Monday 5 January 2026 - 20:13
Soyayyar Sarkin Muminai Ali (AS) Tana Da Tushe A Cikin Dabi’ar Dan Adam (Fitra)

Hauza / Hujjatul Islam Wal Muslimin Abedini ya jaddada cewa: Idan soyayyar Sarkin Muminai Ali (AS) tana karuwa a cikin zuciyarmu, to wannan alama ce ta lafiyar dabi’armu ta asali (Fitra). Amma idan wannan soyayya tana raguwa, to ya kamata mu damu da cewa dabi’armu ta asali ta fara samun lullubi ko shamaki.

Bisa rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza daga birnin Tehran, Hujjatul Islam Wal Muslimin Abedini, malamin Hauza, a ranar Asabar a cikin shirin talabijin na "Samte Khoda", yayin da yake bayyana matsayin lokuta a cikin tafiyar bawa zuwa ga Allah (Suluk) da kuma alaka ta musamman tsakanin haihuwar Sarkin Muminai Ali (AS) da Tauhidi, ya jaddada cewa: "Soyayya da Wilayar Sarkin Muminai Ali (AS) abu ne na dabi'a (fitra), kuma alakar dan adam da Imam alaka ce rayayya, mai dorewa kuma ta kowane lokaci, ba wai kawai wani abu ne na tarihi ko na biki ba."

A farkon jawabinsa, ya yi nuni da rawar da lokuta suke takawa a cikin tafiyar mutum ta ruhaniya, inda ya ce: "Lokuta matakai ne na tafiya zuwa ga Allah, kuma kowane mataki na lokaci yana da siffa ta musamman da za ta iya kusantar da mutum zuwa ga Ubangiji. A sahun gaba na wadannan matakai, akwai kwanakin da suke da alaka ta musamman da Waliyyai na Allah, kuma a cikin wadannan kwanaki, matsayin Sarkin Muminai Ali (AS) ya zama na daban kuma ba shi da tamka."

Wannan malamin na Hauza ya yi nuni da haihuwar Sarkin Muminai Ali (AS) a cikin dakin Ka'aba, inda ya bayyana cewa: "Haihuwar Sayyidina Ali (AS) a cikin dakin Allah zabi ne na hikima domin nuna cewa wannan mutum ne na musamman kuma mara tamka. Haihuwa a cikin Ka'aba tana bayyana alakar dake tsakanin wanzuwar Sarkin Muminai (AS) da Allah Madaukakin Sarki, kuma wannan siffa tana taka muhimmiyar rawa a cikin tafiyarmu ta zuwa ga Tauhidi. Wannan haihuwa tana hada mutum ne da alkibla ta gaskiya, wato hakikanin Ka'aba kuma makoma ta karshe ta dukkan zukata."

Hujjatul Islam Wal Muslimin Abedini ya kara da cewa sanin hakikanin Sarkin Muminai (AS) ya fi karfin fahimtar dan adam ta yau da kullum, ya ce: "Duk da cewa ba mu da ikon fahimtar hakikanin wanzuwarsa, amma za mu iya ganin hasken rayuwarsa ta hanyar mabiyansa da dalibansa. Tarihi ya nuna cewa mutane irin su Abu-Zar, Salman, Mikdad, da Ammar, ta hanyar haskakawar da suka yi, sun bayyana kadan daga cikin girman Wilaya."

Malamin ya ci gaba da cewa: "A zamaninmu ma, muna ganin bayyanar wasu fitattun mutane wadanda ta hanyar kulla alaka ta kurkusa da makarantar Sarkin Muminai Ali (AS), suka rayar da wannan gaskiya a wannan zamani namu. A fagen ilimi da tunani, mutane irin su Allama Misbah Yazdi da Shahid Mutahhari sun kasance madubin wannan tafarki. Sannan a fagen gwagwarmaya da ayyukan zamantakewa, Janar Shahid Haj Qasem Sulaimani ya kasance babban misali na bayyanar adalci, yaki da zalunci, soyayya, da taimakon wadanda aka zalunta irin na Sarkin Muminai Ali (AS)."

Wannan malamin na Hauza ya yi ishara da halayen Shahid Haj Qasem Sulaimani, inda ya bayyana cewa: "Haj Qasem ya kai hakikanin Wilayar Sarkin Muminai (AS) zuwa fagen duniya, kuma ya nuna cewa duk wanda yake kaunar Shugaba (Maula), to yana kaunarsa ne da dukkan jikinsa da rayuwarsa; da zuciyarsa, da harshensa, sannan da aikinsa. A cikin lokacin da duniya ta rasa jarumai, shi ya haskaka a kololuwar mutuntaka har ya janyo hankalin kowa zuwa gare shi."

Malamin ya ci gaba da cewa: "Haskaka da daukakar shahidai mafi yawanci tana kara bayyana ne bayan shahadarsu. Kamar yadda bayan shahadar Shahid Mutahhari ne mutane suka fara amfana sosai da iliminsa da koyarwarsa, haka ma bayan shahadar Haj Qasem Sulaimani, tsoron da makiya suke wa sunansa da tafarkinsa ya kara yaduwa a ko'ina. Wannan tasiri yana da tushe a cikin soyayya ta gaskiya, wacce take samo asali daga kaunar Sarkin Muminai Ali (AS)."

Hujjatul Islam Wal Muslimin Abedini ya bayyana wasu misalai na dabi'un Shahid Sulaimani na kankan da kai da kuma nuna iko, inda ya ce: "Ya kasance mai tsananin kankan da kai a gaban iyalan shahidai, amma kuma yana tsayuwa da dukkan karsashi da kwarjini a gaban masu girman kan duniya (istikbari) da kungiyoyin 'yan ta'adda. Wannan ita ce daidaitacciyar dabi'a ta Wilaya wacce take samo asali daga makarantar Sarkin Muminai Ali (AS); wato kankan da kai a gaban gaskiya, da kuma tsayin daka a gaban karya."

Malamin ya ci gaba da bayani kan yadda alaƙar ɗan adam da Walayya take ta dabi'a (fitra), inda ya ce: "Alaƙar Imam da zukata alaƙa ce ta dabi'a. An ambata a cikin riwayoyi cewa a cikin alkawarin 'Alast' (alkawarin farko kafin halitta), baya ga Tauhidi da Annabta, an karɓi alkawarin Wilayar Sarkin Muminai Ali (AS) daga dukkan mutane. Wannan alkawari ya ci gaba a tsawon tarihi, kuma a ƙarshen tarihi ma dukkan al'ummai za su shiga Aljanna tare da Manzon Allah (SAWA) da Sarkin Muminai Ali (AS)."

Wannan malamin na Hauza ya ƙara da cewa: "Annabawa da wasiyyan Allah a tsawon tarihi, kowannensu ya bayyana wani sashe na hasken gaskiyar Manzon Allah (SAWA) da Imam Ali (AS) gwargwadon ikon fahimtar mutanen zamaninsu, domin su shiryar da ɗan adam zuwa ga cikamakon Annabawa (Khatamul Anbiya) da kuma cikamakon Wasiyyai (Khatamul Awsiya)."

Hujjatul Islam Wal Muslimin Abedini ya ambaci wata riwaya daga Manzon Allah (SAWA) game da yadda za a gane wanda zai gaje shi (Wasiyyi) bayansa, inda ya ce: "Manzon Allah (SAWA) bai bayyana wasiyyinsa ta hanyar siffofin zahiri kawai ba, a'a, ya gabatar da ma'auni na dabi'a (Fitra). Wasu rukunin mutane daga kasar Yemen da suke da zukata masu tsarki, sun gane Sarkin Muminai Ali (AS) ba tare da an gabatar musu da shi kai tsaye ba. Wannan yana nuna cewa dabi'a (fitra) mai lafiya tana da wata alaka ta dindindin da Wilayar Ubangiji."

A karshen jawabinsa ya jaddada cewa: "Idan soyayyar Sarkin Muminai Ali (AS) tana karuwa a cikin zukatanmu, to wannan alama ce ta lafiyar dabi'armu da kuma rayuwar fitrarmu. Amma idan wannan soyayya tana dusashewa, to dole ne mu damu da cewa dabi'armu ta samu lullubi (hijabi). Alakarmu da Sarkin Muminai Ali (AS) alaka ce rayayya kuma ta har abada, wacce ya kamata ta bayyana a kowane lokaci na rayuwarmu."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha