tabbatar da buƙatar Imam. Addinin Musulunci shi ne addini na ƙarshe, kuma Annabi Muhammad (s.a.w.) shi ne manzon Allah na ƙarshe. Saboda haka, dole ne wannan addini ya kasance mai bayar da amsar dukkan buƙatun ɗan Adam har zuwa ranar ƙiyama. Al-Kur’ani Mai Girma ya ƙunshi ka’idoji da tsarin umarnin Allah, amma Annabi (s.a.w.) ne Allah Ya ɗora wa nauyin fassara da bayani game da su. Duk da haka, Annabi (s.a.w.) ya bayyana su ne bisa buƙatar al’umma da yanayin da suka kasance a zamaninsa. Saboda haka, wajibi ne a sami magada na gaskiya waɗanda suke da haɗin kai da ilimin Allah, domin su ci gaba da bayyana abin da Annabi bai bayyana ba, da kuma jagorantar al’umma a dukkan zamani bisa ga ƙa’idar shiriya, Kmar ydda Alah mabuwayi yake cewa:

إِنِّي تَارِكٌ فِيكُمُ الثَّقَلَيْنِ كِتَابَ اللَّهِ وَعِتْرَتِي؛ مَنْ تَمَسَّكَ بِهِمَا لَنْ يَضِلَّ بَعْدِي أَبَداً.

Na bar muku abubuwa biyu masu nauyi: Littafin Allah da zuriyata (Ahlul-Baiti). In har kuka manne da su, ba za ku taɓa bata hanya ba a bayan ni.

Imamai (a.s.) su ne masu tsare gadon Annabi, su ne masu fassarar gaskiya na Al-Kur’ani Mai Girma, domin kare addinin Allah daga ruɗu da kuskure har zuwa ƙarshen zamani.

Bugu da ƙari, Imam a matsayin mutum cikakke (insān kāmil) shi ne abin koyi na kamala da adalci a dukkan fannoni na rayuwa. Mutane suna da buƙata ta zahiri da ta ruhaniya zuwa ga irin wannan jagora wanda zai tsarkake zukatansu, ya koya musu hanyar Allah, kuma ya kare su daga ruɗun sha’awa da makircin shaidan kamar yadda Allah mai jinkai ya fada cewa:

بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلزُّبُرِۗ وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلذِّكۡرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيۡهِمۡ وَلَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ

Mun aiko su da hujjoji bayyanannu da littattafan wahayi; kuma Mun saukar da Ambato (Al-Kur’ani) gare ka, domin ka bayyana wa mutane abin da aka saukar musu, ko da za su yi tunani. (Surat An-Nahl, 16:44). Imam Sadiq (as) a wannan fagen yana cewa:

إِنَّ الْأَرْضَ لَا تَخْلُو إِلَّا وَفِيهَا إِمَامٌ كَمَا إِنْ زَادَ الْمُؤْمِنُونَ شَيْئاً رَدَّهُمْ، وَإِنْ نَقَصُوا شَيْئاً أَتَمَّهُ لَهُمْ.

Ƙasa ba ta taɓa zama babu Imam ba; domin idan muminai suka ƙara wani abu (a cikin addini), Imam yana mayar da su zuwa gaskiya, idan kuma suka rage wani abu, yana cika musu daidai da tsarin Allah. Daga cikin muhimman ayyukan Imam akwai:

- Jagoranci da gudanar da harkokin al’umma (kafa gwamnati bisa adalci).

- Tsaron addini da bayanin Al-Kur’ani bisa fahimtar gaskiya.

- Tsarkake zukata da jagorantar mutane zuwa ga kamalar shiriya

Duk waɗannan suna tabbatar da cewa kasancewar Imam wajibi ce ga rayuwar Musulmi a dukkan zamani, har ma a lokacin ɓoyuwarsa (ghayba).

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha